Wednesday, July 22, 2015

An Gano Rubutun Al-Kur'anin Da Ya Fi Kowanne Dadewa A Duniya A Ingila

A Jami'ar Birmingham ta kasar Ingila, an gano wani rubutun Al-Kur'ani da za a iya cewa ya fi kowanne dadewa a duniya.

Rubutun wanda wasu kwararru suka gano shi a dakin karatun jami'ar ana kyautata zaton ya fi shekaru 1,370 da rubutawa.

Mahukuntan jami'ar sun bayyana cewa rubutun ya fi shekara 100 a dakin karatun amma ba su taba fahimtar menene ba sai yanzu da wani kwararre kan gano tsofaffin rubutun larabci Muhammad Isa Waley yayi nazari akansa.

A cewar Muhammadu Waley gano wannan rubutu ba karamin farin ciki zai sanya a zukatan Musulmai ba.

...Allah ya karawa Musulunci daraja, Ya kara kare martaba da tsarkin Al-Kur'aninsa mai girma.

1 comment:

  1. DANGOTE CEMENT FACTORY LOKOJA OBAJANA PLANT NIG PLC.WISH TO INFORM THE GENERAL PUBLIC OF SALES OF ITS CEMENT REDUCTION TO N1000 PER BAGS...CEMENT GRADE 50KG,THE MANAGEMENT NOW OFFER CEMENT AT LOW FACTORY PRICE @N1000 PER BAGS AND DELIVER TO ANYWHERE IN NIGERIA CONTACT DISTRIBUTOR MANAGER MR ABDU DANTATA FOR PURCHASE +2349038571819 OR +2348137579314."NOTE"PROMO ENDS BY 18th OF DECEMBER 2015?

    ReplyDelete