Tuesday, June 2, 2015

Yadda Na Fahimci Sabon Shugaban Kasa Janar Buhari

Daga Bashir Ahmad, Abuja

Janar Muhammadu Buhari wanda a ranar Juma'a (29/5/2015) aka rantsar da shi a matsayin sabon zababben shugaban kasar nan, Nijeriya, mutum ne kamar kowa, amma za a tara daruruwa ba a samu mai halaye irin na sa ba. Na fahimci hakan ne saboda damar da Allah ya bani na kasancewa a kusa da shi sosai yadda har na iya fahimtar shi wane ne. Na fahimce shi daidai kwarkwadon da zan iya rubuta babban littafi akan sa.

Farkon haduwa ta da Buhari, na fara magana da shi ne tun kafin na fara ganinsa ido da ido, har yanzu ina tunawa nayi wani rubutu ne akan sa mai take "Dalilina Na Son Janar Buhari" a wajajen 2009, cikin rubutun na bayyana cewa ni ban taba ganin Buhari ba, lokacin da yayi gwamna a tsohuwar jihar Arewa maso Gabas, yayi ministan albarkatun man fetur da shugaban hukumar NNPC, sannan ya zama shugaban kasa a mulkin soja ba a haife ni ba, haka kuma lokacin da ya jagoranci hukumar PTF bani da cikakken wayo da hankalin da zai sa na san halin da kasa take ciki, amma duk da haka na ji na taso da son sa cikin zuciyata, da kuma imanin idan ba shi Nijeriya ta samu ba, zamu iya kasancewa a lalace ba tare da mun koma mikakkiyar hanyar da a baya muke kai ba. Wannan shi ne ginshikin rubutun nawa, sannan na sa a shafina na yanar gizo (www.dandalinbashir.blogspot.com) wanda a lokacin na tabbatar dubban mutane za su ga rubutun kuma za su karanta, amma ko a mafarki ban taba tunanin wani na kusa da Buhari zai karanta rubutun har ya sanarwa Buharin ba. Amma sai Allah ya kaddari hakan, wani wanda har yanzu ban san ko wane ne ba, ya karanta rubutun nawa kuma ya kaiwa Buharin ya gani, watakila a lokacin Buhari ya kalli kananan shekaruna ne, shi ya sa abin ya burge shi, don haka sai ya umarci wanda ya kawo masa rubutun ya gani ya kira ni a waya mu gaisa da shi. Haka kuwa aka yi ina zaune na ga waya ta shigo, dama tun a baya a tsarina bana tantance kiran da zan amsa, nan take wannan kiran ma na amsa, bayan mun gaisa da wanda ya kira din, sai ya ce fatan yana magana da Bashir Ahmad ne, na ce kwarai shi ne, sai ya ce ya fahimci ina son Buhari, ko zan fada masa dalilin hakan, sai na bashi amsa da cewa ba zan iya cewa ga dalili ba, amma ina tunanin saboda na ga yadda ya rike manya mukamai a baya ne amma ba a taba samun sa da hannu cikin kowace irin almundahana ba, watakila haka ne ya sa zuciya ta aminta da shi nake sonsa, daga nan sai kuma ya sake tambaya ta ko na taba haduwa da Buharin mun yi magana, sai na ce ai ko ganinsa ma ban taba yi ba, sai ya ce to idan aka ce yau ga Buharin za kuyi magana ya zaka ji, sai na fada masa cewa zan yi farin ciki matuka, daga nan bai kara cewa komai ba sai ya ce ga Buharin za ku gaisa, hmmmm! Maganar gaskiya har yanzu na kasa kwatanta abin da na ji a zuciyata, kawai dai na ji an cewa Assalamu Alaikum, Malam Bashir, wato Buhari ne kenan ya karbi waya, har muka gama wayar ta kusan mintuna 3, na kasa cewa komai sai dai bada amsa da eh, na'am ko a'a.

Haduwar mu ido da ido, wannan kuma ya faru ne lokacin da ya zo Kano yakin neman zabensa a 2011, na gan shi a cikin mota zai je gidan Sarkin Kano, yana dagawa magoya bayansa hannu, amma mun fara magana ne bai fi shekaru biyu ba, a lokacin ina aiki da Jaridar Rariya, bayan kafa APC, an gudanar da wani taro a otel din Transcorp Hilton, a birnin tarayya Abuja, sai gani ga Buhari, ban ji tsoro ba, kuma na taki sa'a jami'an tsaronsa basu dakatar da ni ba, watakila don sun ganni da shedar cewa ni dan jarida ne, sai kawai na je inda yake a zaune na tsuguna na gaida shi ya amsa, sannan na ce Baba ni ne Bashir Ahmad na Kano, abin mamaki ina tuna masa kaina sai ya gane, mun danyi magana ta 'yan mintuna ya tambaye ni karatu da inda nake aiki duk na fada masa. Ba dadewa kuma sai na zama daya daga cikin ma'aikatan Sam Nda-Isaiah, a lokacin da yake neman takarar shugabancin kasa a APC, da yake koda yaushe ina tare da maigidana Nda-Isaiah sai ya zama muna yawan haduwa da Buhari akai-akai, na kan yawaita zuwa gaida shi har ya gane cewa ina tare da Sam ne wato muna takara tare da shi, amma ko kadan ban ga wani sauyi a fuskarsa ba.

Akwai ranar da APC ta gudanar da wani babban taro a Abuja, kowa a jam'iyyar ya halarci taron, ga shi kuma satin Sam zai kaddamar da takararsa a Minna, ni na je da katin gayyata na gwamnoni da duk manyan jam'iyyar don raba musu a wurin taron, ciki har da na Buhari, dana je kai masa na sa, bayan mun kaisa sai nace Baba ga kati muna gayyatarka taron kaddamar da takararmu, sai yayi dariya ya ce "Bashir ai ni da na kaddamar da tawa takarar ban ga kun zo ba, ni kuma sai ku gayyace ni na ku?" Sai na ce Baba ai lokacin dukkan mu mun zo, Oga (Sam) ne dai kawai bai zo ba, kuma shi ma lokacin yayi tafiya baya kasa ne da shi ma zai zo, sai ya ce shi kenan tun da haka ne na kara masa katin gayyatar uku ya zama biyar, da biyu na bashi, sannan ya ce idan suna gari za su zo. Haka kuwa aka yi a lokacin da aka gudanar da taron Buhari na Port Harcourt amma sai da ya tura wakilansa wurin.

Buhari baya ganin mutum a matsayin karami idan har yana da babban tunani, a ranar da aka gudanar da babban taron jam'iyyar APC a Lagos inda jam'iyyar ta gudanar da zaben fidda dan takara, wanda ya samu nasarar lashe zaben, tun ana cikin gudanar da zaben saboda ganin yadda zaben ke tafiya, sai na hau sama wajen da manyan baki suke zaune, naje wurinsa bayan na gaida shi sai na ce Baba na zo taya ka murna ne, sai ya ce ya gode sosai, ni kaina a wurin nayi mamaki sosai, wurin duk gwamnoni ne da shugabannin jam'iyyar amma mun kusa mintuna 10 ina tsugune Buharin ya sun kuyo kansa muna zance wanda ko wadanda suke kusa da shi ba wanda yake jin abin da muke fada, bayan na taso na sha kallo ta ko ina, kai akwai wani babban ma sai da ya taso ya biyo ni yake tambaya ta wai ni wane ne, sai kawai na ce ni SA ne na Sam Nda-Isaiah, sai ya ce "oh na gane".

Ban taba haduwa da wani babba da yake da rikon addini kamar Buhari ba, na je yakin neman zabe da Buhari a jihohi da dama ciki har da Borno, amma duk jihar da aka je idan lokacin Sallah ya yi kafin a fita filin taro sai ya yi Sallah kafin a fita, idan kuma ana filin taron lokacin yayi, to ana dawowa masauki ba abinda yake fara yi sai Sallah, akwai wata rana da aka dawo daga Lagos, ana sauka a filin jirgin Abuja, Buhari bai wa kowa magana ba, sai kawai ya wuce bandaki ya dauro auwala, anan dole sai da kowa ya tsaya ya idar da Sallah, sannan aka tafi. Kuma yana yawaita yin azumin Litinin da Alhamis.

Na san duk wanda ya san Buhari ya san cewa shi mai gaskiya ne da kuma rikon amana, to kullum abin Buhari yake jaddawa duk wadanda suke tare da shi kenan kan su rike gaskiya da amana za su ga amfanin haka tun a duniya.

Buhari yana da wasa da dariya, idan ana zaune da shi a wajen ba a yin shiru ba tare da ana murmusawa ba. Wannan shi ne Buharin da na sani, kuma yanzu shi ne shugaban kasar Nijeriya.

- Ni (Bashir) ina daya ne daga cikin membobin kwamitin yada labarai na shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma mataimaki na musamman ga Sam Nda-Isaiah, sannan ina aiki da Jaridar Leadership.

An fara buga wannan rubutun a jaridar Leadership ta ranar 29 ga watan Mayu, 2015, ranar da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.

1 comment:

  1. DANGOTE CEMENT FACTORY LOKOJA OBAJANA PLANT NIG PLC.WISH TO INFORM THE GENERAL PUBLIC OF SALES OF ITS CEMENT REDUCTION TO N1000 PER BAGS...CEMENT GRADE 50KG,THE MANAGEMENT NOW OFFER CEMENT AT LOW FACTORY PRICE @N1000 PER BAGS AND DELIVER TO ANYWHERE IN NIGERIA CONTACT DISTRIBUTOR MANAGER MR ABDU DANTATA FOR PURCHASE +2349038571819 OR +2348137579314."NOTE"PROMO ENDS BY 18th OF DECEMBER 2015?

    ReplyDelete