Monday, May 11, 2015

Buhari Na Ci Gaba Da Karbar Bakuncin Jakadun Kasashen Duniya

...Yau ya karbi jakadun kasashe 15 a Abuja

Zababben shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari na ci gaba da karbar bakuncin jakadun kasashen duniya, inda suke zuwa taya shi murna a madadin shugabanni da jama'ar kasashen su.

Yau ma kamar kullum Buhari a mazauninsa na wucin gadi, wato Defence House a Abuja ya karbi bakuncin irin wadannan jakadu, sai dai na yau ya bambanta da na kowace rana domin kuwa jakadun kasashe 15 ne suka kawo masa ziyarar kuma dukkan su ya zauna da sun don jin abin da ke tafe da su.

Kasashen da jakadun na su suka ziyarci Buhari a yau sun hada da: Japan, Holland, Kenya, Kuwait, Syria da Korea.

Sauran su ne: Iraq, Lebanon, Qatar, India, Algeria, Denmark, Serbia, Finland da Sweden.

Wannan na nuna cewa lalle karkashin jagorancin Buhari Nijeriya za ta zama abokiyar kusan dukkan kasashen duniya, kamar yadda a yanzu kasashen ke tururuwar ganin sun samu shiga a wajen sabuwar gwamnatin mai zuwa.

No comments:

Post a Comment