Monday, September 29, 2014

Tarihin Galadiman Kano - Alhaji Tijjani Hashim

Marigayi Galadiman Kano
An haifi Galadiman Kano Ahmadu Tijjani dan Turakin Kano Hashimu dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi I dan Sarkin Kano Ibrahimu Dabo a shekarar 1932 a cikin birnin Kano.

Ya fara karatun elementare a garin Bebeji a shekarar 1944. A shekarar 1944 ya shiga makarantar Medil ta Kano inda ya daina a 1951.

A 1952 ya fara aiki a En'e ta Kano da mukamin Malamin Dabbobi, mai duba tsaftar dabbobi da za a yanka a kara ta Kano. A 1956 aka zabe shi dan majalisa mai wakiltar Sumaila a majalisar dokoki ta Arewa.

A zaman sa a wannan majalisa ne ya rike mukamai da dama kamar shugaban hukumar bada kwangila ta Kaduna da shugaban kwamitin tabbatar da jam'iyyar NPC ta lashe zabe a lardin Sardauna. Ministan cikin gida na Jihar Arewa. Kwamishinan lardi mai kula Lardin Kabba wadda akan wannan mukami soja suka yi juyin mulki. Dawowarsa gida ne tasa Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero, ya nada shi sarautar Dan Isan Kano kuma kansila mai kula da ayyukan gayya da taimakon kai da kai.

A 1976 ya sami karin girma zuwa sarautar Turakin Kano da bashi kulawa da gundumar Kumbotso. A 1980, ya sami canji zuwa kansila mara ofis saboda yawan harkokinsa. A 1989, ya sami karin girma zuwa sarautar Dan Iyan Kano da ci gaba rike mukamin kansila mara ofis.

A1992, ya sami karin girma a babbar sarautar Kano a matsayin Galadiman Kano kuma shugaban kwamitin kudi na majalisar Sarki. A 2012 Sarki ya kara masa aikin hakimcin birnin Kano. Kuma a kan wannan aiki ya ke zuwa yau da Allah ya amshi ransa. 

"Galadiman Kano Tijjani mashahurin mutum ne da babu iri nai a wanga zamani wajen taimako, adalci, tausayi da kyautatawa. Shi kadai na sani a wanga zamani mai sarauta attajiri mashahuri Kasaitacce da za ka je wuri nai har ka tadda shi ba mai tambayar ka ina za ka". 

Allah ka dube shi, Ka yi masa rahma ka tausaya masa Ka jikansa, Ka sa Aljanna ce makomarsa.

3 comments: