Friday, September 26, 2014

Babu Tabbas Kan Mutuwar Shekau - Amurka


Gwamnatin Amurka ta ce har yanzu ba ta samu wata shaida da za ta tabbatar da ikirarin gwamnatin Nigeria ba, na mutuwar Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Wani jami'in harkokin wajen Amurka, Rodney D Ford ya ce suna ci gaba da kokarin tabbatar da sahihancin ikirarin gwamnatin Nigeria, da gaskiyar cewa akwai mutanen da ke shigar-burtu da sunan Abubakar Shekau.

A baya dai, rundunar tsaron Nigeria ta ce dakarunta sun kashe wani mutum da ke batar da kama da sunan shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau yayin fafatawa a garin Kunduga.

Mai magana da yawun shalkwatar tsaron Nigeria, Manjo Janar Chris Olukolade ya yi ikirarin cewa Abubakar Shekau ya jima da mutuwa amma wasu ke yin shigar-burtu don ci gaba da yada angizon kungiyar.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da batun mutuwar Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram.

- BBC Hausa

2 comments:

  1. GORON JUMMA`A:
    GAMEDAWA ZA`AYI MINI TAMBAYA A QABARI?
    Idan na mutu za`a yimin tambayane gameda MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAI WASALLAM, baza`a tambayeni mahaipfina ko mahaifiya ko malami ko shugaba ko sarki ko gomna ko mazhaba ko dariqa ko kunyaba, a`a za`a tambayeni gameda manzon Allah ne kawai.
    Idan har na gane babu wanda za`a tambaye a kabarina sai MANZON ALLAH to ashe babu wanda zanbi saishi kenan, kuma babu wanda zan yarda da maganarsa kai tsaye babu neman dalili sai manzo,
    Amma duk wani wanda zaka zaba a nan duniya ka bishi idan ka shiga kabari baza`a tambayeka shiba kuma idan kukaje filin qiyama wallahi gudu zaiyi ya barka.
    Da wannan zamu gane cewa ashe ba mutum zamu biba ayanzu aa maganarsa indai ta dace da kitabu wassunnan kuma a ko ina yake babu banbancin mazhaba dariqa kungiya ko karkashi.
    IMAM MALIK YAKE CEWA:
    "KO WANE MUTUM ANA KARBAN MAGANARSA KUMA ANA IYA WATSI DA ITA SAI MA ABUCIN WANNAN KABARIN" sai yai nuni ga kabarin manzon Allah sallallahu alai wasallam.
    DON HAKA BA`A DUBA MAI WA`AZI ANA DUBA WA`AZINNE abinda ya dace da kitabu wassunnanh sai a dauka abinda ya saba musu ko dayansu sai adauki kitabU wa ssunnan shi kuma abar masa kayansa wannan bai nuna an soke malantarsa ko an renashiba. domin babu ma`asumi sai manzanni, wassalam.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Godiya mai tarun yawa, Muhammad, Allah ya bada lada.

      Delete