Saturday, February 5, 2011

DALILAN DA YASA GENERAL MUHAMMAD BUHARI YA DAUKI PASTOR BAKARE A MATSAYIN MATAIMAKINSA

A farkon makon nan ne dan takarar
shugaban kasa a jam ’iyyar CPC, Janar
Muhammadu Buhari ya zabi Fasto Tunde Bakare ya zama mataimakinsa.
Don jin yadda aka yi, Aminiya ta tattauna da
shi, ta kuma ji ra ’ayin wasu na kusa da shi
kamar haka:
Aminiya: Me ya sanya ka nace sai Fasto
Tunde Bakare ya zama mataimakinka a
takara da kake yi ta shugabancin kasar nan?
Buhari: A tsarin jam’iyyarmu hakkin dan
takarar shugaban kasa ne ya zabi wanda
yake so ya zama mataimakinsa, shi ya
sanya na bukaci Tunde Bakare ya cika fom
Aminiya: Ana ta yada sakonnin waya da ke
nuna cewa zaben Buhari zaben Musulunci
ne, me za ka ce game da haka?
Buhari: Ban yarda cewa ’yan jam’iyyarmu
ne suke yada wannan sakonni ba. Ina ganin
daga abokan hamayya ne, kuma mun dauki
matakin magance matsalar, domin ba shi
yiwuwa ka iya neman goyon bayan
kowane bangare na kasar nan ta hanyar
amfani da addini, idan kana bukatar zama
shugaban kasar nan amma ka yi amfani da
addini ba za ka yi nasara ba, domin tsarin
mulikin kasar nan bai ce ga wani addini da
gwamnati za ta rike ba. A Najeriya
Musulunci da kiristanci ne manyan addinai,
amma akwai wadanda suka rude suka ce ba
su yarda da wani addini ba kuma su ma
kana bukatar kuri’arsu, yaya za ka yi da
irinsu?
Aminiya: So suke su ce kai mai tsananin
ra’ayin addinin Musulunci ne?
Buhari: Sun ma riga sun fadi haka, tun a
shekarar 2003 na ziyarci bishop-bishop da
ke kasar nan.
Aminiya: Saboda an dangantaka da addinin
Musulunci ne ya sanya ka jawo Fasto Tunde
Bakare ya zama mataimakinka?
Buhari: A’a, ba don haka ba ne, Fasto
Bakare ya zo har nan ofishin tare da
mutanensa ya zauna a inda kake zaune ya
ce ya yarda cewa nine na fi dacewa daga
cikin ’yan takarar da suka fito suna son su
shugabanci kasar nan. Kuma ya fada wa
mutanen cocinsa a ciki da wajen kasar nan
cewa ni ne dan takaran da ya fi dacewa.
Wannan ba maganar addini ba ce, magana
ce ta wanda yake da mutane kuma ya
amince da tsare-tsarenmu, kuma ya fito ya
bayyana haka ba tare da an roke shi ba. Tun
watanni takwas da suka gabata Bakare bai
zauna ba yana ta kaiwa da kamowa wajen
tuntubar mabiyansa tare da jawo
hankalinsu game da mu.
Aminiya: A shekarar 2003 an ce ka bukaci
kiristoci su zabi kirista, musulmi su zabi
Musulmi, haka ne?
Buhari: Wannan ya faru ne a shekarar 2002,
abin da ya faru shi ne, wani malamin
addinin musulunci ne ya rubuta littafi a kan
shari’a ya bukace ni in shugabanci
kaddamar da littafin, shekarun malamin sun
kai 70, na ce masa zan halarci wurin . Daga
cikin manyan bakin da suka halarta akwai
marigayi Sarkin musulmi Maccido Abubakar,
ina jin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari
ma yana wurin. Idan ka tuna a shekara
2002 ba na cikin harkar siyasa, saboda haka
bayan an kaddamar da littafin sai aka ce in
yi jawabi a matsayina na shugaban taro, na
dubi littafin na ga ni ban san komi ba game
da shi da zan sharhi a kai ba, marubucin
littafin ya zauna a kasar Saudiyya shekara
11 yana nazarin shari’ar musulunci da
musulunci, babu yadda zan yi sharhi a kan
littafin domin ban karata ba. Saboda haka
na ce, mutanen Sakkwato kun san
mutanenku, kwanan nan za a fara harkar
siyasa, don haka ku zabi mutanen da za su
yi muku aiki kuma su yi wa kasa aiki da
gaskiya. Ga alama dan jaridan da ya rubuta
labarin a jaridar Thisday ba musulmi ba ne
kuma Bayarabe ne, bai jin Hausa, sannan ba
a Sakkwato yake zaune ba, ta yaya ya sami
labarin?
Aminiya: Da hausa ka yi magana a wurin ko
da turanci?
Buhari: Da hausa na yi magana, domin da
hausa aka gudanar da taron, to, a ina ya
samo wannan? Wani ne kawai ya tsara
labarin, kuma wannan na daya daga cikin
matsalolin da muke fuskanta kasar nan.
Aminiya: Ta yaya za ka samar da fahimtar
juna a tsakanin mabiya addinai?
Buhari: Samun fahimtar juna a tsakanin
mabiya addinai yana da sauki, muhimmin
abu shi ne ilimi. Idan muka ilmantar da
mutanenmu za su iya kula da kawunansu
kuma ba za su saurari wani shirme daga
kowa ba. Amma idan aka bari hakar ilimi ta
gurgunce, aka kawo maganar bambancin
addini da kabilanci, hakan zai cutar da kasa
ne. Saboda haka amsar da zan ba ka ita ce
mayar da hankali a kan ilimi, kada
shugabanni su ji tsoron ilimantar da
mutanensu domin suna jin tsoron idan suka
samu ilimi za su yi musu bore. Ta yaya za ka
iya gina kasa ba tare da ilimantar da
mutanenta ba?

No comments:

Post a Comment