Wednesday, January 26, 2011

DALILAN DA ZASU SA NA ZABI GENERAL MUHAMMAD BUHARI (RTD)


Komai ba'a yinsa sai da dalili don haka nima ina da dalilai masu dumbin yawa da zasu sa na zabi General Muhammad Buhari, a zabe mai zuwa, duk da a zahirin gaskiya bazan iya kawo dalilan duka a rubuce ba, ba don komai ba saboda tarun yawansu amma dai zan dan fadi ginshikai daga cikinsu, su ma kuma dan kadan ba masu yawa ba.

Da farko idan akace General Muhammad Buhari anan Nigeria ko Africa kai koma nace ma a duk duniya ba wani bukatar dogon jawabi, domin kuwa sananne ne kuma sanin ba'a kan komai aka sanshi ba sai akan jajircewa don cigaban talaka sannan kuma kusan kowa yana yi masa kyakkyawan zaton shi mai gaskiya ne.

Ni dai a matsayina na dan shekara 19 a duniya, ba zance nasan lokacin mulkin General Buhari ba, wato lokacin da ya zama shugaban kasa a mulkin soja, sannan kuma bani da cikakken wayo a lokacin da ya rike hukumar PTF a mulkin General Sani Abacha.

Duk da haka da irin bayanai da nake karantawa, a jaridu, mujallu, litattafai da kuma shafukan na'ura mai kwakwalwa (Internet) da kuma labari da nake ji a wurin mutane wanda suka ga lokutan da yayi mulkinsa, tabbas zan iya cewa Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya da son talakawa.

General Muhammad Buhari, yayi aiki da rike manya manyan mukamai kala-kala a tarayyar kasar nan (Nigeria) yayi aikin soja har yakai mukamin zama General.
Sannan ya rike mukamin zama shugaban hukumar NNPC (hukumar man fetur) a lokacin mulkin General Olusegun Obasanjo na farko.

Sannan Muhammad Buhari ya zama shugaban kasa dungurugum duk bai dade ba amma kowa yasan yayi mulki na kwarai wanda hakan tasa har yanzu kowa ke yaba masa kuma ke muradin ganin ya sake dawowa don sake zama shugaban Nigeria, don samun cigaba mai amfani.

Buhari ya rike Hukumar PTF wanda babu bukatar fadin ga abinda General Buhari ya aiwatar a wannan hukuma, domin kuwa har a yau akwai irin ayyuka da jama'a ke amfana sama da shekara 10 ta wucewar wannan kungiya.

Abin mamaki duk da irin wannan manyan mukamai da Buhari har yanzu bai tara irin dukiyar nan da masu mulkin kasar nan ke tarawa ba, domin kuwa har yanzu Buhari gidanshi biyu tak a duniya Daura da Kaduna, wanda kowa yasan a kasar nan ko mukamin gwamna mutum ya rike to zaka same shi da gidaje sama da 10 gida da waje.

A karshe ni dai zabina a zaben 2011 shine General Muhammad Buhari kamar sauran zabuka biyu da suka wuce. Amma kuma idan akwai wanda yake ganin akwai wani dan takara da yafi nawa inganci da cancanta, to ina sauraronsa yazo ya fadamin gamsassun hujjojinsa zan bar nawa na zabi nashi. Amma fa Musulmi kawai don bazan taba zabar kafiri ba har abada indai za suyi takara da MUSULMI.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
+2348032493020

2 comments:

  1. Gaskiya bashir ka yi kokari kwarai da gaske, ina dada karfafa maka gwiwa ka ci gaba da wannan aiki na yada manufar General Buhari, Shugaban kasar Nigeraia 2011 in Allah ya so. Allah ya sa mu dace.

    ReplyDelete
  2. Gaskiya mal. Bashir kayi kokari , Kuma inamaka fatar Alkheri ya cikamaka Burinka na Alheri, Ameen.

    Daga Zayyanu Jabo, a Sokoto

    ReplyDelete