Kwaikwayon al’adu da fina-finan wasu:
Fina-finan Hausa sun ciri tuta wajen
kwaikwayon al’adu da kuma fina-finan
wasu kasashe da kuma kabilu, kamar su
Indiya (Bollywood), Amurka (Hollywood) da
sauransu. Hasali ma tarihi ya nuna fina-
finan Hausa na farko-farko an wanko su ne
daga fina-finan kasar Indiya, misali,
Soyayya kunar Rai (1995), wanda aka
kwaikwayi fim din Indiya mai suna Mujhe
Insaaf Chahiye (1983), Soyayya Rayuwa
(1996), wanda aka kwaikwayi Aadmi Chalte
Chalte (1982), Farin Gani (1997) wanda aka
kwaikwayi Raghubeer, Ikon Allah (1997) an
kwaikwayi Pet Pyaar Aur Paap (1984).
Bincike ya kuma nuna fim din Dijengala
(1999) an kwaikwayi fim din Return To
Eden, wanda shi kansa Return To Eden din
aka wanko shi daga fim din Khoon Baremag
(1992).
Hakazalika, idan muka koma fina-finan
Hausa na shekarun bayan kadan, misalan
fina-fiani irin su Dafa’i (Mis Production), an
kwaikwayi Ghayal, Nasara an kwaikwayi
Jeet, Gasa an kwaikwayi Mujse Shaadi
Karogi. Fina-finan FKD Production, irin su
Mujadala, an kwaikwayi Dillaghi, Khusufi, an
kwaikwayi Taal, Zo Mu Zauna an kwaikwayi
Khabi Khushi Khabi Gam, So, an kwaikwayi
Mohabbatein. Idan muka koma ga fina-finan
Hausa da suka koyi fina-finan kudancin
Najeriya, akwai fina-finan Hujja (Mai Shunku
Mobie) an kwaikwayi Disguise, Amaliya
(Al’umma Production), an kwaikwayi
Married to the Enemy. Sai Na Dawo (2-
Effect), an kwaikwayi The King is Mine. Duk
da cewar Yakubu Muhammad ya shaida
cewa sun dauko wata al’ada ce ta mutanen
kasar Ghana. Abin tambayar shi ne, ko an
taba samun inda masu shirya fina-finai na
wata kasa ko kabila sun kwaikwayi fina-
finan Hausa? Shin wannan al’adar da
Yakubu ya kwaikwayo tana da wata
muhimmanci ga al’ummar Hausa? Idan
babu, me ya sa mu muke dauko na wasu?
Fina-finan Indiya sun taka rawa wajen
sanya sunayen fina-finan Hausa da kuma
rubuta sunayen taurarin shirin fim. A wata
hira da na taba karantawa da mujallar fim
mai suna Tauraruwa, ta yi da Hafizu Bello,
ya shaida cewa an kirkiro fina-finan Hausa
don zamo wata garkuwa ta hana kallon
fina-finan Indiya da sauran fina-finai. Bisa
wani nazari da bincike ne da na yi na gane,
tun kafin a fara shirya fina-finan Hausa,
al’ummar Hausawa sun fi raja’a wajen kallon
fina-finan Indiya. To ganin haka ne, sai
masu shirya fina-finan Hausa suka dauki
zubi-da-tsarin fina-finan Indiya, don su ma
fim din su ya samu karbuwa. Wanda a
cewar su, tun da Hausawa suna kallon fina-
finan Indiya, idan suka yi fim irin na su, to
fim din su zai samu karbuwa.
Tasirin fina-finan Indiya a kan fina-finan
Hausa sun hada da: Sanya sunan fim irin
yadda Indiyawa suke rubuta sunayen fina-
finansu, da rubuta sunayen taurarin fim
kamar yadda Indiyawa suke rubutawa da
rawa da waka kamar yadda Indiyawa suke
yi a fina-finansu. Misalan sanya sunan fim
irin na Indiyawa: Baade de Heeral, Sitapurki
Geeta, Amir Aadmi Gareeb, Mere Jeeban
Saathi, Aadm Desh Pramee, Haseena Maan
Jaayegi, Khushi, Chori Chupke Chupke,
sakamakon amfani da Indiyawa suke da
kalmomi irin su ee da ch da kuma gh, sai
Hausawa suke rubuta sunayen fim din su
irin yadda Indiyawa suke. Misali: Huznee (H.
B. Production), Najjee (Multi Purpose
Concept), Jaheed (2-Effect), Zughi (AIDIM
International Company), Inganchi (Man
Entertainment), Khushu’i (Hali Dubu Mobies),
Khusufi (FKD Production) da fina-finai irin su
Chanji, Chanchanta da dai sauransu.
Rubuta sunayen taurarin fim kamar yadda
Indiyawa suke rubutawa: Mansoor Sadeek,
Abbas Sadeek, Ahmad Sani Sadeek, Sadeek
Ahmad, Kabeer Mai Kaba,
Sadeeya Gyale, Suleiman Sa’eed, Tijjani
Ibraheem da dai sauransu da aka rubuta a
fina-finai da yawa.
Waka da rawa: Kowa ya sani idan aka ce za
a kirgo ko lissafo wakokin Indiya da
mawakan fina-finan Hausa suka juya, to za
a dade ba a gama ba. Idan ka dauke
mawaka irin su Sani Yusuf Ayagi da
Mudassir Kassim da Misbahu Ahmad da suka
tsaya kai-da-fata wajen ganin sun rera
wakokinsu cikin siga da kamala da salo da
kuma karin waka irin ta Hausawa, sauran
mawaka irin su Yakub Muhammad, Adamu Hassan Nagudu,
Abubakar Sani, Mahmud Nagudu, Umar M.
Shariff, Sani Tudun Murtala, Auwal Adam,
Auwal Ishak, Nazifi Asnanic da sauransu, duk yawanci suna
rera wakokinsu bisa siga ta kwaikwayon
Indiyawa ko Sudan. Kai har da wakokin
Nasara, masu lakabin Hip-Hop, RnB, Blues da
sauransu, kamar yadda aka yi Kallabi (FKD
Production), Bakace (HB Production) da Tsumagiya (Sarari Ventures) inda Sani Danja
yake rawa irin ta Micheal Jackson, har
gawarwaki suna fitowa, da dai sauran
misalai. A cikin mawakan, gwanda-gwanda
Yakubu Muhammad yana kokari wajen rera
wakokinsa cikin salo, zubi-da-tsari da kuma
karin waka irin na wakokin Hausawa.
Hakazalika, idan aka ce za a lissafa raye-
rayen Indiyawa da aka kwaikwaya, nan ma
ba za a iya lissafawa ba. Dalilin faruwar
hakan kuwa yana da nasaba ne da rawar da
za a yi a waka tana tafiya da karin waka ne,
kuma yawancin karin wakar fina-finan
Hausa, sun samu tushensu ne daga wakokin
Indiyawa.
Idan muka koma al’adun Nasara ma, haka
kawai muka rika kwaikwayon su. Misali, a
fina-finan Hausa za ka ga taurarin da shiga
irin ta Nasara kuma wani abu za ka samu,
ba wai fim din ya kunshi da sai an yi irin
shigar ba ne. Inda za ka ga mutum ba
ma’aikacin banki ko wata ma’aikata ba,
amma za ka gan shi sanye da kwat. Wani
abu kuma, hakazalika a fina-finai da yawa,
sai ka ga jarumai maza, sanye da kaya Body
Hug, ko Yankees da dai sauransu. Haka abin
yake ga fannin mata. Akwai fim din da na
kalla, inda wata mata ta fito a Ustaziya,
amma da aka zo waka sai na gan ta sanye
da matsattsun kaya tana tikar rawa.
Har ila yau, haka kawai mawakanmu na
fina-finan Hausa, suka tsiro waka mai zubi-
da-tsari irin na Makosa, inda a cikin wakokin
nasa mawakin har wani lakabi yake wa
kansa da mai Makosar Hausawa. Ko a ina
Hausa ta samo Makosa kuma?
A karshe, ina kira ga masu shirya fina-finan
Hausa da su sani cewa, lokaci ya yi da ya
kamata su rungumi al’adu da addininmu
hannu biyu-biyu, su kuma zama masu kishi
da kare dukkan al’adun Hausa. Mu lura
yanzu, su kansu Amurkawa (Hollywood) sun
fi mayar da hankalin ga fina-finan al’adu,
kamar su Spartacus, Merlin, Legend Of The
Seeker da sauransu. A karshen–karshe, Allah
Ya sa wannan makalar ta zam mai
amfanarwa.
Bashir Musa, Marubuci, Manazarci da sharhi
kan al’amuran yau-da-kullum ne
08052585817, 08032493020
Salam! Malam Bashir Hakika kayi tsokaci mai gamsarwa akan yanayin fina-finan Hausa...Saura dame su wadanda akayi domin su Allah Yasa suji su kuma yi aiki da abun da aka fada domin ingantar da harshe, al'ada da kuma uwa uba addinin musulunci wanda shine addinin da Hausawa suka runguma shekaru aru-aru.
ReplyDeleteSaidai wani hanzari ba gudu ba, ance idan bera da sata to daddawa ma da wari, kamar yanda ka fada acikin tsokacinka cewa masu shirya fina-finan Hausa suna fim dinsu ne akan sigar fina-finan Indiyawa; to ana kana ganin idan suka bar wannan siga fina-finan su zasu samu karbuwa ga galibin Hausawa? musamman samari, 'yammata da kuma matan aure wadanda akasari sune suke kallon wadannan fina-finai. Anan ina ga dole sai anci gaba da wayarma da mutane hankula ta nuna muhimmancin dogaro da kuma tinkaho da al' adummu da kuma addininmu.
Allah Yayi muna jagora.
Sanusi Sama'ila Moyi
Mal. Sanusi tabbas maganarka haka take, amma kuma ai su suka yarda akan zasuyi fim din a bisa tunbar al'adar Hausawa, Al'adar Hausawa kuwa mafi yawancinta Musulunci ce, don haka kuwa kaga ai dole su hakura su dawo kan hanya. Don Musulunci ba a yi masa uzuri., amma kuma ai su suka yarda akan zasuyi fim din a bisa tunbar al'adar Hausawa, Al'adar Hausawa kuwa mafi yawancinta Musulunci ce, don haka kuwa kaga ai dole su hakura su dawo kan hanya. Don Musulunci ba a yi masa uzuri.
ReplyDelete