Thursday, January 13, 2011

MU FITA MU YANKI RIJISTAR ZABE DON ZABEN SHUGABANNI NAGARI

Hukumar Zabe ta kasa wato (INEC) ta bada sanarwar fara rijista masu kada kuri'ar zabe. Ranar Asabar 15th January zuwa ranar 29th January 2011 ga duk cikakken dan asalin Nigeria wanda shekarunsa suka kai 18 zuwa sama.

Wannan muhimmiyar dama ce ga dukkan matasa maza da mata masu kishin Nigeria da su fita don yin wannan rijista, domin da wannan rijista ne kadai zamu samu damar canja da kuma zaban shugabannin da muke ganin zasu yi mana wakilci nagari.

SHAWARA
Sannan ina bamu shawara da bin dokokin da sharadin wannan rijista, kamar fadin gaskiya indan jami'in rijistar ya tambaye ka, misali wasu zaka ga ko sunansu aka tambayesu basa fadin gaskiya ko me yasa oho.

Sannan kuma ka'idar wannan rijista ita ce kowane mutum sau daya zai yi, amma abin mamaki ko nace abin haushi sai kaga mutum shi kadai sai yayi rijista sama da guda 10 wai saboda ranar zabe ya samu kudi, Allah ya kyauta.

Tabbas wannan lokacin hukumar INEC ta tsaurara tsaro akan ganin kowa baiyi wannan rijista sama da guda daya ba, idan kuma mutum yayi aka kamashi akwai tara (Fine) mai ciwo ko kuma yayi gidan kurkuku (Jail).

To me yayi zafi da mutum zai damu kansa akan yin rijista sama da guda daya, har yaje a kai shi kurkuku ko aci tarar shi. Duk da haka kuma Malamai sun ce duk wanda yayi rijista sama da yadda akayi ka'ida to ya sabawa Allah (SWA).

Fatanmu mu fita muyi wannan rijista kuma muyi amfani da ita wajen zaben shugabanni nagari.
Allah ya taimake mu, Ya bamu shugabanni nagari masu kaunar talakawa.

Bashir Ahmad
Bashigy@yahoo.com
+2348032493020

No comments:

Post a Comment