|
Dalibai Na Karantar Kwamfuta |
Babu yadda za ayi dalibi ya kware a harkar kwamfuta matukar bai mayar da
hankalinsa wurin abin da malamansa suke koya masa ba.
Wani lokaci ba matsalar dalibai ba ce, matsalar abin da zasu yi practice da shi
shi ne matsala. Wadansu kuma a lokacin da suke koyan karatun hankalinsu baya
wurin malamin.
Idan mutum yana son ya kware kuma ya zama gwani a
duk harkar da ya sa a gabansa to ya sani sai ya baiwa wannan abun mahimmanci.
Misali zaka samu dalibai kowa na kokarin ya mallaki
kwamfuta amma kuma da zarar ya samu ba shi da abin da zai yi da ita face kallon
fina-finai ko kuma yin game ko kuma sauraron wakoki.
Ya ake zama gwani a harkar Kwamfuta? Hanya daya ce,
ka daukarwa kanka cewar ina son in zama kwararre a wannan fanni ta hanyar yin
kokarin ganin kana aikata ayyukan da aka umarce da su a makaranta.
Wani abu da yake kara goge dalibai shi ne lokacin
da dalibi ya dauki ragamar kara fadada bincike da maimaita ayyuka da malamai ba
su saka shi ba.
Misali ba yadda za ayi a ce ka san me zaka yi,
kawai ka dauko kwamfuta ka bude MS Word, ko Excel, ko Access, ko CorelDraw da
makamantansu baka san mene ne dalilin da ya sa na bude su ba.
Misali idan kana koyan aikin Graphics da CorelDraw
(Duk da cewar ba a yi shi don Graphics ba) to idan kana son ka zama gwani sai
ya kasance kana daukan wadansu takardu da aka yi Graphics din a ciki kana
kwatantawa.
Yin haka lallai zai taimaka maka wajen gano mene ne
na iya mene ne ban iya ba, a wannan lokaci zaka ga ka kara kwarewa a wani
bangare da da iya shi kayi, za kuma ka ga ka fahinci wani abu da da baka ma
gane me ake nufi da shi.
really i like your blog so nice and good:)
ReplyDeleteMak really, is good and wonderful, hope you understand the language he write with most of the time.
DeleteGaskiya mun karu sosai, Allah ya biya.
ReplyDeleteTo da kyau
ReplyDeleteEnter your comment... salam
ReplyDeletegodiya muke allah bar zumun ci
ReplyDelete