Monday, November 4, 2013

JARIDAR RARIYA A FUSKAR FASAHAR ZAMANI


Tambarin Jaridar Rariya

RARIYA jarida ce da take fitowa a duk ranar Juma'a, sai dai bayan haka akwai dama ga masu karatun jaridar da za su ci gaba da kasance wa da ita a kowane lokaci, kamar yadda manyan jaridun duniya ke tafiyar da harkokinsu a shafukan sadarwa na intanet, sakamakon ci gaban zamani, haka RARIYA ma ba a barta a baya ba.

•FACEBOOK: Rariya na da shafi a dandalin sada zumunta na Facebook, wanda cikin kankanin lokacin shafin ya zama kan gaba a tsakanin shafukan jaridun Hausa na Facebook. A halin yanzu sama da mutane dubu saba’in (70,000) ne ke samun labarai kai tsaye ta shafin RARIYA na Facebook. Shiga NAN don kasance da RARIYA a shafin Facebook.

•TWITTER: Ba kowace jarida ke da gurbi a shafin sadarwa na Twitter ba, amma RARIYA tun-tun-tuni ta samu gurbi a shafin, inda jama'ar da suka biye da ita ke samun labarai a koda yaushe ta wannan kafa. Za ku iya biyo RARIYA a Twitter akan @rariyajarida

•YANAR GIZO: A baya RARIYA ta fara kawo wa masu karatu labarai ta shafinta na (www.rariyaonline.com) wanda aka dakatar da shi, sakamakon wani muhimmin aiki da ake yi akan shafin don kara kawata shi, yayi daidai da salo na zamani, wanda nan gaba kadan shafin zai ci gaba da aiki.

•WAYAR SALULA: Sai wani sabon tsari da RARIYA ta fito da shi, wanda shi ne irinsa na farko a tsakanin jaridun Hausawa, tsarin ana kiran shi “RARIYA A WAYAR SALULA” tsarin na bawa masu amfani da shi damar samun labarun RARIYA a kullum a wayoyinsu na salula koda kuwa babu fasahar sadarwa a cikin wayoyin. Za ku iya shiga tsarin ta hanyar aika sakon RARIYA a wurin aika sakon tes a wayoyinku zuwa 700. A halin yanzu tsarin na aiki ne akan layin MTN kadai. Sannan za a caji naira 50 kacal har tsawon kwanaki bawai.

Ku ci gaba da kasancewa da RARIYA a kowane lokaci domin samun ingantattun labarai.

No comments:

Post a Comment