Friday, May 31, 2013

NEMAN SHAWARA: NI DA MATAR ABOKINA

Ni da babban abokina mun kasance masu sharholiya da 'yan mata a lokacin da muke kan samartakarmu, amma cikin rahmar Allah, daga baya Allah ya shiryemu. Har Abokina ya samu budurwar da zai aura. Soyayyar ta su ba ta dau lokaci ba suka daidaita suka yi aure.

Wata rana bayan 'yan watanni da daura musu aure, mu kayi alkawarin zamu kai ziyara Bauchi, abokin nawa yace min na shirya da safe misalin karfe 9:00am nazo gidan shi don a motarsa zamu tafi, nace masa to Allah ya kaimu. Tun 8:30am naje gidansa, nayi packing motata, sannan na karasa cikin gidan, da na shiga sai Matar shi tace min ''Ai kuwa abokin naka yace idan kazo na sanar dakai cewar maganar tafiyarku ba zata yiwu ba, don an kirashi a gurin aiki emergency, don haka yace saidai ku sake saka wata ranar'' Sai nace to ai ba komai, amma mai yasa bai kirani a waya ya sanar dani ba?'' sai tace itama bata san dalili ba. Har na Juya zan fita sai tace ''Bashir dama ina da maganar da nake son yi da kai'' sai na juyo nace wace maganace haka? sai tace '' Bashir kaima kasan cewar Tun lokacin da abokika yake neman aure na, idan ya min laifi kai nake gayawa'' nace kwarai kuwa, to yanzu laifin mai ya miki?'' sai tace '' Ni gaskiya bazan boye maka ba, Abokinka baya gamsar dani wajen kwanciyar Aure'' Da naji haka sai maganar ta daure min kai, kafin nace kamai sai taci gaba dacewa '' Gaskiya Bashir kai kam duk matar da ta aureka zata More'' sai nace ban gane mai kike nufi ba'' sai tace '' Gaskiya da alama zaka iya gamsar da dukkan 'ya mace, Gaskiya da zaka aminci da ka biya min bukata ta ko sau daya ne''.

Tana fadan haka sai naji maganar ta kona min rai, kawai sai na hauta da fada da masifa, ina cewa '' Amma kin bani kunya, Ban taba tunanin zaki iya furta irin wannan kazamar maganar ba, ina daukar ki mai hankali ashe ba haka bane, yanzu kina nufin inci amanar abokina kenan?'' Da taga dai babu kofa sai tace ''Haba wallahi dama wasa nake maka, gwadaka kawai nakeyi'' sai nace mata ''To bari kiji na gaya miki, daga yau sai yau karki kara min irin wannan wasan'' sai na dauki hanya na fita.

Mai gadin gidan ya bude min Gate, zan fita kenan da motata sai ga Abokina shima ya nufo da motarshi sai nayi packing, shima ya tsaya, na fito daga motata nazo gurinshi, sai nace masa ''Ance min kaje aiki'' sai yace eh wallahi wani dan aikine ya taso mana a gurin aiki amma har na gama, yanzu sai ka shigo ka packing motarka a ciki sai mu tafi a tawa. sai na shigar da mota ta na ajiye. sannan na shiga tashi motar na zauna ina jiranshi ya shiga gida yayi sallama da matarshi. sannan ya fito muka tafi.

Tun wannan lokacin nake ta tunanin anya da gaske take cewar gwadani takeyi? Anya kuwa idan ta samu dama ba zata ha'inci abokina ba?

Ina neman shawararku shin ya kamata na sanar da abokina irin matar da yake zaune da ita? ko kuna ganin na rufa mata asiri?

NT: Abin lura duk da cewar wannan labari gaskiya ne amma ba da ni BASHIR din ya faru ba.

Follow me on Twitter @BashirAhmaad

9 comments:

  1. subaha hanallahi gaskiya ka kara godiya ga ubangiji, ka kuma kara rokon tsari da shirrin wanna mata, yakuma kamata ka sanar da mijinta tare da kwakkwarar hujja don kada kana sane ya fada wata masifa ba tare da ka ceceshiba.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Gaskiya ne wannan Babangida, Allah ya kara kare mu daga sharrinsu.

      Delete
    2. Gaskiya matan bata kyautaba. In nine bazan qara zuwa gidan ba, sai dai muhadu da abokina a waje.

      Delete
  2. Saboda darajar aure kayi hakuri kar ka fada masa - Maryam Suleiman Abubakar

    ReplyDelete
  3. Bashir ka dai fadi gaskiya ko kai ne.... Lolz, ni ma shawara iri daya zan bada da Maryam. Allah ya kiyaye gaba.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Hmm da ka fadi sunanka da na baka amsa. Lolzzz

      Delete
  4. wadda ya rufa asirin wani Allah zai rufa masa nasa.

    ReplyDelete
  5. Hmmm ka gaya masa gaskiya kawai indai zaman amana kukeyi inyaso inma baya gamsar da ita ne da gaske sai ya nemi mafita karya jefashi cikin halaka dan dagaji ba maganar wasa a maganar nan

    ReplyDelete