Friday, May 31, 2013

Bazazzage Da Surukarsa Bakanuwa


Wani Bazazzage ne ya auri uwar gidansa Bakanuwa, wata rana ya raka ta ganin gida, sai aka kawo musu abinci irin na Kanawa hade da naman kaji, gogan naku saboda kunyar gidan surukai sai ya koshi, akai akai dashi yaci yace a'a. Nan aka ci gaba da hira da sirikarsa da matarsa da sauran mutanen gida, sai katsam aka dauke wuta, nan fa Bazazzage yaga duhu sai yasa hannu ya dauki cinya yana ci yana baza ido, ba za to ba tsammani kwatsam sai aka dawo da wuta. Sai gashi Bazazzage tsuru yana fisgar nama, nan fa kunya ta kama shi sai kawai ya fara kiran mis! mis!! mis!!! Hahahahahahahahaha!!!! Na sadaukar da wannan labari ga manyan dogarawa na Aliyu Danlabaran Zaria da Bashir Mukhtar Yusuf Zaria

1 comment:

  1. Wannan labari juya sa kayi, domin ta faru da wani Bakano ne. Kuma ni na sanshi na san unguwansu a cikin kwaryar birnin Kano. Hahahah

    ReplyDelete