Wednesday, August 8, 2012

Musulmai Ba Za Su Yi Ittikaf Wannan Shekarar A Jihar Kano Ba

Masarautar jihar Kano ta bada umarni dakatar da yin Ittikaf a masallatan jihar a wannan shekara.

Ittikaf dai ibada ce da Musulmai suke yin ta a lokacin watan Ramadan, musamman idan ya rage saura kwanaki goma, inda ake yin kaura daga gida zuwa manyan masallatai, domin kara zage dantse wurin yin ibada da kara neman kusanci ga mahalicci Allah, wannan ibada ta samo asali tun lokacin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW).

Sanarwar ta fito ne a daren jiya Talata, a kafafen yada labarai dake jihar ciki har da gidan rediyon Kano mallakin gwamnatin jihar. Duk da a cikin sanarwar ba a bayyana dalilin daukar wannan mataki ba, amma wata majiya ta bayyanawa RARIYA hakan na da nasaba da harkokin tsaro da yake addabar jihar.

Wannan dai shi ne karo na farko da hukumomi a jihar suka taba yanke irin wannan hukunci tun bayan jaddada addinin Musulunci da Shehu Usman Danfodio yayi a jihar ta Kano.

No comments:

Post a Comment