"Fatan Mai Rabo Guda Ne Baya Fada,
Don Kowa Ya ja Da shi Sai Ya Bar Masa,
Koda Dambe Ne Bare Filin Kokawa,
Kowa Zai Karo Da shi Sai Ya je Kasa,
Gode Wa Ubangiji Don Shi Yai Maka,
Domin Ka Sani Ma Nema Wasu Sun Rasa."
A karshe dai, bayan shekaru 51, Kano ta sake yin sabon Sarki, hakan kuwa ya faru ne bayan rasuwar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a ranar Juma'ar da ta gabata, wanda Allah ya bawa sabon Sarkin shi ne Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi, tsohon gwamnan babban bakin CBN. Sai dai wasu na ganin Sanusin ba shi ne ya cancanta ba, hasalima gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ne ya yi amfani da damarsa, ya yi karfa - karfa ya kakabawa Kanawa, Sanusi a matsayin sabon Sarki. Hmm, ni dai kam ina da ja akan hakan.
Maganar gaskiya, mafiya yawan jama'ar Kano, ba sa goyon bayan nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon Sarkin da zai jagorance su, kuma suna da dalilin su na yin hakan. Ko ni har ga Allah a zuciyata na fi so daya daga cikin 'ya'yan marigayi Sarkin Kano ya gaje shi saboda wani dalili na wa. Amma hakan bai sa na gamsu tare da yin addu'ar fatan alheri ga Sanusi Lamido a matsayin sabon Sarkinmu ba. Ba don komai ba sai don saboda na san Allah shi ke bada mulki ga wanda ya so, kuma a lokacin da ya so.
Duk karfin Sanusi, kudi da mukaminsa bai isa ya sa ya bawa kansa mulki ba, misali Sanusi ya rike mukamin gwamnan babban banki har na tsawon shekaru 5, amma hakan bai sa ya zama Sarkin Kano ba, sai lokaci da shugaban kasa, ya dakatar da shi, ko kuma na ce wa'adinsa ya kare, sannan Allah ya nufa zai zama Sarkin, kuma ya zama.
Kuma mu tuna cewa, da Gwamna Kwankwaso zai iya yin karfa - karfa ya dora wani ya zama Sarki, to ko tantama ba zan yi ba, da mahaifinsa, Mai Girma, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso ne zai zama sabon Sarki, tun da kuwa, shi ma basarake ne. Na san za ku amince da haka, saboda kuwa duk irin soyayyar da Kwankwaso yake yi wa Sanusi, ba ta kai wanda yake yi wa mahaifinsa ba.
'Yan uwana Kanawa na san abin akwai ciwo a zuciya, ga shi Allah ya dauki ran Sarkinmu da kowa yake so, sannan wanda ba ma so saboda wani dalilai ya zama sabon Sarkin.
...Sai dai na lura da cewa da yawa daga cikin mutanen da ba a Kano suke ba, suna matukar goyon bayan Sanusin a matsayin sabon Sarki, kuma su ma na hakikance suna da kwararan dalilan su.
Allah ya zaunar da Kano lafiya!!!