Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Wednesday, January 26, 2011
DALILAN DA ZASU SA NA ZABI GENERAL MUHAMMAD BUHARI (RTD)
Komai ba'a yinsa sai da dalili don haka nima ina da dalilai masu dumbin yawa da zasu sa na zabi General Muhammad Buhari, a zabe mai zuwa, duk da a zahirin gaskiya bazan iya kawo dalilan duka a rubuce ba, ba don komai ba saboda tarun yawansu amma dai zan dan fadi ginshikai daga cikinsu, su ma kuma dan kadan ba masu yawa ba.
Da farko idan akace General Muhammad Buhari anan Nigeria ko Africa kai koma nace ma a duk duniya ba wani bukatar dogon jawabi, domin kuwa sananne ne kuma sanin ba'a kan komai aka sanshi ba sai akan jajircewa don cigaban talaka sannan kuma kusan kowa yana yi masa kyakkyawan zaton shi mai gaskiya ne.
Ni dai a matsayina na dan shekara 19 a duniya, ba zance nasan lokacin mulkin General Buhari ba, wato lokacin da ya zama shugaban kasa a mulkin soja, sannan kuma bani da cikakken wayo a lokacin da ya rike hukumar PTF a mulkin General Sani Abacha.
Duk da haka da irin bayanai da nake karantawa, a jaridu, mujallu, litattafai da kuma shafukan na'ura mai kwakwalwa (Internet) da kuma labari da nake ji a wurin mutane wanda suka ga lokutan da yayi mulkinsa, tabbas zan iya cewa Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya da son talakawa.
General Muhammad Buhari, yayi aiki da rike manya manyan mukamai kala-kala a tarayyar kasar nan (Nigeria) yayi aikin soja har yakai mukamin zama General.
Sannan ya rike mukamin zama shugaban hukumar NNPC (hukumar man fetur) a lokacin mulkin General Olusegun Obasanjo na farko.
Sannan Muhammad Buhari ya zama shugaban kasa dungurugum duk bai dade ba amma kowa yasan yayi mulki na kwarai wanda hakan tasa har yanzu kowa ke yaba masa kuma ke muradin ganin ya sake dawowa don sake zama shugaban Nigeria, don samun cigaba mai amfani.
Buhari ya rike Hukumar PTF wanda babu bukatar fadin ga abinda General Buhari ya aiwatar a wannan hukuma, domin kuwa har a yau akwai irin ayyuka da jama'a ke amfana sama da shekara 10 ta wucewar wannan kungiya.
Abin mamaki duk da irin wannan manyan mukamai da Buhari har yanzu bai tara irin dukiyar nan da masu mulkin kasar nan ke tarawa ba, domin kuwa har yanzu Buhari gidanshi biyu tak a duniya Daura da Kaduna, wanda kowa yasan a kasar nan ko mukamin gwamna mutum ya rike to zaka same shi da gidaje sama da 10 gida da waje.
A karshe ni dai zabina a zaben 2011 shine General Muhammad Buhari kamar sauran zabuka biyu da suka wuce. Amma kuma idan akwai wanda yake ganin akwai wani dan takara da yafi nawa inganci da cancanta, to ina sauraronsa yazo ya fadamin gamsassun hujjojinsa zan bar nawa na zabi nashi. Amma fa Musulmi kawai don bazan taba zabar kafiri ba har abada indai za suyi takara da MUSULMI.
Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
+2348032493020
Friday, January 14, 2011
YAN AREWA KAR KU MANTA "NAKA FA SAI NAKA"
Jiya 14th January da misalin karfe 10:29 na dare, aka fara zaben fidda gwani (Primaries) na Jam'iyyar PDP inda aka bayyana sakamakon yau da safe da misalin karfe 5:58 na safe.
Yan takara uku ne suka fafata a wannan zabe:
1 - Atiku Abubakar
2 - Jonathan Ebele Goodluck
3 - Sarah Jibril
Sakamakon zaben ya nuna cewa Jonathan Goodluck shi yayi nasara a wannan zabe da gagarumin nasara.
An kada kuri'u 3,542
Goodluck - 2,736
Atiku - 805
Sarah Jibril - 1
Wannan zabe na cike da abin mamaki ko nace abin haushi musamman a wuri mutanen Arewa-Musulmi domin kuwa Goodluck a matsayinsa na Dan Kudu kuma kafiri shike da rinjaye a jihohin Arewan. Yayin da shi kuwa Atiku ko jiha daya baiyi nasara ba a cikin jihohin Kudu. Kuma wani abin mamakin Atiku har a mahaifarsa ma baiyi nasara ba wato Adamawa.
Ga sakamakon jihohin Adamawa da Bayelsa wato jihohin da Atiku da Goodluck suka fito:
(Adamawa)
Goodluck - 76
Atiku - 31
Sarah - 0
(Bayelsa)
Goodluck - 67
Atiku - 0
Sarah - 0
Wannan sakamakon shi kadai zai iya nuna mana rashin kishi a wajenmu mutanen Arewa-Musulmai, to duk kusan gaba daya sauran jihohin ma haka sakamakon yake, duk Atikun shi a kasa
.
A karshe ina jinjina ga Delegates na jihohin Kano, Sokoto, Niger da Zamfara da suka jajirce suka zabi Atiku Abubakar ba tare da kudi ya ja hankalinsu sun zabi kafiri dan Kudu ba wato Jonathan Goodluck.
Allah ya kyauta!!!

Thursday, January 13, 2011
MU FITA MU YANKI RIJISTAR ZABE DON ZABEN SHUGABANNI NAGARI
Hukumar Zabe ta kasa wato (INEC) ta bada sanarwar fara rijista masu kada kuri'ar zabe. Ranar Asabar 15th January zuwa ranar 29th January 2011 ga duk cikakken dan asalin Nigeria wanda shekarunsa suka kai 18 zuwa sama.
Wannan muhimmiyar dama ce ga dukkan matasa maza da mata masu kishin Nigeria da su fita don yin wannan rijista, domin da wannan rijista ne kadai zamu samu damar canja da kuma zaban shugabannin da muke ganin zasu yi mana wakilci nagari.
SHAWARA
Sannan ina bamu shawara da bin dokokin da sharadin wannan rijista, kamar fadin gaskiya indan jami'in rijistar ya tambaye ka, misali wasu zaka ga ko sunansu aka tambayesu basa fadin gaskiya ko me yasa oho.
Sannan kuma ka'idar wannan rijista ita ce kowane mutum sau daya zai yi, amma abin mamaki ko nace abin haushi sai kaga mutum shi kadai sai yayi rijista sama da guda 10 wai saboda ranar zabe ya samu kudi, Allah ya kyauta.
Tabbas wannan lokacin hukumar INEC ta tsaurara tsaro akan ganin kowa baiyi wannan rijista sama da guda daya ba, idan kuma mutum yayi aka kamashi akwai tara (Fine) mai ciwo ko kuma yayi gidan kurkuku (Jail).
To me yayi zafi da mutum zai damu kansa akan yin rijista sama da guda daya, har yaje a kai shi kurkuku ko aci tarar shi. Duk da haka kuma Malamai sun ce duk wanda yayi rijista sama da yadda akayi ka'ida to ya sabawa Allah (SWA).
Fatanmu mu fita muyi wannan rijista kuma muyi amfani da ita wajen zaben shugabanni nagari.
Allah ya taimake mu, Ya bamu shugabanni nagari masu kaunar talakawa.
Bashir Ahmad
Bashigy@yahoo.com

SHIN WANENE BARAWO A NIGERIA?
Shin waye barawo a Najeriya?
Kalmar barawo a kasar Hausa ba bakuwar
kalma bace, kusan duk mutumin da aka
ambaci barawo a kasar Hausa yasan da cewa
wani mutum ne da son zuciya ya rinjaye shi
ya dauki abin da bai ajiye ba kusan wannan
shi ne barawo, kuma barawo a Najeriya kala
kala ne domin wani dan sungume ne kawai
wani kuma zari ruga ya iya wani kuma haura
gida yake sa saci ‘yan tukwane da ludaya da
da sauran ‘yan kayayyakin amfanin gida wani
kuma zakaga babu abin da yafi kwarewa irin
satar awakin mutane wani kuma duk wannan
ba shi yake kayatar dashi ba abin da ya dame
shi shine yaje masallaci ya kwashi takalman
mutane, ko wayoyi ko kuma yabi sa ’a ya zari
wayoyin mutane a cikin aljihu batare da sun
ankare ba, kai wata satar kamar da asiri domin
mutumne bakasanshi ba zai zo ya nanike ka
ya kwaftara maka wata uban sata kamar kayi
hauka saboda irin yadda yayi amfani da
basira wajen yin satar, na ji wani mutum da
akayi masa sata irin wannan yace shi da zaiga
barawon to lallai da yayi masa kyauta domin
irin yadda ya nuna kwarewa cikin satar.
Kai kusan idan dai magana akeyi ta sata zamu
iya bugar kirji muce a iya zuwa najeriya ayi
kwas domin ‘yan najeriya sun kware kwarai
da gaske wajen iya sata, domin dukkan wani
launi na sata ‘yan najeriya sun iya shi, haka
kuma dukkan wani nau’I na mutumin da za a
kira barawo akwai shi a wannan kasar, a
wannan kasar tamu babu wani abu da ya
huce a sace shi domin wani abu da bazai iya
yuwuwa ba a inda aka cigaba shi ne a sace
mutum da ransa a yanka aci, a Najeriya
wannan ya zama ruwan dare uwa uba kuma
ga muggan barayi wadan da sukeyi da biro
wato fararen barayi wanda suna zaune a
guraren aikinsu suke kartawa akan takarda
suke satar kudin jama’a.
Ga duk mutumin da bai taba zuwa najeriya ba
zai dauk duk ‘yan Najeriya barayin domin
dukkan wani gida da kagani zakaga an sanya
karafan kariya waan da ake kira da suna
bugla duk wai don a hana mutumin da son
zuciya ra rinjaya shiga gidan da ba nasa ba,
haka kuma idan kaje ma’aikatun gwamnati
abin haka yake, kai kusan yanzu ko masallaci
ka shiga ka kuma coci zaka ga agogo da
kayan samar da sauti duk ansanya masu wasu
karafa ankare su daga daukan wanda bai
ajiye ba, wannan yake nuna irin yadda barayi
ke barazana ga rayuwarmu akoda yaushe.
Kuma wani abin mamaki shi ne hartana
agidan biki da mata suke zuwa zaka duk gidan
da akayi b iki aka gama zaka tarar anyi sace-
sace masu dama a wannan gidan tundaga
kayan abinci ko kuma kayan sawa ko kayan
masarufi koma kayan alatu, wani abin bam
mamaki da na gani shi ne wani gida naje da za
ayi biki mai gidan ya sanya akasiyo masa kaji
goma sha biyar da yake gidan babba ne sai ya
tura yaro ya kaimusu cikin gida shi kuma
yaron da ya kai kawai sai ya ajiye acikin falo
atakaice dai wadan nan kaji akasamu wata da
ta faki ido ta sanya su cikin hijabi tayi awon
gaba dasu wannan abu yabani mamaki to wai
shin wannan mata taje tacewa mijin tame, kai
dai idan namiji ne mai kishi dole ka tambayi
matarka ina tasamu wadan nan kaji, Allah ya
kyauta.
Bayaga ga sata da ‘yan najeriya suka kware,
ga kuma wata musiba da tayi mana katutu
itace mutuwar zuciya
Mutuwar zuciya agurin dan najeriya bawani
sabon abu bane domin kwana ki ina kan wani
titi a kano ‘yan Hizba na raba kayan agaji ga
masu rauni na buda baki kawai sai ga wani
mutum yazo da motarsa mai tsada ya tsayar
dasu suka dauko kulli uku suka bashi ya sanya
cikin mota kuma ya kara gaba Allah ya kyauta.
Haka kuma ga duk mutumin da yaje kasar
Saudiya da ‘yan Najeriya sukayi kaka gida
musamman ma idan Allah yasanya kaje
lokacin aikin haji zakaga yadda ‘yan Najeriya
ke hamburin hayam domin mutumin da ka
hakkake cewa shi ma zai iya sayan abinci da
kaza ya rabawa mutane sai ka ganshi alayin
karbar sabil, kuma wata hadama irin tamu shi
ne bamu iya daukar daidai bukatarmu ba sai
mun nika, don wani zaka ga ana raba burodi
sai ya karbi wajen goma amma kuma idan
anjima sai ya sake ganin anan rabawa kaga
yayi zuru-zuru kuma gashi kasce da babu
almajirai irin nan kasar.
Misali idan akace yau ga wani hamshakin
mutum na zakkar kudi aboye karkaso kaga
masu halin da zasu je karbar wannan kudi
kuma idan da zaka bishin sai kaga cea shima
zai iya bada sama da wadan nan kudin da
yaje karba Allah ya kyauta.
Na taba jin wani dan siyasa yace duk ‘yan
Najeriya barayi ne domin awani karin magana
da bahaushe ke cewa zama da madaukin
kanwa shike kawo farin kai ko kuma abokin
mugu mugu ne shima yace yanzu idan kana
da aboki shugaban karamar hukuma ko
gwamna ko shugaban kasa ko kuma
hamshakin mia rike da madafun iko idan ya
dauko kudi masu nauyi ya baka zaka karbe ne
kana godiya bater da ka tambayeshi ba cewa
shin wannan guminsa ne kuma kai kasan ba
noma yai yasamu ba kudin jama ’a ne.
Allah ka shiryemu shiri Addini kuma ka
azurtamu da wadatar zuciya da zamu iya
hakura da gwargwadon abin da muke dashi.
Daga karshe ina kira ga ‘yan uwana ‘yan
Najeriya ga zabe yana zuwa lallai ne dukkan
mutumin da yakai shekara goma sha takwas
ya fita yayi rigista aduk lokacin da hukuma ta
bada shelar yin rijistar masu kada kuri ’a, kuma
muyi kokari wajen zaben mutane na gari
wadan da zasu taimakawa kasarnan da
cigabanta. Allah ya sa ayi zabe lafiya agama
lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
Shugaban kungiyar Muryar Talakawa
Reshen jihar kano
07028690570

Subscribe to:
Posts (Atom)