|
Yusuf Dingyadi (Magayakin Garkuwa) |
Daga, Sharafaddeen Sidi Umar, Sokoto
Ko
tababa babu a duniyar aikin jarida Malam Yusuf Dingyadi ba ya bukatar
ko wace irin gabatarwa, kamar kuma yadda ya shige kan gaba a fagen
rubutu da marubuta tare da zama fitacce a haujin siyasar yau a
hobbasarsa ta ganin an samar da kyakkyawan shugabaci a tarayyar Nijeriya
bayan gurbacewar lamurra a tafin hannun shugaba Goodluck Jonathan.
Kwararre
ne da ke da kwarewa da gogewa a aikin da ya fi iyawa, wayo da lakanta,
hasalima shekaru da dama zuwa yau akwai masu ra'ayin a aikin jarida
Dingyadi ya yi wa tsara ratar da sai dai su biyo sahu, domin ko ba komai
caran da zakaransa ya yi an jiwo amonsa a ko'ina.
Wadanda suka
san shi, da wadanda suka kusance shi da wadanda suka yi hulda da shi sun
bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa tare da juriya da naci da
sadaukar da kai domin ganin an samu biyan bukatar da ake bukata a
lokacin da ake bukata ba tare da rashin biyan bukata ya rinjayi bukatar
da ake bukata ba.
Haka ma shekarunsa na rayuwa, shekaru ne da ya
rayu rayuwa tagari, rayuwa abin muradi kuma rayuwar Allah-sam barka ta
yadda aka shaide shi da biyayya ga magabata da mutunta tsara da kuma
zama lafiya da matasa. A daya gefen tare da kasancewa a bisa alkiblar da
yake ganin ita ce mafi a'ala kuma mafi dacewa a gareshi da sauran
al'umma ba tare da kaucewa alkiblar ba, duk kuwa da bukatar wasu ta son
ganin ya kaucewa inda ya dosa.
A haka jama'a da dama ba su yi
mamaki ba yayin da Garkuwan Daular Usmaniyya, Dakta Attahiru Dalhatu
Usman Bafarawa ya aminta da nadin mashawarcinsa ta fuskar aikin jarida a
matsayin Magayakinsa wato Magayakin Garkuwa, wanda zai shige kan gaba
wajen kariyar ko wace irin arangama da artabun da aka kai ko ake shirin
kaiwa Garkuwa a fagen fama kamar kuma yadda zai zamo Magayakinsa ta
fuskar rungumar kowace irin kwaramniyar murhun siyasa a yau da gobe.
Kari da karau Magayakinsa a aikin jarida. Yayin da shi kuwa Garkuwa zai
ci gaba da aikinsa na kariyar Katafariyar Masarautar Daular Usmaniyya da
dukkan karfinsa.
Kamar dai yadda aka sani marigayi Mai Martaba
Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido (Allah ya lullube shi da bargon Rahama)
ne ya nada Attahiru Bafarawa a saman sarautar Garkuwan Daular Usmaniyya
a farko-farkon hawansa kan karaga. Shi kuwa daga baya ya nada wasu
mutanensa a sarautu daban-daban a matsayin Sarakunan Garkuwa.
Haduwa Da Bafarawa:
A
tattaunawar musamman da ya yi da wannan marubucin, Dingyadi ya bayyana
cewar duk da cewar duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan ya san da
zaman Bafarawa, amma bai samu sa'ar fara hulda da shi ba sai a 1987, a
lokacin da Bafarawa ya kara yin fice wajen taimakawa al'umma musamman a
kungiyance a lokacin da yake jagorantar "Bafarawa social club". dan
jaridar ya ce "Mun shaku da Bafarawa sosai a 1993, hasalima daga lokacin
har zuwa lokacin dawowar mulkin siyasa muna tare duk da cewa ba mu taba
siyasa tare ba sai a 2007." Ya kara da cewar "Ina matukar farin ciki
sosai da a yau Garkuwa ya bani wannan sarautar ta Magayakinsa.
Kima Da Tasirin Bafarawa:
Magayayakin
Garkuwa ya bayyana Bafarawa a matsayin nagartaccen basarake kuma dan
gwagwarmayar siyasar cigaban al'umma wanda a jiya da yau hidimar al'umma
ya sa a gaba. Ya kuma ce Garkuwan Sakkwato "Dattijo ne a magana kuma
dattijo ne a kowane irin lamari, domin a bayyane yake bai taba sa kansa a
kowane irin lamari na ba daidai ba. A lura Garkuwa bai sa kansa a
lamarin sabon Allah, kuma bai sa kansa a wajen cutar jama'a, illa iyaka
ya kan sa kansa a duk wata harka da za ta amfani jama'a. Kazalika mutum
ne wanda ya san daraja da ciwon wadanda yake tare da su. Baya ga wannan
mutum ne mai son aiwatar da gaskiya tare da taimakon marasa gata." Ya
bayyana.
Ayyuka Da Tattaki A Cikin Tarihi:
Tattaki a
cikin tarihi za a ga Yusuf Abubakar Dingyadi ya zo duniya shekaru 40 da
suka gabata a Kwalfa da ke Gundumar Dingyadi a karamar hukumar mulkin
Bodinga. Bayan karatun addinin Musulunci a shekarunsa na farko, ya samu
kansa a karatun boko domin samun gishirin zaman duniya ta yadda a yau ya
ke da muhimman takardun ilimi.
Bisa ga sha'awar da yake da ita
ta aikin yada labarai, Dingyadi ya fara aikin jarida a Mujallar Zuma
mallakar Umaru Dembo a 1991. Ya kuma yi aiki da mujallar Nasiha a
1992-1993, daga baya kuma ya rika aikawa da labarai a mujallar Sentinel a
Kaduna gabanin ya samu matsugunni a Democrat.
Likkafar Dingyadi
ta yi gaba a yayin da sashen Hausa na gidan radiyon BBC ya yabawa
kwarewa da gogewarsa wadda ta zama silar daukarsa aiki a BBC a shekarar
1994, a matsayin wakilin gidan radiyon da ake aika labarai daga
tshohuwar jihar Sakkwato da Kabi da Katsina da kuma wani bangare na
Jamhuriyar Nijar.
Bayan barin BBC Hausa, Dingyadi ya zama
karamin daraktan yada labarai na yakin neman zaben Obasanjo da Atiku a
1999. Bayan samun nasarar lashe zabe ya zama mataimaki na musamman (P.A)
ga Ministan sadarwa, Alhaji Arzika Tambuwal, kamar kuma yadda ya zama
mataimaki na musamman ga Jakada Ladan Abdullahi Shuni a matsayin mai
kula da kididdigar 'yan Nijeriya da ke shiga birnin Casablanca daga
kasar Morocco. Ya kuma yi aiki a matsayin mataimaki na musamman kan
aikin jarida ga marigayi Garba Koko Sarkin Yakin Gwandu a lokacin da
yake a matsayin shugaban jam'iyyar SDP na jiha da kuma lokacin da yake a
matsayin shugaban makarantar horas da ma'aikata (ASCON) da ke Lagas.
Dingyadi
wanda a yanzu haka jami'in tuntuba ne kan yada labarai ga hukumar bayar
da ilimi bai daya ta jihar Zamfara (ZSUBEB); wasu ayyukan da ya yi a
baya su ne; mataimakin daraktan yada labarai na jam'iyyar SDP a bangaren
matasa, da daraktan yada labarai na jam'iyyar DPN duka a jihar
Sakkwato, da kuma sakataren kwamitin G-15, wadanda suka yi fafatukar
ganin Sule Lamido ya zama Gwamnan jihar Jigawa a 2007. Haka kuma ya rike
mukamin daraktan yada labarai na yankin Arewa na dan takarar
shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar DPP a 2007.
Daga 2007 zuwa
yau Dingyadi shi ne sakataren kungiyar marubuta ta kasa (ANA) reshen
jihar Sakkwato, haka ma shi ne mataimakin shugaban kungiyar matasan
marubutan Arewa wadda Farfesa Yusuf Adamu na jami'ar Bayero ke
jagoranta. Haka ma jami'in tuntuba ne ta fuskar yada labarai ga
Majalisar Tarayya ta shida da ta bakwa da ke wakiltar al'ummar kasa a
yau, haka kuma yana daga cikin jami'an tuntuba ga kungiyar mataimakan
'yan majalisar tarayya ta kasa reshen jihar Sakkwato.
Hidimar Al'umma:
Haka
ma a fili yake cewar Dingyadi wanda yayi takarar kujerar dan majalisar
dokokin jihar Sakkwato a tutar ACN domin wakiltar mazabar Bodinga ta
Yamma a 2011, za a ga wasu daga cikin kwamitocin da ya yi wa hidima a
matsayin manba sun hada da: Kwamitin rubuta manufofi da tsarin mulkin
jam'iyyar PDP a 1998, da manba a kwamitin samarwa 'yan asalin jihar
Sakkwato aiki a Gwamnatin tarayya daga 2000-2004 da kuma manba a
kwamitin gyara tsarin mulkin kungiyar marubuta ta kasa (ANA) a 2008 da
kuma manba a kwamitin sake mayar da alkibla da darajar Arewa wanda
kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta kafa a 2006 da kuma manba a kwamitin
sake daidaitawa da gyara koma]ar sha'anin ilimin furamare a jihar
Zamfara (ZSPEAC) da kuma manba a kwamitin shirya taron marubutan Arewa
wanda a ka gudanar a Kabi 2013.
Bugu da kari Dingyadi ya samu
mabanbantan karramawa da lambobin girmamawa da dama kamar kuma yadda
kamfaninsa na Dingyadi Media ya taka rawar gani. Kadan daga ciki su ne;
karramawa a matsayin dalibi mafi hazaka wajen karanta labaran safe da
kuma gwarzon dalibi wajen samar da ingantaccen tafarki a cikin Hakiman
makaranta duka a kwalejin Sarkin Musulmi Abubakar III.
Haka ma
ya samu lambar yabon wakilin jarida wanda ya tserewa abokan aiki wajen
aika labarai daga Arewa a Mujallar Nasiha. "Ka yi mun gani mun shaida"
hakan ce ta tabbata yayin da sadaukar da kai wajen aiki ta kai Dingyadi
ga samun lambobin yabo har guda biyu a zamansa a gidan radiyon BBC. Na
farko a matsayin wakilin BBC wanda ya fi kowa samun labarai a lokacin da
suke faruwa, da kuma dan jarida mafi aika labarai da dumi-duminsu a
gidan radiyon BBC. Baya ga wannan Dingyadi ya kuma zama dan jarida mafi
kwarewa a kafafen yada labarai na waje daga Arewa maso Yamma a
karramawar da aka gudanar a birnin Accra kasar Ghana a 2003.
Kamfaninsa
Dingyadi Media na tuntuba kan aikin jarida da yake jagoranta ya samu
lambobin yabo a matsayin gwarzon kamfanin yada labarai daga sashen
nazarin Hausa a jami'o'in Bayero da ke Kano da kuma Danfodiyo da ke
Sakkwato, tare kuma da karramawa daga Mujallar Beacon wadda ake bugawa a
jami'ar Bayero. Baya ga wannan manba ne a sama da kungiyoyi 20; daga
ciki akwai Dandalin Siyasa na duniyar gizo da majalisar Burin Zuciya da
ke cikin LEADERSHIP Hausa.
Littaffai:
Littaffan da alkalamin
Dingyadi ya rubuta sun hada da: Halina da Labarina da Ina Muka Kwana? Da
Dashen Masoya da Dacewar Yarima a 2003 da Barka Da Zuwa APC da sauransu
da dama. Baya ga wannan akwai mukalu da sharhi da rubuce- rubucensa da
dama da aka buga a jaridu da mujallun Hausa da Turanci.
Rana Ba Ta Karya:
A
yayin da mabanbantan al'ummar kasa suka shirya tsaf domin amsa kiran
wannan muhimmiyar sarauta wadda za a gudanar a gobe Asabar a fadar
Garkuwan Sakkwato da karfe biyu na rana; abin da zai biyo baya shi ne
yadda rayuwar Dingyadi za ta kasance a matsayin Basarake a gidan Sarauta
ba ya ga rayuwar da yake a kai ta fitaccen dan jarida, kwararren
marubuci kuma karbabben dan siyasar da ke fatar ganin gobe ta yi kyau
bayan ganin jiya da yau ta lalace a mulkin mallakar shugaba Jonathan.
- BASHIR AHMAD: Ina taya Mai Girma Magayaki, murnar wannan babban matsayi, Allah ya bada lafiya da nisan kwana. Na gaida Magayakin Garkuwa, Magayakin Matasan Arewa!!!