Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Thursday, May 31, 2012
Zan Fice Daga Filin Wasa Idan Aka Nuna Min Wariyar Launin Fata - Barotelli
Dan wasan Manchester City kuma dan kasar Italiya, Mario Balotelli ya yi barazanar ficewa daga filin wasa idan aka nuna ma sa wariyar launin fata a gasar cin kofin kasashen Turai, Euro 2012 da za a fara mako mai zuwa.
Ya ce muddin aka yi min wani abu da ya danganci cin mutunci wanda ya shafi wariyar launin fata to kuwa ba abin da zan yi illa na fice daga filin wasan na kama hanyata zuwa gida. Dan wasan ya ce ''ban amince da wariyar launin fata ba, kuma ba zan iya jurewa ba''.
Mu na shekara ta 2012 ne, abu ne da ba zai yuwu ba. Balotelli ya kara da cewa zai iya kashe duk wanda ya yi gangancin jefa ma sa ayaba akan titi (Abin da ke nufin maida shi tamkar biri), koda hakan zai yi sanadiyar tafiyar sa gidan yari.
Tsohon dan wasan na Inter Milan, dan shekara 21 yakan fuskanci matsalar wariyar launin fata akai-akai duk lokacin da ya ke buga wasa a kasar Italiya.
Daga BBC Hausa
Wednesday, May 30, 2012
Taimako: Bankin Musulunci na Barazanar Rashin Abokan Harka
Wani lokacin abubuwa suna bani mamaki, ka fin bude Ja'iz Bank PLC a kasar nan, wato bankin Musulunci da ba riba ko ruwa a cikinsa, abin kusan zama yaki yayi tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista. Ta bangaren Musulmai mutane da dama suna ta hura hanci sai an bude wannan banki, tunda dai Musulmai ne ke da rinjaye a Nijeriya, da sauran maganganu daban daban. Har wannan dalili ya sa daya bangaren mabiya addinin kirista suka shiga gaba da abin saboda a tunaninsu yin hakan kamar Musuluntar da kasar ne baki daya. Ba na mantawa har zanga - zangar nuna kin amincewa da kafuwar Bankin Musulunci a kasar nan, shugaban mabiya addinin kirista ya jagoranci wasu matasa. A haka cikin yardar Allah dai har aka kai ga nasarar bude bankin a wasu sassa na kasar nan.
Saboda jajircewa da gwamnan Babban Bankin Kasar nan, ya nuna Malam Sanusi Lamido Sanusi har bakin jini yayi a lokacin a wurin wadanda ba sa goyon bayan zuwan bankin.
Wani abin haushi yau gashi an bude bankin, kuma Musulman da suke ta fadin ko ana ha maza ha mata, ko ta halin kaka sai an bude bankin, yanzu sun ja baya, sun zubawa bankin ido kowa ya ki zuwa ya bude account ya fara ajiya a ciki. Wannan dalilin yasa bankin ya shiga barazanar rashin abokan harka (costumers), wanda kuma idan aka tafi a haka komai na iya faruwa.
Tabbas idan muka zuba ido muna gani wannan banki ya durkushe to lalle za ayi mana dariya, za a yiwa addininmu isgilanci, kuma za a dauke mu masu son addininmu a iya fatar baki, kuma wallahi idan hakan ya faru ko a ranar lahira sai Allah ya tuhume mu akan hakan.
Ya ku 'yan uwana Musulmai maza da mata, mu taimaki wannan banki, mu taimaki addininmu, mu garzaya zuwa cibiyoyin wannan banki na Ja'iz da suka fara aiki domin fara ajiya a ciki, hakan ne kadai zai taimaki wannan banki daga barazanar daya ke ciki a yanzu.
Ja'iz Bank PLC na da reshina a birnin tarayya Abuja, jihar Kano da kuma jihar Kaduna.
Fatan za ka/ki sanar da wadanda ba su sani ba.
Janar Buhari Ya Gudanar Da Bikin Ranar Demokradiyya a Jihar Nasarawa
Tsohon shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin kasa a zaben 2003, 2007 da 2011, sannan wanda talakawa ke burin ya sake tsayawa takara a 2015 wato Janar Muhammad Buhari ya gudanar da bikin zagayowar ranar Demokradiyya a garin Lafia fadar gwamnatin jihar Nasarawa.
Janar Buhari ya isa garin na Lafia da misalin 10:30 na safe, duk da zuwan nasa na ba zata ne, wato ya kai ziyarar ne ba tare da sanarwa ba, amma duk da haka bai samu isa filin da aka tanada don yin taron ba sai wajen 11:30 saboda dafifin magoya baya, daga nan taro ya fara, manyan baki suka yi jawabai ciki har da Mai Girma Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Umar Tanko Al-Makura, amma mai gayya mai aikin Janar Buhari bai samu damar yin jawabin a wurin ba.
Idan ba a manta ba Janar Buharin ya taba kai irin wannan ziyata ta ba zata jihar ta Nasarawa a shekarar da ta gabata lokacin rantsar da gwamna Al-Makura.
Janar din ya samu rakiyar mutane da dama ciki har da tsohon ministan birnin tarayya Abuja, Malam Nasir El-Rufai.
Yadda Rikicin Tattalin Arzikin Turai Zai Shafi Kasashen Afrika
A halin yanzu kashi daya bisa uku na kayayyakin da Afrika ke fitarwa tana kaisu ne zuwa kasashen Turai. Haka kuma Afrika na samun fasaha da ayyukan kwararrun da take takama da su daga nahiyar Turai, sai dai wadannan abubuwa na iya fuskantar koma-baya sakamakon rikicin tattalin arzikin Turan.
Don haka koma-baya a tattalin arzikin Turai zai haifar da raguwar kayayyakin da Afrika ke fitarwa. Kuma duk wani koma-baya a kudaden da ake samu daga kasashen waje, musaman a yankin kudu da sahara, to babu shakka zai haifar da mummunar illa ga jama'ar yankin.
Babu makawa, illar za ta banbanta daga kasa-zuwa-kasa - adadin kayan da kasa ke fitarwa zuwa Turai da kuma ingancin manufofin tattalin arzikinta. Baya ga raguwa wurin adadin kayan da ake fitarwa, akwai wasu ababen damuwa ganin yadda Turai ke fadi-tashin shawo kan matsalar basukanta:
Yiwuwar rage tallafi daga kasashen waje saboda kasashen Turai na kokarin tallafawa matasansu da basu da aikin yi da kuma sauran bukatu na yau da kullum.
Raguwa wurin kudaden da ake aikowa da su Afrika saboda 'yan nahiyar da ke zaune a Turai, za su fuskanci rashin aikin yi a Turai. .
Raguwar kudaden shiga ta fannin yawon bude ido, saboda Turawa na fama da matakan tsuke bakin aljihu. .
Koma-bayan tattalin arziki baki daya: Hukumar kula da ci gaban tattalin arziki ta OECD, ta yi hasashen cewa kayayyakin da nahiyar Afrika ke samarwa za su fuskanci koma-baya da kashi 0.7 da kuma 1.2 a 2012 da kuma 2013.
Dukka wannan koma-baya ne ga nahiyar da ke dauke da kashi daya bisa uku na talakawan duniya, da rashin katabus wurin cimma muradun karni (MDGs).
WASU KASASHEN ZA SU IYA KAI LABARI
Sai dai duk da haka, kasashen Afrika da ke da ci gaba da kuma kyakkyawan tsari, ka iya jawo hankalin masu zuba jari sakamakon matsalar da ake fuskanta a Turai.
Alal misali, Afrika ta Kudu da Ghana da ke da zaman lafiya, ka iya samun masu zuba jari fiye da Masar da Mali wadanda ke fama da rikice-rikice. Baya ga haka, fannin ma'adanai na Afrika zai ci gaba da jan hankalin masu zuba jari daga Turai da kuma wasu wuraren saboda alfanun da ake samu daga fannin.
Hakan ne kuma ya sa Najeriya, ke ci gaba da samun masu zuba jari a fannin mai da iskar gas, duk kuwa da tashin hankalin da ake fama da shi a kasar. Matsalar ita ce zuba jari a fannoni masu kawo riba sosai bai fiye yin tasiri kan rayuwar talakawa ba.
A takaice, ya kamata Afrika ta tashi tsaye wurin tunkarar koma-bayan tattalin arzikin da ake fuskanta a duniya ta hanyar shimfida manufofin da za su bunkasa sauran fannonin tattalin arziki, da ayyukan ci gaba, da inganta ayyukan gwamnati da bunkasa alaka tsakanin yankunan nahiyar.
Daga Farfesa Murtala S. Sagagi
Na Jami'ar Bayero, Kano.
Rahoto daga BBC Hausa.

Tuesday, May 29, 2012
Ina so kasata Nigeria....... Ku fa?
NIGERIA: Har yanzu Nigeria tana raina kullum ina sata a cikin addu'ata, saboda sanin ita ce kadai kasata ta haihuwa, koda ma na bar ta zuwa wata kasa nan din dai shi ne asalina. Wannan dalili ya sa kullum nake kara tursasa zuciyata akan soyayyar kasar tawa.
Shin kai/ke ma kuna son Nigeria? Kuna yi mata addu'a kodayaushe?
Sakona Zuwa Ga Shugaba Goodluck Jonathan
Kamar yadda kowa ya sani yau May 29 rana ce ta farin ciki ga kasar Nijeriya, amma kuma ranar bakin ciki ga mafiya yawan 'yayanta, saboda ranar ne ake nada sabbin barayi a matsayin jagororinmu.
A kashen duniya daban daban musamman masu bin tafarkin demokradiyya idan irin wannan rana ta zagayo musu 'yan kasar sukan rubuta sakonni kala kala don aikawa da shugabanninsu na taya murna da zagayowar ranar da kuma neman ayi musu wasu ayyukan ci gaba a wasu bangarori dake bukatar hakan. Sannan kuma shugaban ya fito fili ya yiwa 'yan kasar jawabin irin ci gaban da suka cimma a shekarar da ta gabata.
To yau ni ma zanyi koyi ga irin wadannan al'ummoni, wato zai aikawa shugaba Goodluck Jonathan sakona a wannan rana ta farin ciki.
Sakona zuwa ga shugaba GEJ: Ya mai girma shugaban tarayyar Nijeriya da ta hada da shiyoyi guda shida, jihohi 36 tare da birnin tarayya Abuja, ina taya ka da sauran 'yan kasa murnar zagayowa wannan rana wadda ka cika kwana 365 a karagar mulki baya ragowar mulkin Marigayi Malam Umar Musa Yar'adua da ka karasa. Ya mai girma shugaba muna yaba ma da irin kokarinka na fitowa kafafen yada labarai kana bayyana irin tsare tsarenka, sai dai kash! Har yanzu baya karasowa wurin talakawa bamu sani ba ko baka san da hakan ba.
Shugaba GEJ yau shekararka daya kenan akan gadon mulki, a lokacin da kazo jiharmu Kano yakin neman zabe ka yi mana alkawarin za mu shaki Fresh Air idan ka samu damar kaiwa bantenka, amma sai gashi har yanzu iskar ko yankinmu na Arewa ma bata karaso ba, kuma wadda muke amfani da ita a da, tun daga hawanka ta gurbace, fatan za ka tuno alkawarin da ka daukar mana kuma ka cika mana shi. Kafin wata shekarar mai dawowa. Muna yiwa maka fatan karasa mulkinka lafiya.
A karshe ina fatan sakona zai samu isa kunnuwan mai malafa.
Sunday, May 27, 2012
Shin Ranar May 29 Tana Da Muhimmanci a Gare Ka?
Ranar 29 ga Mayu kowace shekara rana ce ta tarihi, kuma rana ce ta hutu a dukkan fadin kasar nan, tun daga shekarar 1999, wato a ranar ne mulki ya dawo wurin farar hula daga hannun sojoji masu kaki. Wannan dalili ya sa ake kiran ranar da suna "DEMOCRACY DAY" wato ranar Demokradiyya. Dukkan kasashen da suka kan tsarin demokradiyya 'yan kasar sukan shirya gagarumin bukuwa idan ranar irin wannan rana ta zagayo musu, ranar da mulki ya dawo hannunsu, suke da wuka da nama a cikinsa, wato suke da 'yancin zabe ko su shiga takara a zabe su.
Ba komai yake sa jama'a farin ciki ba idan irin wannan rana ta zagayo, sai don yadda 'yancinsu shi ne kan gaba sama da komai, saboda wannan dama da suke da ita ta 'yancin zabe, saboda ta haka ne kadai suke da damar canja duk wani shugaba da yayi musu alkawari ya kuma saba musu.
Saboda irin wannan 'yanci wasu kasashe da dama suka fafata yaki suka sadaukar da rayukansu domin samun 'yancin. A baya bayan nan kasashe irin su Tunisia, Egypt, Libya da sauransu duk sai da suka zage kwanji kafin 'yancin nasu ya samu. Amma mu Nijeriya mun samu wannan 'yancin ne cikin ruwan sanyi ba tare da ja'inja ba. Sai dai kash! Mafi yawa daga cikin al'ummar kasar ba sa amfana da wannan 'yanci, saboda ba kasafai suke zaben ake basu wanda suka zaba ba.
Wannan dalili yasa ko da irin wannan rana ta Demokradiyya ta zagayo ba mu fiye ba ta muhimmacin kamar wadanda suke cikin ribar demokradiyyar ba. Da dama cikin 'yan Nijeriya ba sa sani zuwan rana, balle sanin muhimmacinta. Duk kuwa da dumbin muhimmancinta a gare mu.

Wednesday, May 2, 2012
CHELSEA ZA TA IYA YIN NASARAR DAUKAR KOFIN ZAKARUN TURAI
Kungiyar Chelsea da ke taka leda a kasar England za ta iya yin nasara a karawar da za tayi da kungiyar Bayern Munich ta kasar Germany a was an karshe na cin kofin zakarun turai (UEFA Champions League) wanda za a fafata a ranar 19 ga Mayu da muke ciki, a filin wasa na Allianz Arena take birnin Munich.
Akwai wasu dalilai da idan tarihi ya maimaita kansa za su sa Chelsea lashe kofin na zakarun turai. Wadannan dalilai ko nace tarihi sune:
A duk lokacin da Munich ta dauki nauyin wasa karshe, ana samun kungiyar da bata taba daukar kofin ba tana yin nasara. An yi wasannin karshe a filin na Allianz Arena sau uku, wanda Nottingham Forest ta kasar England ta samu nasarar lashe kofin karo na farko a shekarar 1979, sai Marseille ta kasar France ita ma ta dauki kofin karo na farko a filin wasan a shekarar 1993, sai kuma Dortmand ta Germany tayi nasara a shekarar1997 ita ma a karo na farko.
To saboda haka idan Chelsea ta dage za ta iya zama kungiya ta hudu da ta fara yin nasarar daukar kofin a filin na Allianz Arena.Sai kuma wani tarihin makamancin haka, tarihi ya nuna ba kungiyar da aka taba yin wasa a filin wasanta kuma tayi nasarar daukar kofin, hasalima kungiyar AS Roma ta kasar Italy itace kadai ta taba yin nasarar zuwa wasan karshe ta doka a filinta, sai kuma Bayern Munich a wannan lokaci.
Ita ma Roma ba ta yi nasarar daukar kofin ba a filin wasanta na Olympic wanda ya gudana a shekarar 1984.Wannan ma wata dama ce da za ta karawa kungiyar ta Chelsea kwarin gwiwa, ita da magoya bayanta baki daya.
To mu dai kallo ne kadai namu, sannan “ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare” in ji masu iya magana.
Bashir Ahmad
bashgy90@yahoo.co.uk

Will You ‘Occupy Nigeria’ Again? Wole Soyinka, Tunde Bakare, Save Nigeria Group to Organise Mass Protests over Fuel Subsidy Scam
Early this year, when the President of Nigeria, Goodluck Jonathan announced a removal of the fuel subsidy, increasing the price from N65 to N141 per litre, Nigerians came out to the street in large numbers, protesting the increase until the price was reduced to N97. From North to South to East to West, the streets were taken over by citizens protesting the hike and for once in a long time, we spoke with one voice.
Now, few months later, reports by the Farouk Lawan led House of Representatives’ Ad -Hoc Committee on Fuel Subsidy probe has revealed that over N1.7trn was looted by fuel marketers and government agencies.
The news has come as a shock to Nigerians who feel sorely cheated. While the Federal Government was giving excuses that it could no longer fund subsidies on the price of fuel and wanted to use the money for other developmental projects in the country, the money has actually been there all along but was looted by some agencies including the the Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC), Petroleum Product Pricing Regulatory Agency(PPPRA), Department of Petroleum Resources, Office of the Accountant General of the Federation and other petroleum marketing companies.
To protest this, convener of Save Nigeria Group (SNG), Pastor Tunde Bakare, and others recently served notice to the Federal Government of another round of mass protest in Lagos and other towns in the country, following the House of Representatives’ report on how over N1.7trn was looted by fuel marketers’and government agencies.
Similarly, Nobel Laureate, Wole Soyinka, another leader of the group at a press conference urged Nigerians to get ready for another determined protest over the fuel subsidy scam adding that the Farouk-Lawan report shows that Nigerians have been dehumanized.
“I have studied the figures revealed by the probe and I pinch myself to be sure that I am really living in the real world. Nigerians are being bludgeoned into sensitivity by sheer excessive corruption by public officials. We are being treated, not even as second class citizens, but excessively dehumanized,” Mr. Soyinka said.
Mr. Bakare queried how Nigeria spent N3 trillion in 2011 above the N245 billion budgeted for subsidy the same year, as revealed by the probe. He commended the House of Representatives for its consideration and adoption of the subsidy probe report in a record time of two days.
“In 2011, the report reveals that we spent almost N3tn on subsidy, and the ones (subsidies) paid for the previous years were lower than that. Do they think we are idiots? This shall go down in history as one act of redemption by a chamber of the National Assembly that has not done much since 1999, to endear itself to the people it represents,” he said.
He said that the time had come to save Nigeria from the grip of corruption, warning that the SNG would call the people out for massive protests if those indicted were not seen to be prosecuted speedily.
Mr. Soyinka on his part urged the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) and the Independent Corrupt Practices Commission (ICPC), to immediately launch the prosecution of all those involved to prevent Nigeria from being a laughing stock in the world.
“So far, we have not heard any of the figures disputed by relevant government parastatals in the oil industry. The facts on ground are enough for the EFCC and ICPC to establish a prima facie case against those indicted,” he said.
The SNG said that it had started dissecting the report, adding that another “Occupy Nigeria”, was imminent if government failed to act swiftly in prosecuting the culprits.
If these protests go on as planned, it would be the second time this year Nigerians are protesting over Fuel Subsidies.
So, are you in support of the protests? Do you think massive protests is what we need to push the Federal Government into action on prosecuting the culprits? Will you join them to ‘Occupy Nigeria’ once again?
Via NAN/Punch Newspaper
Subscribe to:
Posts (Atom)