Wednesday, August 8, 2012

Musulmai Ba Za Su Yi Ittikaf Wannan Shekarar A Jihar Kano Ba

Masarautar jihar Kano ta bada umarni dakatar da yin Ittikaf a masallatan jihar a wannan shekara.

Ittikaf dai ibada ce da Musulmai suke yin ta a lokacin watan Ramadan, musamman idan ya rage saura kwanaki goma, inda ake yin kaura daga gida zuwa manyan masallatai, domin kara zage dantse wurin yin ibada da kara neman kusanci ga mahalicci Allah, wannan ibada ta samo asali tun lokacin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW).

Sanarwar ta fito ne a daren jiya Talata, a kafafen yada labarai dake jihar ciki har da gidan rediyon Kano mallakin gwamnatin jihar. Duk da a cikin sanarwar ba a bayyana dalilin daukar wannan mataki ba, amma wata majiya ta bayyanawa RARIYA hakan na da nasaba da harkokin tsaro da yake addabar jihar.

Wannan dai shi ne karo na farko da hukumomi a jihar suka taba yanke irin wannan hukunci tun bayan jaddada addinin Musulunci da Shehu Usman Danfodio yayi a jihar ta Kano.

Cristiano Ronaldo Ya Yi Nasara Zama Zakaran Shekara a Shafin Goal.com

Dan wasan gaba, na kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya zama Zakaran Shekara a shafin yanar gizo na Goal.com (Goal.com 50 Prices) na 2011/2012.

Shafin na Goal.com a duk shekara yana sanya gasar ne ta zama zakarar shekara a tsakanin gwarazan 'yan wasan kwallon kafa guda 50 wanda makaranta shafin ke zaben wanda ya fi cancanta a tsakanin 'yan wasan.

Ga jerin 'yan wasa 10 farko da suka fi samun maki:

1. Cristiano Ronaldo 38.82%
2. Lionel Messi 35.51%
3. Andrea Pirlo 12.25%
4. Didier Drogba 5.46%
5. Iker Casillas 4.07%
6. Andres Iniesta 1.57%
7. Yaya Toure 0.72%
8. Xavi Hernandez 0.63%
9. Ashley Cole 0.58%
10. Sergio Ramos 0.4%

Wannan nasara da Ronaldo ya samu za ta iya taimaka masa wurin lashe kambun gwarzon dan wasan duniya na Ballon d'Or da hukumar FIFA ke sanyawa a duk shekara ga dan wasan da ya fi gwazo a fadin duniya ta fannin kwallon kafa.

Daga Jaridar Rariya