Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Monday, April 30, 2012
Shekara Daya Bayan Zaben 2011
A nawa tunani ba abin da ya kai tarihi dadi. Dadin nasa kuwa ya fi armashi a lokacin da mutum ke biye da aukuwar tarihin cikin natsuwa da fahimta da kuma nazari. Shi tarihi kamar yadda masana suka yi nuni ba wani abu ba ne sai wanzuwar al’amurran da mutum da kan sa ya gina ya kuma tabbatar da gudanuwarsa. Dukkan abin da ka aikata dazu-dazun nan ko jiya ko shekaran jiya ko kuma wasu kwanaki ko watanni ko ma shekaru a baya su ne tarihinka ko tarihin al’umarka. Yake-yake da takaddamar mulki da aure da siyasa da neman ilmi da ma dukan zamantakewar yau da kullum cike take da taskokin rayuwa na tarihi. To amma shi tarihin nan da muke magana ba kowa ke gane aukuwarsa ba, ba kowa ke fahimtar irin wainar da ya toya ba, ba kowa ne ke cin moriya ko gajiyarsa ba. Ba kuma wani abu ya jawo haka sai ganin cewa sinadiran da ke dabaibaye da aukuwar tarihi masu sarkakiya ne, fahimtar su sai mai riskar al’amurran bisa yadda ya kamata.
Ke nan tarihi shi ne rayuwa, fahimtarsa ko gane aukuwarsa ita ce gishirin rayuwar, aiki da abin da tarihin ya kyallaro kuma shi ne abincin rayuwar. Shi ya sa masana ma ke ikirarin duk wanda bai san abin da ya faru ba( a gidansu, ko unguwa ko kauye ko kasa) kafin a haife shi, wato bai nakalci tarihin rayuwarsa ba, zai kasance tamkar jariri ne, wato bai san komi game da rayuwa ba. Shi kuwa jariri ai mun san ba kawai rashin sanin abin da ya wakana ba ne ya dame shi, a’a, jikinsa da kwakwalwarsa da yanayin ginuwarsa duk suna da nakasu. Ke nan bai da wani amfani a irin wannan rayuwa.
Idan haka ne, kuma hakan ne, me ke nan za mu ce mun karu da shi a lokacin da muke bikin cika shekara daya da zaben shugaban kasa da aka yi a watan Afrilun shekarar 2011 a wannan makon? Wadanne darussa muka karu da su daga abin da ya faru cikin wannan shekara guda mai dimbin tarihi? Shin tarihin da muka baro a baya ya kasance mai dadin ji ne ko gani? Shin akwai ma tarihin da za mu iya tsinkaya a cikin wannan shekara guda? Ko kuwa dai abin nan ne da masana ke nuni, ga tarihin ya auku amma mun kasa fahimta saboda tulin jahilci.
Abin da zan yi a wannan karon bai wuce kokarin komawa baya ba domin na ga irin rawar da muka taka ko kuma in mun karu da wani abu na a-zo-a-agani! Haka kuma da kokarin ganin ko za mu iya dorawa daga inda muka baro. Domin kuwa amfanin tarihi shi ne kada a bari ya maimaita kansa, duk kuwa da masana na nuni da cewa da ma can bai maimaita kan nasa. A nan ina magana ne ko za mu iya hasashen gaba daga abin da jiya ta haifar mana a yau.
Mu soma da hayaniyar da ta biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan Afrilun 2011 din. Shin kashe-kashe da tashin hankali da ya faru me ya koyar da mu? Ba wani abu da ni na fahimta da ya wuce talakawan kasar nan har yanzu ba su gama wayewa ba. Duk da irin hayaniyar da aka yi da tashin-tashinar da ta biyo baya ganin wai an hana mutane zaben wadanda suke bukata, har yau ba ta sauya zane ba, domin kuwa ko bayan badakalar Jega ta 2011, har yau ana nan inda ake. An sake gudanar da zabubbuka a wasu jihohi, kuma tamkar jiya i yau! Shin talakawan sun sami damar barje guminsu? Ko alama! Abin da ya faru a jihohi biyar da aka sake gwabzawa a fagen zabe ya ishe mu misali? Nan ma din ba a bar talaka ya sake zabar wadanda yake so ba ne? Na yi wannan tambayar ne domin kuwa da alama akwai muna-muna dangane da kowane irin zabe a kasar nan, ciki kuwa har da hadin bakin talakawan da ke kukan ba a ba su dama suka zabi wadanda suke so ba. Me ya faru a Sokoto da Adamawa da Kogi? Shin mun koyi wani abu daga tarihin abin da ya wakana a zaben 2011 daga wannan zabe da aka yi a wadannan jihohi? Da alama ba mu koyi komi ba, ko kuma ba mu damu da mu koyi komi ko kuma mun koya mun dai kasa aiki da abin da muka koya. Bai yiwuwa a ce an yi kashe-kashe da raunatu mutane bilahaddin da lalata dukiyoyin jama’a saboda ba a son abin da ya faru bayan zabe, sa’annan a ce ‘yan watanni kadan angulu ta koma gidanta na tsamiya. Akwai dai wani abu da kila har yanzu ba mu kai ga gane shi ba. Idan kuma wannan bai ishe mu misali ba, to me za mu ce game da zaben da Jega ya gudanar a jihar Kebbi? Shi kuma wane tarihin ne ya koya mana na irin wannan badakalar? Shin da gaske ne mutanen jihar Kebbi sun sake yi zabe bayan wanda aka gudanar a shekarar 2011? Ina jam’iyyar CPC a jihar Kebbi? Ina dan takararta da ya fadi zabe ya tafi kotu, kotun ta ce a sake zabe? Ina ya shiga, me wannan ya koya mana? Shin ba a sake zaben ba? Wane darasi ke nan muka karu da shi daga zaben 2011 da ya sa muka yi wannan juyin-juya- hali a jihar Kebbi da aka je har kotun koli, aka rushe zabe, amma jam’iyyar da ta yi nasara ta bar wa wanda ta kada a kotu fili domin ya wataya? Wane irin tarihi ne wannan?
Ba wannan kadai ba, shin tun da aka kammala zaben shekarar 2011 zuwa yau wane irin ci gaba muka samu? Shin gwamnatocin da muka ‘zaba’ wane irin ci gaba suka kawo mana? Idan babu to wane darasi ko tarihi muka tsinkaya? Shin alkawurra nawa gwamnatocin nan suka yi mana kafin da bayan zabe, shin nawa suka cika? Idan ba su cika ko daya ba to me muka koya daga wannan tarihi?
Shin zaben 2011 ya canza mana rayuwa ko yaya take a yanzu? Shin ina wadanda suka rasa gidajensu suke zaman gudun hijira saboda aukuwar wancan zabe? Suna nan a sassanin gudun hijira, shekara guda da yin wancan zabe? Ina darasi a nan? Shin tallafin albarkatun man fetur da aka janye ya kare mu da wani abu? Shin zaben nan ya kawar da tashin-tashina irin ta Boko Haram da fashi da makami da kashe-kashen addini da kabilanci da makamantansu? Idan duk tsawon shekarar nan ba ta canza zane ba, me ya sa? Wane tarihi muka hango game da haka? Anya kuwa muna karuwa da wani abu ko dai dodorido ne makomarmu da makomar kasarmu?
Wani zai iya cewa ai cikin shekara guda da zaben 2011 kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. To sai me? Wane darasi muka karu da shi daga abin da ya faru? Wannan shi ne abin tambaya!
Saboda haka ni dai abin da na hanga na hango a cikin tsawon shekarar nan guda tun da aka yi zaben 2011 shi ne ‘yan siyasar da muke da su, ba su canza hali ba, kuma da alama ba su da niyyar canzawa, domin ba canji suke neman su yi ba. Canjin da kawai za mu gani ko nan gaba shi ne na motoci da tufafin da suke shiga da sanyawa da kuma maka-makan gidajen da suke ginawa. Tattalin arzikin kasar nan bai ci gaba ba kuma da alama ba zai ci gaban ba, domin kuwa ba wani tubalin gini da aka aza shi bisa, in ma akwai to tubalin toka ne. Haka kuma rayuwar talaka ba za ta canza ba, domin ba a yi wata shimfida da za ta taimaka ta canza ba tun azal. Ke nan talauci da yunwa da fatara da jahilci da komadaddar rayuwar da muka baro cikin wancan tsohuwar shekarar su ne za mu ci gaba da kai da kawo da su shekara mai zuwa, idan ba mun tashi mun yi wa kanmu maganin matsalar ba. Menene maganin matsalar? Ina jin ba sai na bada amsa ba! Allah ya nuna mana shekara mai zuwa mu ga ko mun nazarci wani abu ba wai daga tarihin ba, hatta daga wannan rubutun!
Daga Dr. Ibrahim Malunfashi, marubuci akan al'amuran da suka shafi rayuwar yau da kullum, musamman game da kasarmu Nijeriya.
Wednesday, April 25, 2012
Asalin Maguzawa
Babu wani takamaiman bayani a kan asalin kalmar ‘Maguzawa’, wato babu wanda zai ce ga daga inda ta samu, sai dai akwai bayanai na tarihi a kan Maguzawa. Ko da yake Maguzawa a yau suna nufin Hausawa wadanda ba Musulmi ba, wato wadanda suke bin addinin gargajiya.
A Kano wadansu masana suna ganin cewa Maguzawa kabila ne daga cikin kabilun da suka hadu suka yi Kanawa, suna ganin Maguzawa suna daga cikin birbishin jikokin Barbushe wadanda suka bai wa tsafin Tsumburbura gaskiya sosai. Su ne kuma suka ki karbar Musulunci a farkon lokaci, don haka duk Bahaushen da bai musulunta ba ake ce masa Bamaguje.
Ko ma dai yaya labarin yake, akwai Hausawa da suka ki karbar Musulunci a cikin birane, kuma hakan ya sa suka yi nesa da birane zuwa cikin dazuzzuka domin kubutar da tsohon addininsu da sauran al’adunsu na iyaye da kakanni. Haka kuma akwai wasu tarin Hausawa da suke cikin qauyuka wadanda sakon bai ma je musu ba, don haka suka ci gaba da addininsu na gargajiya.
Wadannan mutane a yau su ne ake kira Maguzawa. A iya cewa akwai bambanci tsakanin Arna da Maguzawa duk da cewa Sarkin Arna shi ne mai kula da tsafi tun kafin Musulunci a tsarin addinin gargajiyar Hausawa.
Kalmar arna an fi amfani da ita a yau a kan wadanda ba Musulmi ba sannan ba kuma Hausawa ba. Ba a cewa Arnan wata kabila Maguzawa, sai dai Arnan Hausawa kawai. Don haka a iya fahimtar cewa kalmar Maguzawa a Hausa tana da alaka da kabila ne, ba kawai suna ba ne na masu bin addinin gargajiya. A cikin tarihin Gobirawa sun ce masarautun kasar Hausa da suka sallamawa Sarkin Alkalawa (Gobir) su ne Adar da Yawuri da Mazamfara da Zazzau da Katsina.
Wadanda suka ki kuma su ne Kano da Daura da Rano da Hadeja. Sai sauran Hausawan da suke tare da Alkalawa suka kira wadanda suka ki bin su Maguzawa, wato Kano da Daura da Rano da Hadeja su ne Maguzawa. Wannan kuma shi ne asalin Maguzawa. Wannan kalma ta Maguzawa irin ta ce Turawan Ingilishi suke amfani da ita wajan bayyana waxanda ba Kiristoci ba, wato Pagan.
Ita wannan kalma sun are ta ne daga harshen Latin, wanda shi ne harshen daular Rome. Sarkin Rome Costantine shi ne farkon wanda ya karbi addinin Kiristanci, ya yi umarni da sauran mutane su karbi wannan addini. Kowa ya karba sai mutanan Pagus, don haka duk wanda ba Kirista ba ne, ake ce masa Pagus ko da ba daga yankin Pagus yake ba.
Wannan ya yi kama da dalilin da wasu suke cewa Maguzawa kabila ne daga kabilun Hausawa.
Shahararren marubucin Hausan ne Ado Ahmad Gidan Dabino ya rubuta wannan makala a shafin wannan dandali dake shafin sada zumunta na Facebook, Allah ya karawa Malam basira amin.

Monday, April 16, 2012
Ngozi Ikonjo-Iweala Ta sha Kaye A Zaben Shugabancin Bankin Duniya
Babban bankin duniya ya zabi dan Amurka Jim Yong Kim a matsayin sabon shugaban bankin inda ya doke ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo- Iweala.
A karon farko a tarihi, an kalubalantar mamayar da Amurka ta yi wa bankin na duniya - inda kawunan masu zaben ya rabu. Mr Kim ya samu goyon bayan kasashen Turai da Japan da Canada da kuma wasu kasashe masu tasowa kamarsu Rasha da Mexico da Koriya ta Kudu.
Kim wanda shi ne shugaban Dartmouth College, zai fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli.
A ranar Juma'a ne dan kasar Colombia Jose Antonio Ocampo ya janye daga takarar yana mai cewa "siyasa ce kawai a cikin lamarin".
Dr Kim zai maye gurbin Robert Zoellick, wanda ya jagoranci bankin tun shekara ta 2007.
Turai ta goyi bayan Amurka A tarihi dai, Amurka ce ke jagorantar bankin tun lokacin da aka kafa shi a shekara ta 1944.
Yayin da jagorancin Hukumar bayar da Lamuni ta duniya kuma, ke fadawa hannun Turawa. Sai dai ana samun karin matsin lamba domin ganin an bude kofar neman shugabancin hukumomin biyu ga kasashe masu tasowa.
Masu sharhi kan al'amura musamman a kasashe masu tasowa na ganin Ngozi ce ta fi cancanta da mukamin, ganin cewa ta shafe shekara-da-shekaru tana aiki a bankin.
Kasashen Turai da Japan na da kashi 54 cikin dari na kuri'u a zaben shugabancin bankin na duniya.
Sabon shugaban bankin zai jagoranci kwararrun ma'aikata masana tattalin arziki da kuma ci gaban kasa 9,000, da kuma ikon bayar da bashin da ya kai dala biliyan 258 - kamar yadda ya bayar a bara.
Daga BBC Hausa

Saturday, April 14, 2012
Har Yanzu Talakawan Nijeriya Ba Su Gaji Da Zaben Gen. Muhammad Buhari ba
Tun bayan maganar da Janar Muhammad Buhari ya fada a lokacin da wasu magoya bayansa suka kai masa ziyara a gidansa dake Kaduna wadda ya bayyana cewa "Zai kasance a harkokin siyasa har sai lokacin da abubuwa suka daidaitu, sannan talakawan Nijeriya suka fara cikin ribar demokradiyya a kowane mataki na gwamnati"
Wannan magana da Janar Buhari ya yi ta zama kamar wata allura ya zikarawa talakawan kasar nan, ba don komai ba sai don a tunanin talakawan wannan maganar da Buhari ya yi na nufin zai sake tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2015 kenan. A cewa wasu da dama sun bayyana cewa tun da Janar ya yi wannan magana to zai sake yin takara kenan, saboda har yanzu babu wanda zai iya daidai al'amuran kasar nan har talaka ya fara cin ribar dimokradiyya idan ba Baba Buharin ba.
Wasu kuma goyon bayansu suka nuna ga Janar Buhari tun kafin ya bayyana da bakinsa cewa zai tsaya takarar a 2015, inda za kaji suna fadin "Za mu ci gaba da dangwalawa Buhari kuri'armu koda za'a ci gaba da murde mana" wani bangaren kuma na fadin "Idan Buhari zai tsaya takarar sau 1000 ana murde masa ba zamu taba gajiya ba, za mu zabe shi sau 1000" da dai sauran maganganu na nuna kwarin gwiwa da rashin gajiyawa a wurin magoya bayan Buharin.
Idan ba'a manta ba Buhari a lokacin yakin neman zabensa a 2011, ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba, idan kuma yayi nasara to shekaru hudu kadai kawai zaiyi, ba don komai ba saboda yawan shekaru, wanda shekarunsa za su kasance 72 a shekarar 2015.
An nakalto daga Dandali Bashir Ahmad Facebook http://bit.ly/dandali

Tambayoyi Game Da Sabuwar Jaridar RARIYA
Bayan rubutun dana yi a kwanakin baya game da sabuwar jaridarmu ta RARIYA wadda ake yiwa lakabi da "Matatar Gaskiya" na samu sakonni masu tarun yawa, wasu na nuna fatan alheri ga wannan jaridar ta mu, wasu kuma tambayoyi suka yi game da wasu abubuwa daya shige musu duhu game da jaridar. Duk da mafi yawanci na bada amsoshin tambayoyin ga wadanda suka yi tambayar, to amma akwai bukatar nayi karin bayani akan tambayoyin saboda wadanda irin wadannan tambayoyi ke yi musu zirga - zirga a cikin zuciyoyinsu.
GA TAMBAYOYIN KAMAR HAKA:-
TAMBAYA: Shin yaushe RARIYA ke fitowa? Jaridar RARIYA na fitowa ne duk sati biyu a ranar Juma'a, amma kwanan nan RARIYA za ta fara fitowa duk sati. Da yardar Allah kafin karshen wannan shekara RARIYA za ta fara fitowa a kullum, wanda hakan zai zama wani abin tarihi ga jaridun Hausa. (A tarihi babu wata jaridar Hausa da ta taba fitowa a kowace rana).
TAMBAYA: Shin jaridar RARIYA na da shafi a yanar gizo? A halin yanzu RARIYA ba ta da shafi a duniyar internet, amma nan bada dadewa ba RARIYA za ta fara gudanar da harkokinta a shafinta na yanar gizo kamar sauran takwarorinta.
TAMBAYA: Shin akwai dandalin jaridar RARIYA a shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter? Eh kwarai kuwa RARIYA na da dandali a wadannan shafuka, wanda za'a iya samun na Facebook kai tsaye idan aka bincika sunan "RARIYA" a akwatin bincike (Search box) sai kuma a shafin Twitter akan @rariyajarida
TAMBAYA: Shin wanene editan RARIYA? Ashafa Murnai Barkiya shi ne editan RARIYA, saboda kwarewarsa da sanayyarsa, babu bukatar karin bayani akansa.
TAMBAYA: Shin a ina zamu iya samun RARIYA a jihar Sokoto, Lagos, Bauchi, Katsina dss.? Za a iya samun RARIYA a dukkan wuraren sai da jaridu dake fadin tarayyar kasar nan.
A karshe za a iya tuntubar wannan lamba 08034269830 domin samun cikakken bayani ga dukkan wani abu daya shafi jaridar RARIYA ko kuma aika sako kai tsaye ta wannan email: rariyajarida@yahoo.com ko kuma a ziyarci ofishin jaridar kai tsaye.

Monday, April 2, 2012
Shin Gaskiya Ne Nasir El-Rufai Ya Fara Yakin Neman Zaben Shugabancin Kasa Na 2015?
A jiya 02/04/2012 jaridar Sunday Trust ta kamfanin Daily Trust ta wallafa rahoton cewa Malam Nasir El-Rufai tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja, ya fara yakin sunkuru a fafutukarsa ta neman samun damar darewa shugabancin kasar nan a shekarar 2015 a karkashin jam'iyyarsa ta CPC mai alamar ALKALAMI.
Wannan rahoto na Sunday Trust ya ja hankalin mutane masu yawan gaske, wanda hakan ya haifar da tattaunawa mai zafi a shafukan internet. Wani bangare daga cikin mutanen na nuna goyan bayansu, wani bangaren kuma na nuna rashin goyan bayansu, wasu kuma na addu'ar Allah ya kawowa kasarmu Nijeriya mafita.
Wannan dalili ya sa na dauki wayata domin kuwa ina da lambar wanda ake tattaunawar akansa wato Malam Nasir El-Rufai, kuma cikin ikon Allah yana daya daga cikin manyan mutanen da duk da karancin shekaruna suna bani damar tattauna abubuwa da su, masu amfani musamman game da ci gaban al'ummar kasar nan.
Na kira Malam da misalin 11:30 na daren jiyan domin na tabbatar da gaskiyar rahoton Sunday Trust daga bakinsa, saboda bada kwakkwaran amsa ga mutanen da suka tambaye ni gaskiya labarin.
Bayan mun gama gaisawa da Malam, kai tsaye na shiga abinda ya sa na kira Malam wato tambayar "Shin menene gaskiyar labarin da jaridar Sunday Trust ta wallafa a yau dangane da maganar fara yakin neman zabenka a matsayin shugaban kasa a 2015?" sai Malam ya bani amsa da cewa "Kamar yadda nake fada a koda yaushe bani da burin yin kowace irin takara a 2015, saboda haka ba ni na bada umarnin a fara yi min yakin neman zabe ba, babban burina a yanzu shi ne na ga jam'iyyar CPC ta samu nasara, amma duk da haka ina godiya ga masoyana"
Bayan amsar tambayata da na samu a wurin Malam, sai na sake jefa masa wata tambayar wadda ta dade a raina "Shin Malam ya maganar kwamitin sake yiwa jam'iyyar CPC garanbawul wanda kake shugabanta?" nan ma dai Malam ya bani gamsasshiyar amsa ba tare da nuna gajiyawa ba, kamar haka "Wannan kwamiti yana nan yana aiki ba dare ba rana, musamman a yankunan da CPC ba tayi karfi ba, sannan kwanan nan ku ma irin ku matasa za ku shigo tafiyar wannan kwamiti domin samun nasarar abubuwan da aka sa a gaba.
Daga nan muka yi Sallama da Malam, na yanke layin wayata.
A karshe kamar yadda Malam Nasir El-Rufai ya bayyana, ya kamata duk masu kudirin neman wata takara a 2015 musamman mabiya jam'iyyar CPC da su dakatar da wannan kudirin nasu, su zo don bada gudunmawar gina jam'iyyar tukunna, wannan ne kadai zai kawowa jam'iyyar nasara a dukkan zabukan da zata tunkara nan gaba.
Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020
Subscribe to:
Posts (Atom)