Thursday, January 9, 2014

TALLA: Jama’a Ga Sabon Littafi


Bangon littafin Batulu

Marubucin shafin GADAR ZARE, a jaridar RARIYA  Dakta Auwalu Anwar, ya wallafa littafi mai suna Batulu, littafin na dauke da shafuka dari biyu da sittin da hudu (264), turkashi!

Cikin littafin, marubucin ya yi amfani da yanayin kulluwar dangantaka tsakanin malamai da dalibansu da kuma tsakanin su kan su daliban, a junan su, a jami’o’in Nijeriya a zamanin mulkin farar hula, a jamhuriyya ta biyu, wajen tsara labarin da aka bayar a cikin wannan littafi. Tasirin gwagwarmayar akidu da ra’ayoyi a tafiyar da kungiyoyin siyasar da ake da su a kasa, ga sarrafa tunanin al’uma, ya taimaka ainun wajen fassara irin fahimtar da dalibai suka yi wa matsayinsu a Jami’ar Goron Dutse, wanda a dalilin hakan ta kai suka dinga takun saka da hukumar makaranta, har a karshe aka yi mummunan boren dalibai a Jami’ar. Hukumar makarantar ta yi amfani da wannan tashin hankali don ta sallami wasu daga shugabannin kungiyar daliban da burin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Hayaniyar takaddama tsakanin dalibai da hukumar jami’ar ba ta hana samari da ’yammata sheke ayarsu tare da mike kafa don kafa tirken shagalin rayuwa a makarantar ba. Ta wannan fuska, an ci lagwadar soyayya an sha wahalarta, an riki alkawarinta an ci amanarta, sau barkatai.

A cikin irin wannan hali na rashin tabbas, aka samu wata daliba mai suna Batulu wadda ta gwanance wajen iya yakin sunkuru da yi wa maneman ta kiwon ragon layya.

Shin Batulu ta kasance sakaina mai iya ruwa don ta dau fansa ne, ko don ta karantar da duniya zurfin makircin mata? Akwai amsoshin wannan tambaya masu bambancin hujjoji a cikin wannan littafi wanda aka rada wa sunan yarinyar, don isuwar muhimmancinta da kasancewa jigon da aka gini labarin a kansa.

An soma shirye-shiryen tsara fim din wannan littafi. Maza ku mallaki naku da wuri, a kan naira dubu biyu da dari biyar (N2,500) mai bangon takarda, ko naira dubu hudu (N4,000) mai bangon kwali. 

Ana iya yin oda daga Kamfanin, ABU Press Limited Zaria, ko Kamfanin Rariya Media Services Ltd, masu buga jaridar RARIYA, a Lamba 53, Titin Mombolo, Wuse Zone 2, Abuja. 

Ana iya kira ko a yi tes ga wadannan lambobi don neman karin bayani: 08032493020, 0803 703 9914, 08065949711 ko a aika da imel ga: adnanwar@libe.com; abupress2005@yahoo.co.uk; abupress2013@gmail.com

No comments:

Post a Comment