Sir Ahmadu Bello Sardauna |
Alhaji Yusuf Tuggar, a makalar da
yake gabatarwa a duk sati a shafin BARANDAMI na jaridar RARIYA. A jaridar ta wannan mako, ya
yi wani rubutu da ya daga min hankali, marubucin ya dauko jawabin Firimiyan
Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna da ya gabatar a ranar 16 ga watan Maris na
shekarar 1964, wato shekaru 50 kenan. A lokacin Sardauna ya yi shekaru biyar
biyar yana mulkar jihar Arewa. Tuggar cikin gabatar da rubutun na sa ya nemi
masu karatu su kwatanta wannan jawabi da irin siradin da muke kai a yanzu
dangane da ci gaba ta fuskar yadda shugabanninmu suke mulkarmu a yanzu. Tabbas jawabin ya sosa min
zuciya, da ba don tarihi ba, da cewa zan yi tatsuniya ce ko kuma ba a Arewar
Nijeriya hakan ya faru ba.
Ba zan cika ku da surutu ba, ga
cikakken jawabin sai ku karanta watakila kuma ku ji abin da na ji a zuciyar ta wa, sannan daga karshe sai ku yi hukunci:
“Na fara da sunan Allah, mai jinkan talikai, mai musu rahama. Godiya ta tabatta a gare shi wanda ya rayar da mu har muka ga karshen wannan shekara.
Mun shiga shekara ta shida a cikin mulkin kan jihar Arewa da wani sabon tsarin mulki. Bara a cikin watan Oktoba Nijeriya ta zama Jamhuriya a cikin tarayyan nan ta ‘Common Wealth’ wannan ko shine matakala na karshe a cikin samowa wanan kasa cikakken iko da kuma ‘yanci na kanta.Yanzu duk duniya tana kallon Nijeriya a kan kasa wacce take tana da cikkaken iko na kanta, kuma bata dogara a kan ko wace kasa ba. A nan Nijeriya ta Arewa mun karpi kowane mataki na cigaban tsarin mulkin mu a cikin farin ciki da natsuwa wadanda suka cancanci zaman lafiyar Jihar nan da kuma fahimtar zaman duniyarta.
Ban da wannan muhimmin canjin tsari na mulki, ina farin ciki da gani cewa mun sami matukar cigaba ta fuskan tattalin arzikin jihar nan da kuma yaduwar ilmi. Ayyuka a kan abubuwan tsarin arzikin kasan nan na shekaru shida suna ci gaba sosai, haka kuma ake samu a wuraren sana’o’i wadanda ‘yan kasa da kuma mutanen waje suke kakkafawa. Na yi matukar farin ciki da sa harsashin ginin ma’aikatar yin siminti a Sokoto kwanan nan da kuma ganin ana kara samun ‘yan makaranta masu fita daga makarantu, tun ba ma masu fita daga makarantun Sakandire ba wadanda suke samun muhimman ayyuka a gwamnatin Jiha da ta tarayya ba, da ma’aikatar soja da ta ‘yan sanda, da kuma kamfanonin ciniki da sana’o’i. A watan Nuwamba da ya wuce ne na sumu darajar da aka nada ni shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, kuma a wanan ranar ce Jami’ar ta fara bada digiri.
To ko wane canji da cigaba su kan kawo sababbin wahaloli. Ko ya ya ina so in yi kokari in bayyana muku wadannan wahaloli ba tare da wata manufa ba, kuma ba tare da wani rufe-rufe ba tun da dai kowa ya san rufe-rufe ba hali na bane.
Nijeriya ta Arewa kasa ce wadda take da manoma, duk galibin arzikin kasar nan ya dogara ga noma ne. Amma abin takaici shine da yawa daga cikin samarinmu na wannan zamani sun dauka akan cewa idan suka sami ilmin zamani, sai su gudu daga wanna al’adatamu ta gargajiya mai daraja (wato noma), su koma su yi aiki a ofis ko a masana’anta. To, ina so in sanar da su cewa suna yin kuskure ne.Tilas ne su fahimta cewa ba abin kunya bane ko kadan in da ko wannenmu zai zama manomi. Ni ma kai na manomi ne. Kullum ina beken cewa dama ayyukana za su rangwanta min da na sami lokaci na yi noma a gonata ta Bakura. Kada ku dauka bata lokaci ne ku aika da ‘ya’yanku makarantu domin karo ilmi idan baza su sami aikin akawu ba bayan sun gama ilimin firamare. Kowane yaro da ya sami ilmi, zai zama ya karu da fahimtar abubuwan da duniya take ciki, zai kuma zama dan kasa mai amfani, wanda zai taimaka wajen kara arzikin kasarsa. Ina kara maimaita cewa arziki da ci gaban kasar nan ya dogara a kan irin himatuwar da manomanmu suka yi ne. Ku wadanda za ku bar makarantar firamare kwanan nan ina da wannan sako a gare ku. Ku zauna gida ku yi amfani da sabon ilmin da kuka samu ku zama manoman bana. Idan ku da abokanku ku ka bi shawarata kauyanku zai fi haka ci gaba, zai kuma zama wuri mai kyawun zama a cikinsa. Muna da shirye-shirye wadanda za su ba ku sha’awa, za ku ji su kwanan nan, wadanda kuma aka shirya musamman don a kafawa masu barin firamare guraren zama yadda za su koyi noma a kan hanyoyin zamani, cikin tsarin jam’iyoyin tsimi da tanadi, da kuma hanyar da za’a kara aikace-aikacen karuwar aikin gona.
Bara na tambayeku ku yi tunani a kan hanyar da za ku bi ku taimaka wajen kara cigaban kasarku ta hanyoyi masu sauki amma fa muhimmai, wato kamar yin ‘yan aikace-aikace wadanda za ku iya yi ta wajen hanyar gayya da gama kai. Na kuma tabbata kuna nan dai kuna tunani akan wannan roko da na yi muku. Ni kam ina nan ina tunani a kansa. Gwamnati tana nan tana ta tunani a kan yadda za’a yi a karfafa aikin gayya saboda jama’a su taimaki kansu da kansu. Wadansu daga cikin hanyoyin sune za’a shirya kyautoci iri- iri wadanda za’a rika bayarwa kowace shekara ga dukkan mutanen da suka fi kowa himmatuwa wajen gama gwuiwa su taimaki kansu da kansu. Don nuna shekara biyar da cikar samun mulkin kan wannan jihar, ina so in ba wa kowane daya daga cikin ku ko a ina yake wannan aiki. Ina so kowa da kowa a cikinku a wannan shekara ya shuka bishiya a gidansa ko a fili ko a gonarsa wanda a nan gaba za ta ba da itacen girki ko kuma ‘ya’yan itacen da za’a ci. Shekaru masu zuwa idan muka zauna a karkashin itacen bishiyoyin, za mu iya tunawa da hijira 1964 a kan hijira wadda mu da kanmu mun taimaka wajen tattalin arzikin kasarmu. Gwamnati ba za ta iya ba ku duk abin da ku ke bukata ba, ko kuma kuke so ku samu ba.Tilas ne ku shirya ku yi abubuwa da dama da kanku. Kuna da kasa wadda take da ‘yanci da zaman lafiya in da kowa daga cikinku zai ci riba idan ya yi amfani da gapopinsa da basirarsa. Cigaba abu ne wanda duk ya shafe mu baki daya , ba sai gwamnati ko En’e kawai ba. Saboda haka ku kudira niyya cewa wadannan bishiyoyi da za ku dasa su zama alama ce ta nuna sa niyya a kan cigaban kasar nan.
Bara gwamnatin tarayya da ta jihohi sun hadu sun kidaya duk mutanen kasar nan. Wannan aiki ne mai wuya da nauyi, to amma na yi farin ciki da cewa mutane a ko ina a jihar nan sun fahimci muhimmancin samun kyakkyawar kidayar mutane. Kuma sun amsa kiran gwamnati sun kuma hada kai da ita. Wannan ya rage nauyin aikin masu kidaya. Gwamnati na ta kara jin karfi saboda irin wannan hada kai da kuka nuna, kuma tana fata cewa a nan gaba duk sanda abubuwa muhimmai suka faru za ku nuna sha’awarku da dagewarku.
Na tuna da na yi muku magana bara a watan Maris, abubuwa mara sa dadi sun faru a kasar Afirka. Galibin abubuwa sun faru ne saboda son zuciya da kuma rashin dabarar wadansu mutane. Ina fata wadannan abubuwa ba za su faru a Nijeriya ta Arewa ba. To amma duk da haka ina so in yi wa duk shugaba wanda yake mulkin jama’a gargadi. Hanyoyin cigaba sun tunkaro da karfinsu, da yawa daga cikinsu za su yi hankoro su nemi ci da zuci. Tilas ne ku san yadda za ku yi ku zauna da su. Mutanen da aka dankawa jama’a a hannunsu, tilas ne su dauki duk nauyin aikinsu, su kuma gane bukatar canji, idan dai canjin nan shi zai jawowa jama’a alheri.
Tilas ne ku nuna cewa kun cancanci mukamin da ku ke da su, da yiwa jama’arku bauta, ko da shugaban kuwa Sarki ne ko Minister ko Hakimi ko Dagaci ko shugaban babbar makaranta ko malamin makarantar kauye, ko dan sanda ko ma’aikacin baitul mali ne. Tilas ne ku yi aikinku da gaskiya, da jure wahala cikin tsoron Allah da son kasarku. Da shugabanni da jama’arsu suna zaman cudeni-in-cudeka ne akan jawowa kasa cigaba. Tilas ne ka da mu yarda saboda sakewa mu kyale rashin kwanciyar hankali ya bata mana kasarmu. Tilas ne mu canzja tare da lokaci, kowane lokaci mu rika gyara halin zaman mu in da zai da ce da zamani, ba tare da mun yi wadansu ra’ayuyyuka ba wadanda ba su dace da halayar zaman kasarmu ba.
Ni bana shakka a zuciyata cewa cigaban kasarmu zai karu a kan hanya madaidaiciya, ko da yake a ko wane lokaci, tilas ne a sami mutane masu son kai da kuma dogon buri wadanda za su so su rudar da jama’a. Hakkin kowa daga cikinmu ne mu bi ta kan hanyar doka mu nuna musu kuskurensu. Mu yi kokari kowane lokaci mu rike halinmu na nagarta da fara’a mu kuma yi kokari mu gyara kowane rudani ne ya faru tsakaninmu, ta hanyar da abokai ya kamata su yi. Don saboda ko wane bambamci ne yake tsakaninmu, dukanmu mutanen gida daya ne, yayye da kanne, da abokai. Ina so daga wannan rana kowa daga cikinmu ya kuduri niyya, ya yi mutukar kokarinsa ya ga cewa kasar nan tamu tana ci gaba ta hanya madaidaiciya wadda ta haka ne kawai za mu sami biyan bukatunmu. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya sa mana albarka baki daya. Amin.”

Idan har kun zo nan a karatunku
ba tare da yin tsallake ko batan layi ba, tabbas na san kuma kun ji wani abu a
zuciyarku, ko da kuwa bai yi daidai da abin da na ji ba. Wannan babban kalubale ne a gare mu, mu ne jikokin su Sardauna, idan har aka ci gaba da tafiya a haka, zuwa lokacin jikokinmu kuma ya abin zai kasance? Allah ya kawo mana
dauki a Arewa da Nijeriya baki daya.
Allah saka da wannan bayanai masu matukar tausasa zuciya, Allah jikan su Ganji lallai sun bar mana babbar wasiya amma kash son zuciya da duniya sun dauke hankulan mu har mun manta asalinmu.
ReplyDelete