Saturday, May 30, 2015

MARTANI - ‘LEADERSHIP HAUSA: Tarihin Da Ba Ku Sani Ba’ Shawara Ga Ashafa Murnai Barkiya

Daga Al-Amin Ciroma

Idan za a iya tunawa, a ranar 15 ga Mayu, 2015 mun yi fitowar musamman don yin bikin Bugu na 450 wanda ya ja hankalin hankalin jama’a da dimbin masu karatu a ciki da wajen kasar nan. A lokacin ne muka nemi editocin baya, su dan tofa albarkacin bakinsu game da jaridar da yadda suke kallonta a yau.

Da kaina na aika musu da sako bai daya kamar haka: ‘Salam edita a fitowarmu ta wannan makon, za mu yi wani Special edition ne. Don haka, a matsayinka na daya daga editocinmu, ko za ka dan tofa albarkcin bakinka kan tambayoyi biyu kacal: (1) Me za ka ce game da Leadership Hausa? (2) Yaya kake ganinta a yau? (Pls also confirm to me the date u were employed and when u left.) Na gode, na ka, Ciroma.’

Ba tare da bata lokaci ba editan jaridar na farko, Malam Ibrahim Biu ya aiko da amsa, kamar yadda ya fito a bugun na musamman (15 ga Mayu), ya ce: “Tsakani da Allah jarida ta yi armashi ina alfahari da ita domin ta kawo karfin da ba Nijeriya kadai ba, duk inda mutum yake matukar zai kalle ta, hakika ya san a na yi wa Hausawa hidima. A Nijeriya kuwa LEADERSHIP HAUSA ta zama matashiya da manuniya saboda irin labaranta. 

“An wayi gari a yau akwai wasu mutanen da hankalinsu ba zai kwanta ba sai sun nemi jaridar a duk ranekun Jumma’a sun karanta, ba don komai ba sai kasancewar tana bayyana abubuwa da yawa da masu karatu suke son karantawa.

“Zan yi amfani da wannan damar na kara karfafa wa ma’aikata shashen na Hausa kwarin gwiwa kan su dage da hakuri don cimma babbar nasara nan gaba, musamman editanta a yanzu, ina mai ba shi shawara da ya ci gaba da hakuri da jajircewa har Allah Ya kara ninnika nasarori.”

“Na fara aiki a ranar 22 ga Satumbar 2006, na kuma yi murabus a ranar 9 ga Oktoba, 2006, inda a ka nada sabon edita.” In ji Malam Biu.

Shi ma edita na uku, Alhaji Salisu Alhassan Bichi a jerin editocin jaridar, ya kama aiki a ranar 24 ga Oktoba, 2011, ya kuma ajiye aiki ranar 30 ga Disambar 2011, ya ce: “Leadership Hausa ta kasance abu mafi inganci da ya taba faruwa ga makaranta harshen Hausa a wannan karni. Kasancewar masu sha’awar labarai da sharhi sun ta’allaka ne kacokan a sauraren rediyoyin kasashen ketare tun tsawon lokuta, sai ga shi a yau jaridar nan ta bayar da damar karanta duk iron labarai da sharhi akan kowane al’amari a dukkan fadin duniya.

“Har yanzu ba ta da na biyu kuma kullum kara daukaka take da shahara a tsakanin manyan mutane da talakawa. Da dama a kan aje kudi ne kafin ta iso don wanda suka saba da ita har da wasu fitattun gwamnoni da mutanen jami’a ba su yarda su rasa ta a kowace Jumma’a. Allah ya kara daukaka da basira.”

Amma ta bangaren edita na biyu Malam Ashafa Murnai Barkiya, al’amarin ba haka ya kasance ba. Farko sai da ya dauki lokaci mai tsawo bai aiko da tasa amsar ba. Daga bisani ya turo min cikakkiyar makala mai dauke da kimamin kalmomi 2689 (dubu biyu da dari shida da tamanin da tara). Ban samu lokacin karanta duka rubutun ba domin muna gaggawar kammala  aiki ne a lokacin da ya turo amsar, amma na dan tsakuro kadan din da zan iya amfani da shi, bisa alkawarin zan buga masa sauran nan gaba. 

Fitowar jaridar ‘Rariya,’ ta ranar 15 ga Mayu, 2015, ya dauki hankalina har na karanta rubutun baki daya, wanda na fahimci akwai matsalolin da zan iya jan hankalin Malam Murnai a kai, musamman don fahimtar juna.

A zatona tuni kan mage ya waye babu sauran hauma-hauma ba duhun kai, amma makalar tasa, wadda ya yi wa taken: ‘LEADERSHIP HAUSA: Tarihin Da Ba Ku Sani Ba,’ da ta fito a bangon jaridar ta ‘Rariya ’ ya tabbatar min har yanzu da sauran rina a kaba. A ganina ya kamata mutum ya yi amfani da kaifin alkalaminsa don wanzar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban al’umma maimakon haddasa rikici, gaba ko bayar da labaran kanzon kurege.

Shawarar farko da zan ba wa Malam Murnai wato editan ‘Rariya’ ita ce, ya rika amfani da hikima, ilmi gami da shimfidaddiyar zuciya a duk lokacin da kuduri aniyar aika sako ko mayar da martani. Ya kamata mutum ya mallaki kansa, ya rike akalar zuciyarsa kada ta yi tutsu da shi, domin bin son zuciya asara ce babba.

Misali, daga cikin abubuwan da suka ba ni mamaki shi ne inda ya ce: “Lokacin da Al-amin ya fara neman ma’aikata, ni ya zo har Kano ya samu, inda ya kira ni a waya na ce masa ina wurin walimar bikin Sulaiman Uba Gaya, mawallafin Jamhuriya a Murtala Mohammed Library. Ya je can ya same ni, ya ce min ya zo ne musamman domin ya ga Maje El-Hajeej Hotoro, kuma ya neme shi bai samu ba, an ce masa idan ya ga Ashafa to ya ga Maje. Na shaida wa Al-amin cewa to Maje kan kashe waya ya ma ya manta da ita ya shiga wani sagarabtu can daban. Don haka tunda kwana zai yi a Kano, ya kwantar da hankalinsa, da safe karfe goma zuwa sha daya na rana ya je LISS COMPUTERS kusa da Dangi Pharmacy inda muke aikin Jamhuriya, idan bai samu Maje a wurin ba, to Maje zai same shi a wurin.” 

Wannan maganar  ce ta fara jan hankalina har na fahimci akwai matsaloli a cikin rubutun na Ashafa, domin a tashin farko akwai coge a zancen. Abin da na san ya faru shi ne: Lokacin da Shugaban Kamfanin LEADERSHIP Mista Sam Nda-Isaiah ya bugo min waya, tambaya daya ya yi mani, ko na iya rubutu da Hausa? Na ce da shi ina dan kokartawa, ya ce ‘That’s good!’ Wannan ita ce ranar farko da na san yana da niyyar fara jaridar Hausa. Duk da na san Daily Trust na shirin fito da ta Hausa wato Aminiya. 

Kai tsaye Mista Sam ya umarce ni da in je in samu Akanta, ya ba ni kudi in tafi Kano, in nemi matashin da na san yana rubutun Hausa mu fara tunanin yadda za a kirkiro jaridar kafin ya dawo daga kasashen waje. 

Bisa wannan umarnin ne na kama hanyar Kano, amma kafin in tafi, mun dan tattauna maganar da mai dakina, kan wanda ya dace in nemo a Kanon. Da farko na kawo mutane hudu, Ado Ahmad Gidandabino, Sanusi Daneji, Bala Anas Babinlata, har da shi Ashafan. Amma a nata ra’ayin, ta ce idan har aikin jarida za mu yi, kada mu tsallake Maje el-Hajeej Hotoro. Ta dan fadi wasu abubuwan da ta sani game da shi, tun da ta zauna a Kano, kuma ta san wasu abubuwa game da adabi a lokacin. Babban abu ma ta nuna bisa yadda take kallon kowanne daga ciki, shakka babu Hotoro zai iya finsu hakuri da juriyar aiki. Wannan shi ne musabbabin neman lambar Maje daga wajen Ashafa, tun da ba mu taba haduwa ba.

Ko da na je Kano muka hadu da Murnai, na nemi ya ba ni lambar Maje, kafin ya bayar, ya rika yawo da hankalina, a dole sai ya san dalilin neman Maje a kaikai ce. Ko da na fahimci wayonsa na dage kan ya ba ni lambar kawai. A nan, duk wanda ya san Ashafa, zai iya bayar da shaida irin yanayinsa. Idan ka je neman abu a wajensa, kafin ya ba ka,  zai yi ta yawo da hankalinka tare da bin diddigin gano abin da kake nema tukunna. Na san da haka sosai, shi ya sa ban furta masa komai ba. Da ya ga dai na dage kawai ya zaro wayarsa daga aljihu ya ba ni lambar Maje, muka yi sallama, na kama gabana. 

Don haka, babu zancen mun yi zan kwana a Kano ko kuma Maje na kashe waya da sauransu.

Sannan a cikin rubutun har ila yau, daidai inda Murnai yake bayyana yada ya shigo kamfanin LEADERSHIP, nan ma ba haka aka yi ba, kuma a zatona edita zai yi adalci ya fadi hakikanin yadda ya samu aikin da ya kara haska shi a duniya. Amma watakila malamin yana bisa ingarmar dokin zuciyarsa ne, har ya kasa rikonsa da kyau, ya yi sake haniniya da yunkurin dokin suka ruda masa kwakwalwar da ya kasa damkewa yadda ya kamata. Ya bige da fadin: 

“Wshegari Al-amin ya kira ni muka yi maganar cewa don Allah na zo na yi aiki da Leadership Hausa. Na bayyana masa uziri na, na ce ina son aiki da ku wuri daya amma Sulaiman mai Jamhuriya fa? Al-amin ya ce na yi masa magana, na ce gaskiya ba zan iya ce masa wani abu ba, domin haushi zai ji. Muka shirya cewa shi Al-amin din ya kira Sulaiman, kuma haka aka yi, ya kira shi suka yi magana. 

Daga baya Sulaiman ya ce min shi wallahi babu komai, tunda ma jaridar tasa ta tsaya, kuma ana tare ai ba wani abu ba ne. Ya kira Al-amin ya ce masa ya amince. Sai ya ce shi tunda ya san Sam da dadewa, ya kira shi a waya ya ce masa ya ga jaridar da ya kafa ta Hausa, amma ya fahimci akwai matsaloli, wadanda shi idan ya na bukata, to yana da editan da zai rike masa jaridar sosai.”

Masu karatu, wannan ita ce maganar da ta fi sosa min rai, don kuwa ina ganin bai kamata Murnai ya yi saurin manta da irin halascin da ni kaina na yi masa ba. A tunanina lokaci bai yi ba da har Ashafa zai yi saurin manta wannan ba. Amma kuma ban yi mamaki ba domin na fada a farkon bayanina, muddin ka kasa mallakar kanka a yayin da kake kokarin isar da wani muhimmin sako, shakka babu, shaidan zai yi wasan kura da zuciyarka, daga bisani ka rasa alkibla. Bisa wannan dalilin ne muke ganin yadda manyan mutane, wadanda suka san kansu suke iya wasa da alkalumansu wajen yada alheri ba sharri ba, kuma su yi amfani da kaifin hankali, ilmi da basira wajen rubutu.

Kafin na nemi Ashafa, tabbas mun yi maganar nemo wani daga Kano da Maje el-Hajeej, har  ya kawo min zancensa. Na ce bai  kamata mu shiga hakkin Malam Ibrahim Sheme ba, saboda a lokacin ana buga jaridar Public Agenda a Kaduna sannan Murnai na daya daga cikin wakilan Sheme a Kano. Don haka a tunanina dauke Ashafa zai iya haifar da tasgaro ga jaridar tasu. Maje dai ya dage cewa babu wata matsala, don yana da tabbacin shi ma Ashafa zai so aikin.

Ba tare da bata lokaci ba na daga waya na kira shi. Bayan mun gaisa na tambaye shi ko zai iya aiki da mu a Abuja? Amsa mai sigar tambaya da ta fito daga bakin Murnai ita ce: ‘Wane mukami za a ba ni?’ Na yi dariya, na ce da shi, ‘Ashafa kenan! Kada ka manta na sanka da dadewa mutum ne mai son tsayuwa da kafafunsa, kana da kokari matuka kan aiki, don haka wannan wata dama ce da za ka iya amfani da ita domin cimma burinka a rayuwa. Ka zo Abuja mu hada kai mu yi aiki tare, mu taimaki juna don ci gabanmu baki daya.’ 

Ya ji dadin hakan sosai. Muka fara tunanin yadda za a dauke shi. A take wata dabara ta fado min. Dabarar kuwa ita ce mu nemi hanyar gabatar da shi a wajen Mista Sam, ta yadda ba zai fahimci ni ne da kaina na kawo shi ba.

Muka yi ta shawarar wanda zai yi mana wannan, a take a lokacin tunanin Malam Badamasi Burji ya fado min, amma Murnai ya ce a manta da zancen Badamasi. Ya kara da cewa akwai wani aminin Chairman dinmu, Alhaji Suleman Uba Gaya, shi ya fi dacewa ya yi hakan. Ya turo min lambarsa na kira shi. Bayan na kira Malam Suleiman muka yi magana, ya fahimci komai. Ya ce ba matsala zai nemi Sam.

Mun yi haka da ‘yan mintuna kwatsam, sai Mista Sam ya bugo min: “Ka san wani Ashafa daga Kano?” Wannan ita ce tambayarsa. Na shaida masa hakika Murnai haziki ne a fagen rubutun Hausa. Ban manta kalmar ma da na yi amfani da ita ba cewar: ‘Ranka ya dade Ashafa IS A GENIUS!’ abin da na fada wa Sam ke nan. Jin haka ya ce bari ya gayyato shi gobe-goben nan. 

Yana shigowa Abuja kuwa da kaina na dauko shi a daidai kasuwar Garki zuwa ofishinmu. Har na yi masa barkwanci na ce, ‘Malam Welcome to Abuja!’ aka dai yi dariya. Wannan shi ne hakikanin abin da na sani game da samun aikinsa a LEADERSHIP. Malam Suleman Uba Gaya yana nan a raye, Maje el-Hajeej shi ma haka bai kamata Murnai ya dakile wannan ba, ko da rai ya baci.

Haka kuma a rubutun nasa har wa yau, Murnai ya nuna wa duniya a ofis yake kwana. Kwarai an yi hakan, amma na dauka zai fadawa mutane nawa aka ba shi ya kama gida, hakan zai ba jama’a damar kimanta darajarsu a shekarar 2007. 

Koma dai me? Ina ba wa Murnai shawara nan gaba ya guji irin wadannan maganganun, idan ma zai yi, yana da kyau ya sa hikima, ilmi da basira a ciki. 

Na tabbatar malamina Barkiya ya san dalilin da har ya sa aka dakatar da biyan kudin gidansa. Idan ya manta ba abin mamaki ba ne domin shi mutum mai saurin mantuwa! 

Amma ba ya rasa nasaba da yadda ya ki amfani da kudin don kama gida, maimakon hakan, ya rika kwana a ofis, a zatonsa ba a gane ba. Duk da an gane din, sai da aka kara ba shi kudin gida a karo na biyu, amma gafarta malam bai daina kwana a ofis ba. Idan kai ne, za ka ci gaba da biyan kudin? Da fatan editana ya tuna da wannan, kuma zai kiyaye nan gaba.

A cikin rubutun Murnai ya kara cewa: “Babun irin wahalar da ban ci ba a wajen fito da LEADERSHIP HAUSA kowace Juma’a. An sha gama aiki za a tafi buga jaridar kudin colour separation ya kakare, sai dai na dauka a aljihu na na bayar a je a yi, don kada safiya ta yi ba a buga jaridar ba.”

Ya salam! Da na karanta wannan sadarar sai da na kusa faduwa saboda dariya. Da me wannan zancen ya yi kama? Ashe Malam Murnai yana da hannun-jari a kamfanin LEADERSHIP ba mu sani ba? Duk da yanzu nake koyon aikin jarida, amma na kan ji ana fadin ayyukan edita. An ce babban aikin da ya rataya kan edita shi ne duba jarida, tabbatar da kammalar shafuka, bayar da umarnin bin diddigin tsaftace labarai da rahotanni, da dukkan shafukan jarida. Uwa uba, tantance manufar jarida don gudun haddasa husuma ko tashin hankali a cikin al’umma gami da wayar da kan jama’a bisa abubuwan da ke faruwa.

Idan har ban yi kuskure ba, ashe kenan babu abin da ya hada edita da harkar dab’i wato buga jarida. Ke nan a yayin da edita ya yi wannan, ya gama aikinsa. Daga nan jami’in dab’i yake dorawa. Zai tabbatar da fitar jarida a tsarin da ake sayarwa a kasuwa.

Idan har haka ne, mene ne matsayin Murnai a LEADERSHIP HAUSA? Jami’in dab’i, mawallafi ko edita? Na dauka Murnai zai fito ya fadi dalilin biyan kudi daga aljihunsa da ya ce yana yi, don a gaggauta fito da jaridar. A ganina, ba wanda zai ba wa edita laifi idan aka kasa buga ta. Wannan ke nan.

Yana da muhimmanci mu tunawa Murnai cewa kowane kamfani yana da tsarin fitar kudi daga wajen akanta. Me ya sa ba zai hakura har sai lokacin da kudin suka fito daga can ba? Ko su kansu masu kamfanin ba su san da aikin jaridar ba? Sannan tun daga aka fara LEADERSHIP, akwai ranar da aka ce saboda babu kudi, jarida ta makale ta kasa fitowa? Ko ya taba jin LEADERSHIP HAUSA ta tafi hutu, ko ta yi nukusanin fitowa?

Ba mu sani ba ko dai malam yana da wata ‘yar yarjejeniya da ya kulla da wasu...? Ko kuma sun ba wa yaransa na goro, wanda idan jaridar ba ta fito a daidai lokacin da ya kamata, za su iya tilasta wa malam ko yaran malam su amayar da dan hasafin da suka yi wa hadiyar Kafino? Allah-gafarta malam ya girmi wannan, kuma bai dace ya rika yayata hakan ga duniya ba.

Tun da aka ba ni wannan kujerar, da zarar na kammala aikin jarida na rattaba hannu kan shafuka, wallahi ba na waige. Zan kama hanya sai gida. Idan ta jarida ba ta fito ba, babu wanda zai tambaye ni dalili don ba aikina ba ne.

A gaba, Murnai ya kara cewa: “Aka rika kawo motoci birjik ana bai wa editoci da sauran manyan ma’aikata, sai da aka shafe sama da shekaru biyu ana raba motoci, amma ni sai dai kallo, sai alkawarin idan an kara kawowa za a ba ni. Farkon lokacin da aka fara kawowa, da aka bai wa editoci sabbin motoci garau daga kamfani, ni sai aka hada ni da wata akwalar Honda Cibic. Kullum ta lalace a hanya, ko ta ki tashi ko ta cakire. Kafin na fara hawanta ma sai da na sai mata sabbin tayoyi. 

“Bayan na yi hadari da ita ne, aka ba ni hakuri, aka ce za a ba ni sabuwa, amma hakan ba ta yiwuba, har sai da haushi ya sa na rubuta takardar barin aiki, inda a cikin dalilai na har da rashin dauka ta da daraja, ga rashin ba ni kudin kama haya, ga kuma rashin ba ni mota, wai sai ake ce min na hakura sati mai zuwa za a ba ni sabuwa rangadau.”

Allah sarki! Ban so a ce Murnai ya fadi wannan ba, domin malam ne ya jaza wa kansa matsalar ba kamfani ba. Tabbas an yi rabon motoci, amma kamar yadda na fada a baya, kowane kamfani yana da tsarin gudanar da ayyukansa. Ina son edita ya kara tuna cewa ko a cikin editocin ma akwai wadanda suka riga shi fara aiki, amma kafin a zo kansa, akwai wata tsohuwar motar da aka nuna masa. Aka tambaye shi ko yana bukatar mallakarta, ko kuma zai jira a kawo wasu sabbi? 

Da ya shawarci mutane, na tabbata wani zai ce kada ya karbi tsohuwar, za a iya ba shi shawarar ya bari har sai an kawo wasu sabbi ya karba. Amma na fahimci a lokacin kowa so yake a ce yana da mota. Watakila dalilin da ya sa Malam ya karbi tsohuwar akwalar kenan.

Har bayan da ya yi gaggawar karbar motar, Murnai ya ji dadinta kwarai domin ko ba komai a kanta ya koyi tuki. Sai dai, kamar yadda na fadi a baya, bai kamata edita yana irin wannan zancen a kafa kamar wannan ba. Ko da zai yi, da sai ya yi magana cikin falsafa da ilmi. Amma aikin gama ya gama, malam ya tallata kansa a duniya, kuma bai fadawa mutane dalilin rashin ba shi sabuwar mota ba. Watakiala masu kamfani sun lura bai riga ya kware a tuki ba, kullum fadawa yake cikin hatsari daban-daban, me zai sa su dauki dankareriyar mota su bayar?

Mu ma ture duk ma wannan a gefe, don ba a ba ka mota ba har sai ka tayar hankali? Bai dace Gafarta Malam yana irin wadannan maganganun ba. Yaya yake son mu na baya mu yi?

Zan takaita a nan domin ba na son tsawaitawa, amma ina ba Malam Ashafa shawara da ya rika tauna zance kafin ya fade ta, hakan shi ne jarunta ba kawai abin da ya zo zuci ba.

Ban damu da yadda har ya kammala rubutunsa bai fadi wani abu daya da ya gani na ci gaba a LEADERSHIP HAUSA a yau ba. Duk kuwa da sanin cewa a yanzu duk kamfanin nan, babu jaridar da ta fi ta mu ta Hausa kasuwa. Sabanin a zamaninsa da bai fi a sayar kwafe dubu biyu zuwa uku ba. Ya kamata malam ya zo ya tambaya a yau kwafe nawa ake bugawa? Kuma nawa ake sayarwa? Sauran editocin da suka gabata (wato Malam Ibrahim Biu da Salisu Alhassan Bichi), sun yaba mana sun kuma ba mu shawarwari masu amfani.

Don haka ya dace editan Ashafa ya daina ci ga zuci, ya rika dora alkaminsa bisa ilmi da basira domin idan baki ya san na fade, bai san na mayarwa ba. Ban ji dadin yadda ya nuna hassadarsa karara ba, don kuwa har ya kammala ‘...Tarihin da ba ku sani ba,’ babu inda ya yaba da irin yadda jaridar take a yau, amma hakan ba ta hana shi bata lokacinsa wajen kwaikwayon LEADERSHIP HAUSA ba. Duk wanda ya kalli ‘Rariya’ da idanun basira, zai ga hakan. Na dauka Murnai zai yi wa jaridar tasa sabon zubi ne ta bambanta da sauran jaridu, kamar yadda kowa ke yi ba wai ya rika kwaikwayon wasu ba. Amma dai ko makaho ya shafa ya san ‘Ta Mu Ba Irin Ta Su Ba Ce!’ 

Shawara ta karshe da zan bayar a nan ita ce ya daina bata wa kansa lokaci wajen neman yardar mutane don a yaba masa, a wajen Allah ake neman yarda. Kalas! 

3 comments:

  1. Alhamdulillahi, na ji dadin wannan takaddama da ta kaure a tsakanin Ashafa da Al-Amin Ciroma. Domin na dade da sanin cewa rana irin wannan ta na kan hanyar zuwa. Ya na da kyau a yi amfani da ilimi da basira wajen yada alheri ba sharrii ba kamar yadda Al-Amin Ciroma ya ce. To sai dai ina so Al-Amin Ciroma ya sake komawa baya, ya dubi dukkan bayanan da ya yi na yadda ya dauki Ashafa zuwa kamfanin Leadership. Akwai wuraren da ya tsallake da yawa. Ni a nawa kundin tarihin da na ke rubutawa akwai inda muka zo daidai da shi, amma akwai inda ya yi tsallake. Na kuma san ba zai ce ya manta ba. Don haka Ciroma ya sake bi-baya ya gyara labarin, banda tsambare.

    ReplyDelete
  2. DANGOTE CEMENT FACTORY LOKOJA OBAJANA PLANT NIG PLC.WISH TO INFORM THE GENERAL PUBLIC OF SALES OF ITS CEMENT REDUCTION TO N1000 PER BAGS...CEMENT GRADE 50KG,THE MANAGEMENT NOW OFFER CEMENT AT LOW FACTORY PRICE @N1000 PER BAGS AND DELIVER TO ANYWHERE IN NIGERIA CONTACT DISTRIBUTOR MANAGER MR ABDU DANTATA FOR PURCHASE +2349038571819 OR +2348137579314."NOTE"PROMO ENDS BY 18th OF DECEMBER 2015?

    ReplyDelete