Kamar mafi yawan lokuta, yau ma karar kiran wayata ne ya tashe ni daga bacci, bayan na tashi na duba wayar na ga sabuwar lamba ce, da na amsa wayar sai na ji wata baiwar Allah ce daga Sokoto, bayan mun gaisa sai tace "Don Allah wai Dan Ibro ya rasu?, an fada min cewa ya mutu, amma ban yarda ba sai na ji daga wajen 'yan jarida". Kai tsaye na bata amsa da cewa "A'a". Ba tare da tunanin ya kamata na bincika gaskiyar labarin ba, dalilina anan shi ne kusan sau biyar kenan a sani na ana yada jita-jitar Ibro ya mutu, yayi hatsarin mota, amma daga baya sai Ibro ya fito ya karyata labarin.
"Ban mutu ba, amma idan lokacin amsa kira ya zo, zan tafi" wannan amsa ce daga bakin Ibro, a wani lokaci a baya da aka yada irin wannan jita-jitar cewa ya rasu.
Bayan mun kammala waya da Malama 'yar Sokoto, ban ajiye wayar ba, sai na shiga Facebook, har ga Allah ko a zuciyata ban shiga don tabbatar da labarin mutuwar Ibro ba, saboda a zuciya ina da yakinin cewa bai mutu ba, kawai abin da aka saba ne na yada jita-jita akan sa.
Rubutun da na fara cin karo da shi ne ya sanya bugun zuciyata tsayawa cak, rubutun edita na Al-Amin Ciroma (Editan Leadership Hausa) na gani, inda yake bayyana labarin rasuwar ta Ibro, wannan rubutun kadai ya tabbatar min lalle Ibro lokaci yayi (Allah ya jikansa). Ina yin kasa sai ga rubutun Ado Ahmad Gidan Dabino, Auwal Danlarabawa da wasu da dama duk suna nuna alhinin su da addu'ar Allah ya gafartawa Ibro.
Kafin na ankara sai naji idanuwana sun cika da kwalla, sai kuma hawaye ya biyu kumatu da daga baya. Ba komai ya sa zuciyata ta kara cikin kankanin lokaci ba, sai tsoron Allah da ya kara shiga jikina. Na kara tabbatar da cewa idan lokacin mutuwar mutum bai yi ba, ko duk mutanen duniya za su so ya mutu ba zai mutu ba, amma da zarar lokacin yayi to fa 'babu tsumi kuma babu dabara' kamar yadda mawaki Aminu Ala yake fada a cikin wata wakarsa.
Allah ya jikan Rabilu Musa Ibro, Allah ya gafarta masa, Allah ya bawa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Da ba don dan Adam akwai shi da saurin mantuwa ba, da zan iya cewa har abada ba za a iya mantawa da Rabilu 'Dan Ibro' ba.
No comments:
Post a Comment