Friday, February 21, 2014

Sharhin Littafin Batulu

Marubuci – Auwalu Anwar
Shekara – 2013
Sunan Littafi – BATULU
Madaba’a – ABU Press Ltd
Shafuka – 264
Mai Sharhi – Halima Musa

BATULU littafi ne da aka wallafa a shekara ta dubu biyu da goma sha uku. Marubucin littafin, Dr. Auwalu Anwar, ba bako ba ne ga duk wani makarancin rubuce-rubucen Hausa. Hasali ma, sanannen marubuci ne wanda ya wallafa kasidu da littattafai da wake-wake da dama. Haka shi malamin tarihi ne wanda ya koyar a jami’ar Maiduguri. Bugu da kari, wasu za su iya tuna shi a matsayin marubucin sharhin GADAR ZARE a jaridar Rariya.

An zayyana labarin BATULU a cikin shafuka dari biyu da sittin da hudu. An kuma kasafta shi babi-babi har ashirin da biyar, ta yadda kowane jigo ya kasance babi daya, da takensa, tare da jero su bibiye da juna yadda labarin ya dinga hauhawa, har karshe. Wannan ya bai wa mai karatu damar hangen abinda kowanne babi zai kunsa.

Littafin ya dace da matasa, ’yan jami’a, samari da ’yammata, har ma da masu burin zuwa jami’a. Saboda su babban jigon labarin ya fi shafa don ya zama ishara. Amma iyaye ma wannan littafi zai musu matukar amfani don su san abubuwan da ke wakana a kusurwoyin jami’o’in da ’ya’yansu ke karatu da kuma abin da ’ya’yansu ke aikatawa da hatsarin da za su iya abkawa ciki. Makarantan littafin baki daya, za su amfana ta hanyar fahimta da kuma kiyaye musabbabin faruwar wasu al’amura a jami’o’i.

Marubucin littafin ya yi amfani da salon zance mai sauki wajen gabatar da shi. Ya yi amfani da Karin Magana sau da dama wajen isar da sakon da ya ke muradin isarwa ta yadda duk wani mai jin Hausa zai iya karantawa ya fahimta. Saukaka salon rubutu da marubucin ya yi, ya kasance tamkar kwarin gwiwa ga mai karatu. Haka ya yi amfani da salon tattaunawa da zancen zuci, wanda ya kara kawata, ya kuma saukaka bin labarin ga mai karatu. Akwai ’yan wuraren da ya yi amfani da kalmomin Larabci (kamar wurin da ake maganar hubbul Nabiyi da hubbul nafsi da hubbul malu). Ko kadan hakan bai takaita saukin fahimtar littafin ba. Wani abin sha’awa ma, sai amfani da Larabcin ya kara kayatar da sakon da marubucin ke kokarin isarwa.

Duk wanda ya karanta BATULU zai yi mamakin yadda marubucin ya fede biri har wutsiya dangane da yanayin rayuwar dalibai a jami’a. Musamman badakalar soyayya tsakanin dalibai, tsakanin dalibai da malamai da kuma tsakanin dalibai da jama’ar gari. Abin mamakin a nan shi ne, yadda ya bayyana yaya fasikanci ke wakana karara tsakanin rukunin wadannan bayin Allah. Musamman tsakanin dalibai mata da malamansu, ta yadda ake shakuwa da cin amana da yaudara. Wannan hakika ya jaddada tunani da kuma muguwar fahimtar da mafiya yawan jama’a ke yi wa daliban jami’a mata. Yawanci ana yi musu kallon ’yan iska kuma watsattsu marasa mutunci da kunya. Hakan na iya kara tunzura masu ikirarin hana ’yayansu mata zuwa jami’a don tsoron kar su lalace, har sai sun yi aure. Wadanda suka dauki abin da zafi ma, wannan na iya sa su hana ’ya’yan nasu mata zuwa jami’ar dungurungun da zimmar kare mutuncinsu.

Hausawa sun ce duniya zaman marina ce. Watau kowa da inda ya sanya gabansa. Duk cikin hayaniya da badakalar soyayya, har ma da fasikancin da ake yi a jami’ar Goron Dutse, marubucin ya iya nuna cewa ba duka aka taru aka zama daya ba. Misali, marubucin ya gabatar da hazikan dalibai da ke dawowa da dakon littattafai daga wajen karatu da tsakar dare, daidai lokacin da ake dawo da wasu ’yan’uwansu dalibai daga dabdala da sharholiya cikin motoci na alfarma. Ya kuma iya zakulo da bayyana mutuntaka da da’a da tarbiyya ta gari, ta hanyar wasu taurari da suka kasance dalibai mata, masu kamun kai da nuna kyama ga halayen ashsha da takwarorinsu, suka dulmiya a ciki. Watakila kasancewar wasu daga cikin wadannan dalibai jinsin Fulbe, ya bankado dan abin da ba a rasa ba, na kyashi da kushe tsakanin kabilun Hausawa da na Fulani, sabanin gamayyar dole da ake yi wa kabilun biyu.

Idan manufar marubucin ya bayyana ruguntsumi da dambarwa da kwamacala da yaudara da munafunci da cin amana a soyayya ne, to lallai ya cim ma burinsa. Haka ya cim ma nasarar bayyana irin gumurzun da ke wakana tsakanin hukumomin jami’o’i da kungiyoyin dalibai, da kuma tsakanin malaman da hukumomin kasa. Kamar yadda abubuwa suka kasance a jami’ar Goron Dutse, tabbas haka suke a jami’o’i da dama a zahiri.

BATULU littafi ne da za a iya gabatarwa ga kowanne irin makaranci saboda akwai darussa masu yawa a cikinsa. Babban darasin shi ne, mutum ya yi takatsantsan a harkokin soyayya. Saboda mayaudara sun yawaita a duniya ba ma a jami’a kawai ba.

An yi amfani da taurari da dama wajen isar da sako a BATULU. Manyan taurarin dai su ne Amadu da Batulu. Duk dambarwar cikin littafin ta rayuwarsu ce. Sai kuma sauran kananan taurari da aka yi amfani da su wajen karin bayanai, wadanda suka kasance kawaye, ko abokanai ko kuma malamai ga masoyan, har ma da iyayen manyan taurarin.

Idan ana maganar jigo, akwai su da dama. Babban jigon dai su ne Yaudara da Munafunci. Marubucin da kansa a karshe ya tari numfashin mai karatu da ya canza wa Batulu suna zuwa “Butulu”.
Wanda kusan duk mai karatu zai yanke wannan hukunci tun kafin ma ya kai karshen littafin. Akwai kuma irin wannan yaudara da ta wakana tsakanin Batulu da Malam Bello. Wasu na iya ganin soyayya a matsayin babban jigon BATULU. Wannan za ta iya kasancewa. Saboda an dabaibaye labarin cikin harkokin soyayyar da ta kasance tun farko tsakanin Batulu da Salisu, ta kai kan Malam Bello, sai kuma Amadu, Sai Musa, ta kuma kare a kan Iliyasu. Akwai jigon siyasa da rarrabuwar akidar mutanen birnin Kano tsakanin masu bin akidar siyasar gurguzu da kuma ta jari hujja. Haka kuma ta kasance a siyasar jami’ar Goron Dutse, tsakanin malamai da kungiyoyin dalibai. BATULU kuma ya kunshi jigon rarrabuwar jama’ar garin Kano tsakanin ’yan boko da malaman addini da ’yan kasuwa (wadanda aka fi sani da ‘alhazan birni’), inda ya kyankyashi jayayya da gasa da ke tsakanin wadannan rabe-raben, ko gungu-gungun al’umma, wajen neman abin duniya.

Duk wadannan jigogin marubucin ya tubka su cikin labarin da ya bayar ta hanyar alakanta su da taurari daban-daban, kamar abokanai da kawaye da malamai da ma iyayen manyan taurarin littafin. Haka jigogin da suka shafi al’adu sanannu ne ba sababbi ba ga yanayin rayuwar garin Kano da ma na sauran al’umma baki daya.

Marubucin ya gabatar da zubi da tsarin BATULU daidai yadda ya dace da yanayin halayyar taurarin littafin da kuma yadda karshen labarin ya kasance. Ta yadda mai karatu zai kagara ya ga yadda za ta kaya, tare da jefo ba-zata a wasu lokutan. Ya kuma yi amfani da nau’o’in hatsari wajen kawar da wasu taurarin wadanda ci gaba da kasancewarsu, za ta haramta warware sarkakiyar cikin littafin. Misali, boren daliban jami’ar Goron Dutse ne ya kawar da Tanko daga labarin, kamar yadda faduwar Salisu jarrabawa ta kawar da shi daga labarin. Haka shiryeyyen tashin hankalin ashararai da ’yan iskar garin Kano ya kawar da Malam Bello daga labarin.

Shi dai Littafin BATULU an gabatar da shi ne a jami’ar Goron Dutse da ke garin Kano. Kusan duk manyan abubuwan da suka wakana a nan suka wakana, sai wanda ba a rasa ba. Wannan kamar wani sabon abu ne. Domin yawancin marubuta suna amfani da sunayen kirkira ne, ba sunayen gaske na garuruwan da aka sani ba. Hakan ta sa mai karatu ganin kamar yana cikin labarin, musamman idan a Kano ya ke zaune, ko ya san garin.

Saura da me? Sai masu karatu su nemi BATULU, don ganewa idanuwansu, kacokan, wainar da ake toyawa a jami’ar Goron Dutse ta Kanon Dabo birni.


Ana iya yin oda daga Kamfanin ABU Press Limited Zaria, ko Kamfanin Rariya Media Services Ltd, Lamba 53, Titin Mombolo, Wuse Zone 2, Abuja.

Don karin bayani za a iya kira ko a yi tes ga wadannan lambobi: 08032493020, 08037039914, 08065949711 ko a aika da imel ga: adnanwar@live.com; abupress2005@yahoo.co.uk; abupress2013@gmail.com

No comments:

Post a Comment