RARIYA – Wasikar Obasanjo Ga Jonathan: Goodluck Na Neman Tarwatsa Nijeriya
An dade ana rade-radin cewa sabani ya shiga
tsakanin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da Ubangidansa Cif Olusegun Obasanjo.
Hakan bai fito fili kowa ya sani ba har sai ranar Larabar da ta gabata, bayan
kafar yada labaran nan ta intanet Premium Times
(Kawar RARIYA) ta fallasa wata wasika mai yawan shafuka goma sha takwas da
Obasanjo ya aika wa Jonathan a fusace. Saboda muhimmancin wasikar RARIYA ta
fassara wa masu karatu, ga cikakkiyar wasika kamar haka:
Mai Girma Shugaban Kasa,
Dr. Goodluck Ebele Jonathan,
Shugaba, Babban Kwamandan Askarawa,
Nijeriya,
Fadar Shugaban Kasa,
Aso Villa,
Abuja.
2 Ga Disamba, 2013
Na yanke shawarar rubuta maka wannan
budaddiyar wasikar ce bisa wasu dalilai don ban da wani zabi a kan haka. Na
farko, yanayin da ake ciki da kuma abin da zai iya haifarwa ya sa na ga ya
kamata, tun kafin duk wata kafa ta toshe game da batun kasa, in fargar da kai
game da fitinar da ke iya tasowa.
Na biyu, ban samu amsa daga dukkan
wasiku hudu ko fiye da haka wadanda na rubuta maka a tsakanin shekaru biyu da
suka wuce ba. Na uku, baya ga kai, dukkan mashawartanka sun sha neman amsar
cewa, shin me Obasonjo ke nema ne?
Na hudu, na hango kamanci tsakanin
yanayin da muka dosa da kuma irin halin da muka samu kanmu a matsayin kasa a
zamanin mulkin Abacha. Na biyar, dole a yi abin da ya dace na ba da kariya ga
tsarin dimokradiyya, dorewarsa da kuma hana zubar da jini.
Na shida, dole mu guje abin da zai
kawo rabuwar kasar nan zahiri ko a fakaice na tsakanin Kudu da Arewa da kuma
Musulmi da Kirista. Na bakwai, bai kamata a bar tattalin arzikin kasar nan ya
shiga cikin mummunan yanayi ba.
Na takwas, kawayenmu na kasashen waje
da kungiyoyin kasa da kasa suna nuna damuwa game da alamomi da suke fitowa daga
kasar nan. Na tara, ya kamata Nijeriya ta yi amfani da damar da ke gareta a
yanzu wajen zuba jari a nahiyar kasancewar wannan damar ba mai dorewa ba ce. Na
goma, ina matukar damuwa da manufarka da rashin cika alkawari wanda kai kadai
ne kawai ka san inda ka fuskanta.
Mai girma shugaban kasa, a lokuta da
dama ka amince da hukuncin Ubangiji kan rawar da na taka wajen zamanka shugaban
kasa. Ka saka ni a aji na uku bayan Ubangiji da iyayenka a cikin wadanda suka
fi tasiri a rayuwarka.
Na yi imanin cewa Ubangiji ne ya
kaddara matsayin da ka samu kanka a yau sannan kuma Ubangiji ne ya kaddara
rawar da duk wadanda suka taka rawa wajen kai wa ga wannan matsayi. A ra’ayina,
na yi imanin cewa a siyasance, kai ne ka cancanta da wannan mukami na
shugabancin kasa kasancewa ka fito daga kananan kabilu na kudanci.
Idan har Obasonjo zai kai ga wannan
matsayi. Marigayi Yar’adua da Jonathan za su iya kai wa ga wannan matsayi kamar
kowane dan Nijeriya. A yau ya wuce batun shugaban kasa ya fito daga wani shiyya
ko wata kabila, amma abin da ya fi dacewa ga kasa da al’ummar Nijeriya ne kan
gaba.
A hakika, babu wata kungiya ta kabila,
harshe, addini ko wani bangare - da ke da iko samar da shugaban kasa. Haka ma,
babu wata kungiya da kashin kanta da za ta iya nada wani daga cikin ‘ya’yanta a
matsayin shugaban wata hukuma. Hakan shi ya fi zama alheri ga Nijeriya.
Na sha nanata maka cewa Ubangiji ya ji
kaina tare da yi mani abin da ban taba mafarkinsa ba. Ban neman komai daga
gareka sai dai kawai ka tafiyar da mulkin Nijeriya bisa tafarki madaidaici tare
da mayar da ita a matsayin fitacciyar kasa wanda a haka ne nake ta rokonka kuma
zan ci gaba da yin haka. Har yanzu kuma ba ka yi abin da al’ummarNijeriya ke sa
rai daga gareka ba.
A bisa matsayin da aka taba rikewa,
dole ka dauki nauyin abin da ke faruwa da kuma na gazawa a Nijeriya sannan a
duk yadda za ta kasance wasu za su dora alhakin a wuyarka kuma Ubangiji zai
tambayeka.
Na samu wata dama na gudanar da hulda
da kai a ‘yan kwanakin nan, na yanke hukunci cikin ko bakin ciki ko na farin
ciki kan cewa idan da za ka iya nesantar da bukatarka ta siyasa da ta kashin
kai, ka mayar da hankali kan batun kasa sannan ka ja layi tsakanin mashawartan
banza da kuma wadanda za su ki gaya maka gaskiya don suna tunanin ba za ka so
jin haka ba. Hakan shi zai fi dacewa.
A kan matsayi biyar da Ubangijinka ya
dora maka wani babban nauyi na jagorancin jam’iyya mai mulkin kasa, shugabancin
gwamnatin tarayya, shugaban hafsoshin Nijeriya, babban mai tsaron kasa da kuma
shugabancin siyasar kasar nan.
Wadannan mukamai su ne suka tabbatar
da kai a matsayin shugaban kasa sannan yayin da nauyin zai iya yi maka yawa, za
ka iya wakilta iko ga wani da ka amince da shi, amma dukkan nauyin yana a kanka
ko ka so ko ka ki.
Zan fara da shugabancin jam’iyya mai
mulkin kasa. Mafi yawanmu muna mamaki kan rikicin da ke faruwa a cikin
jam’iyyar. Yawancin ‘ya’yan jam’iyyar suna dora laifin kan shugaban jam’iyyar
na kasa. Na fahinci cewa, akwai wasu ‘yan fadar shugaban kasa da ke kokarin
nuna wa duniya duk laifinmu ne.
Amma batun ya fito fili a lokacin da
shugaban jam’iyyar ya yi ikirarin cewa, duk abin da ya aikata sai ya samu
amincewa daga shugaban kasa idan kuma ya saba ra’ayin shugaban, sai ya aiwatar
da sauye-sauye, ta haka mun fahinci cewa mafi yawan matakan da shugaban
jam’iyyar ke bi na kashin kansa ne amma kuma yana da cikakken goyon bayan
shugaban kasa.
Rashin adalci ne a ci gaba da ganin
laifin shugaban jam’iyyar game da rikice-rikicen da jam’iyyar ta samu kanta a
ciki. Shi dai shugaban jam’iyyar yana taka rawar ubangidansa ne. Shi kuma uban
gidan yana son kai wa ga wata manufa ce mai kunshe da makirci.
A cikin watanni biyu da suka shige,
Mai girma shugaban kasa ka tabbatar mani ka bayyana ra’ayin sake tsayawa takara
a zaben 2015, nan take na fito fili na nuna maka cewa, alamomi da matakan da ka
ke bi duk sun nuna akasin haka. Ka tabbatar wa wani na irin wannan bayanin
wanda shi ma yana da irin nawa ra’ayin. Dolo ne kawai zai yarda da kalamanka
idan har aka yi la’akari da abubuwan da suke faruwa a yanzu. Wannan ba wata
gwaninta ba ce.
Za ka iya bin tafarkin mutunci. Duk da
yake ba ka bayyana mani matsayinka ta kowace fuska ba, ya kamata ka yi nazarin
abin da ya faru a shekarar 2011. Na je jihar Binue don halartar bikin diyar
daya daga cikin ma’aikatana, Bitalis Ortese. Gwamna Suswan ya karbi bakunci na.
Ya shaida mani cewa ka amince ka yi wa’adi guda da nufin samun goyon bayan
shiyyar Arewa.
Na yanke shawarar tuntubarka, kuma ba
ka jinkirta wajen tabbatar mani da cewa, kana kan gaba a jerin masu ra’ayin
wa’adi guda na shekara shida ba kan cewa da zarar ka kammala sauran wa’adin
Marigayi Yar’adua da kuma wa’adin shekaru hudu wanda zai kama shekara shida
kenan, ba ka bukatar sake karin wa’adi.
Daga baya na samu labari daga wata
majiya ta kusa da kai kan cewa, ka gabatar da irin wannan alkawarin a wani
wurin, a kan haka ne na saka wadannan kalaman a jawabin da na gabatar a lokacin
kammala yakin neman kuri’unka a shekarar 2011 kamar haka:
“ Yakamata a yaba wa PDP a matsayin
jam’iyyar da ita kadai ta rungumi tsarin raba daidai da na karba-karba a tsarin
kundin mulkinta. Jam’iyyar ta kawo daidaito a siyasance da kuma mulkin kasa.
Ban san wanda zai zama shugaban kasa bayan wa’adin Dr. Goodluck Jonathan sun
cika ba. Ubangiji zai kaddara haka. Amma a bisa tsarin PDP, zan iya hasashe kan
ko daga wata shiyya wanda zai gaji Shugaba Jonathan zai fito. Kuma babu yadda
za a canja wani tsarin dimokradiyya na cikin gida.’’
A takaice, rashin kishi da makirci ne
suka haifar da kiyayyar kabilanci da na addini da suka bayyana a kwanakin nan
wanda kuma zai wargaza kasar nan. Hakan ya saba tunanin wadanda suka sadaukar
da rayukansu wajen hadin kan kasar nan kuma ina cikin wannan rukunin mutanen
sannan kuma zan sake bin wannan mataki idan har zai zama alheri ga kasar nan.
Zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga wadanda suka kama wannan tafarki
da su sake nazari. A matsayina na dan Nijeriya kuma dan kabilar Yarbawa, ina
alfahari da wadannan tambarin biyu.
A wannan yanayi, ina son in jaddada
abin da na ke yawan nanata wa. Zaben Goodluck Jonathan bisa kwarewa a matsayin
shugaban kasa zai kara karfafa hadin kan Nijeriya da tsarin dimokradiyya kuma
zai kai mu ga ci. Akwai rahotannin da suke nuna cewa, Dr, Jonathan ya yanke
shawarar bin matakin yin wa’adi guda na mulki. Idan haka ne, ko mun sani ko mun
jahilci haka, wannan sadaukarwa ce. A maimakon mu zarge shi, ya kamata mu yaba
masa kasancewa ya dauki tafarki madaidaici.
Idan ka yi nasarar lashe zabe, abin da
za ka fara tunani a kai shi ne maganar zango daya na shekaru shida. Hakan ya
janyo hankalina, na cewar kana nufin abin da ka fada min kafin na yi a jawabi a
wurin yakin neman zabenka. Ya shugaba, duk ma abin da ka tsara ko ka shirya, ba
zan iya maida martani ba akan maganar zangon mulki karo na biyu, ko kamar yadda
wasu mutane suke cewa zango na uku. A matsayinka na shugaba, dole ka fi maida
hankali kan abubuwa guda biyu, da suka hada da gaskiya da karamci, wadanda
dukkan su abubuwa ne masu matukar muhimmanci a dabi’ance. Ina son ganin duk
wani mutum a ofishin shugaban kasa, namiji ko mace wanda za a aminta da shi,
wanda yake karrama maganarsa da dabi’arsa, zan girmama ka idan ka dauki
wadannan dabi’u don martaba wannan ofishi. Chinua Achebe ya ce “daya daga cikin
hanyoyin da ake tantance mai gaskiya shi ne rashin karya alkawari.” Wannan
darasi ne ga dukkan shugabanni ciki har da kai da ni, duk da haka, shugaba,
bari na yi fata, kamar yadda ka fada ba ka taba fada wa wani cewar za ka yi
takara ba, abin da muke gani kuma muke ji, aiki ne na makusantanka, idan ka yi
haka za ka zama shugaban da za a iya yarda da shi ba tare da daukarka makaryaci
ba.
Watakila, kana bukatar ka san cewa, da
dama daga cikin ‘yan jam’iyya sun damu, saboda taimaka wa wasu ‘yan takara na
wasu jam’iyyu a zaben gwamna a jihohi, don yin alkawarin goya ma baya a zaben
da ya wuce ko a na gaba wanda har yanzu ba ka bayyana matsayarka ba. Ta faru a
Lagos a 2011, lokacin da Bola Tinubu ya zo Abuja, ku ka yi yarjejeniyar za su
goya ma baya, ka yi banza da dan takarar PDP. A matsayin shugaban amintattu, na
yi magana da kai a lokacin. Ya faru a jihar Ondo, inda ake da kwararan shedu.
A zahiri na taso ma da irin wadannan
batutuwa a sauran jihohin na Kudu maso Yamma, inda wasu ‘ya’yan PDP suka shiga
goyon bayan jam’iyyar LP, saboda dalilin zaben kasa, jam’iyyar ba ta da wani
dan takarar shugaban kasa sai kai. Haka ya faru a jihar Edo, wadanda suka san
abinda ya faru ba su yi shiru ba kan hakan, kuma ka san hakan. A fili yake a
Anambra an samu koma baya, idan a matsayinka na jagoran jam’iyyar ba za ka iya
goya wa dan takararta baya ba, ba ka da wani amfani a jam’iyyar.
Duk da haka, ina fatan nasara ga
jam’iyyar, kuma kamar yadda na fada a baya ina fatan nasara ga Goodluck, idan
irin haka ta ci gaba da wanzuwa a cikin jam’iyyar, za ta iya rushewar da ba za
ta taba gyaruwa ba. A irin wannan yanayi Nijeriya a matsayin kasa abin zai iya
shafe ta ba iya PDP kadai ba. Ba na fatan sake ganin zubar jini a lokacin zabe
a kasar nan. Ya shugaba, ka tuna abin da ya faru a lokutan zaben 2011 da irin
alkawuran da ka yi a lokacin yakin neman zabe. Ka ce “Zaben ka ba shi da wata
martaba idan aka hada da digo jinin dan Nijeriya”. Daga gare ka duk abin da ya
kamata, ya kamata ya zama, ya kamata ka bar zaman lafiya, kwanciyar hankali da
walwala, kyakkyawar gwamnati, da ci gaban ‘yan Nijeriya, hakan nauyi ne da ya
rataya a wuyanka, za ka iya, kuma ina rokon ka yi hakan.
Duk irin rikicin da zai faru a PDP,
sannan duk wani abu da za ka ji ko makusantanka za su ji, kai a matsayin
jagoran jam’iyyar, kana da nauyin da ya rataya a wuyanka don samar da mafita da
daidaita ta. Idan PDP a matsayin jam’iyya mai mulki ta rushe, haka zai zama
karo na farko tun bayan samun ‘yancin kan Nijeriya da jam’iyyar siyasa ta rushe
ba ta dalilin juyin mulki ba. Na zauna da gwamnonin PDP har sau biyu, don
daidaitawa, na kuma bayyana ma yadda muka yi da su, kuma makusantanka sun san
duk yadda aka yi. Amma a karshe na fada ma cewa na gano abubuwa guda biyar daga
wurin gwamnonin da suke bukatar kulawa ta gaggawa, a matsayinka na wanda kai
kadai ke da damar daukar wani mataki, na yi fatan ka kokarta don daukar mataki
kan wannan abubuwa. Rikicin da ya haifar da bangarenci a jam’iyyar ya san a
gayyaci wasu zababbun iyayen jam’iyyar, wadanda suka wakilci rahoton da muka
gabatar maka.
An bayyana min cewa ka yarda za ka yi
aiki da rahoton da muka gabatar maka. Na yi ma fatan alheri a duk wani
kokarinka na kawo karshen rikicin. Sai dai lokaci ba abokinka ba ne. Shugabanci
ba yana nufin karfin mulki ba kadai ba, dama ce da daukar nauyin jagorancin
al’umma, da daidaita mai kyau da marar kyau.
Shugabannin kasashen Afrika da dama
sun yi magana da ni akan na taimaka ma don daidaita jam’iyyar kamar yadda ka
roke su, saboda haka muka zo wurinka da Sanata Amadu Ali don sake tattaunawa da
kai a kan batun, sai dai ka musanta cewa ba ka roki kowane shugaba ba don yin
magana da ni. Ban yi mamaki ba, saboda na saba samun kaina a irin wannan hali.
Kuma ban yi kasa a guiwa ba, na ci gaba kokari don kare martabar ‘yan Nijeriya
da jam’iyyar.
Makabala da tattaunawa sun zama kashin
bayan dukkan wani ci gaba na rayuwar al’umma.
Idan aka yi hakan, hadin kai zai samu
kuma kowa zai yi nasara. Rikicin da ake ta fama da shi a jam’iyyar PDP, zai iya
zama silar hadin kai da kuma fahimtar juna har ta kai ga nasara. Ina fatan za
ku yi kokarin shawo kan matsalar rikicin tun kafin lokaci ya kure.
Zan iya cewa a matsayin ka na wanda
hakkin kula da lafiyar al’ummar Nijeriya ke hannunka, ya kamata ka dauki
kakkkararnmataki kan yadda za a shawo kan wannan matsalar da ma sauran wasu
matsaloli makamantan haka. Idan ana batun matsalolin da suka addabi yankin Neja
Delta kamar su, garkuwa da mutane, fashi da makami, farisi da makantan su da
kuma rikicin kungiyar Boko Haram, tsananta tsaro ba shi ne mafita ba. Gano
tushen kugiyar Boko Haram da dalilan da ya sa aka kafa kungiyar a ciki da wajen
kasar nan shine mafita, ba wai baza jami’an tsaro ba ne zai kawo karshen
matsalar Boko Haram ba. Akwai matsaloli da dama da suke da mafita daban daban.
Safarar kwayoyi, satar mutane, safarar bindigogi, sama da fadi da kudade,
addinanci, kabilanci, talauci, rashin aikin yi, tabarbarewar ilmi da sauran su
suna daga cikin dalilan kafa kungiyar Boko Haram. Wani sashe guda ba zai iya
kawar da wannan kungiya ba da wadannan matsalolin suka haddasa kafa ta. Za mu yake
su ne ba tare da mun san dalilin hadda wannan kungiya ba? Ana zubar da jinin
al’ummar Nijeriya, kuma muna bukatar a kawo karshen hakan. Ina fatan za ka
tashi tsaye don ganin ka magance wadannan matsalolin.
Ya mai girma shugaban kasa, babban
dalilin kasancewarka a matsayin da ka ke shine don kana dan Nijeriya. Idan
akasarin al’ummar Nijeriya da suka zabe ka ba su jefa maka kuri’a ba, da baka
kasance a matsayin da kake ba. Ka kasance dan kabilar Ijaw da ya fito daga wani
yanki na kasar nan, amma gadarar da ka ke da hakan kuskure ne wanda bai kamata
ya faru ba. Saboda a matsayinka na shugaban kasa nuna bambancin kabila ba naka
ba ne. Kuma ingiza kana yin hakan ba masoyanka ba ne, suna neman bata ka ne
tare da sanya kabilarka bakin jini a wajen sauran kabilun kasar nan. Kana sane
da cewa na kwabe kwanakin baya kan matsala makamancin haka, amma wasu ba su ji
dadin hakan ba. Ba kowa za ka dauka a matsayin abokin shawara ba. Kuma bai
kamata ka ware wani yanki ka ce sune suka zabe ka ba, ka ware wasu gefe. Ka sani
shi al’amarin siyasa wani abu ne da ke tafe da yawan jama’a. Ko da ba ka
bukatar kuri’a jama’a, jam’iyyarka tana bukata.
Sanya wasu jigajigan mutane a gaba da
sunan siyasa ko kuma umartar wasu na jikinka a asirce domin muzgunwa wasu kamar
yadda Abacha ya yi, idan har gaske ne ba zai yi wa al’ummar Nijeriya dadi ba.
Mai girma shugaban kasa ya manta cewa an zabe shi ne domin ya tabbatar da tsaro
ga dukkan al’ummar Nijeriya. Kuma babu wani da yake da ikon kashe wani domin
biya wa wani bukata. Masu tunzuraka ka muzanta wa masu adawa da kai, ba
masoyanka ba ne, makiyanka ne. Saboda siyasa ta kunshi masoya da kuma ’yan
adawa. Idan abin ya munana, wadannan masu zuga ka din, guduwa za su yi su bar
ka. Abin da ya faru a Misra, babban darasi ne gare ka.
A matsayinka na shugaban kasa komai a
hannunka ya kamata ya kasance, ba sai wani ya kawo maka ra’ayinsa ba. Da yawa
daga cikin kasashe da mutanen da suke mu’amala da Nijeriya suna kokawa da halin
da muke ciki, amma an ki a yi gyara. Suna kokawa da rashin tsaro, satar man
fetur da makamantan su. Suna kuma nuna damuwar su a kan cin hanci da rashawa da
muka kasa shawo kan matsalar. Wannan matsala ta cin hanci da rashawa, ta kai
inda ba mu tsammani a yanzu. Kuma za mu iiya cewa cin hanci da rashawa da keta
doka, yana daga cikin dalilan fadawa halin da kasar take a yanzu. Kuma idan har
baka yi kokarin magance wannan matsala ba, duk wani abin alkairin da z aka yi
babu wanda zai gani. Zai zama abin dariya. Suna kuma nuna damuwar su kan yadda
muke tafiyar da al’amuran ciki da wajen kasar nan. Ni ma zan iya goyon bayan su
ta wani bangaren saboda akwai wurare da dama da ya kamata a yi gyara. Wasu
abokan huldarmu da ke Olokola NLG ma neman janye wa suke saboda mawuyacin halin
da muka shiga, haka su ma na Brass. Dukkan su ina goyon bayan su. Kamfanonin
sun sha alwashin mayar da Nijeriya tamkar kasar Katar wajen samar da mai. Roko
na shine kada a bari wadannan kamfanoni su tafi, sannan kuma a dawo da OK NLG
domin kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya. Akasarin kamfanonin da ke aikin
mai a Nijeriya duk sun tafi, idan kuma ba su tafi ba sun daina aiki. Nijeriya
wadda ita ce Saudiyyar Afrika wajen arzikin mai, yanzu Angola ta sha gabanta ba
don komai ba, sai don rashin mayar da hankali a kan lamarin.
Mai girma shugabn kasa, bari na sake
tunatar da kai a bangaren mai da gas don kada a bar Nijeriya a baya. Yanzu haka
an gano mai da gas a wurare da dama a fadin Afrika. Ina fatan za mu lallaba
kamfanonin OK da Brass NLG don kada su tafi. Abubuwa uku na faruwa a fannin mai
da gas; a magance matsalar satar mai, a tallafawa kamfanonin da suke aikin mai
da kuma karancin masu kula da ma’aikatun. A bangaren tattalin arziki baki daya
kuma, ya zama dole mu yi fiye da yadda muke yi a yanzu. Muna ganin abubuwan da
suke faruwa, domin ba boyayyu ba ne. Babbar matsalar kuma ita ce, rashin aikin
yi ga matasa musamman a wannan lokaci da cin hanci da rashawa ya yi yawa.
Bari na sake maimaita cewa kasancewar
cin hanci da rashawa, rashin tsaro da satar man fetur na faruwa, babu yadda za
a yi a shawo kan matsalar kasar nan. Ya zama dole mu sani cewa cin hanci da
rashwa, keta doka, talauci, tarzoma da makamantansu su suka jefa kasar nan
cikin mawuyacin halin da muka tsinci kanmu. Amma babu komai, Allah yana gani
kuma zai kawo karshen wannan matsala da yardarsa.
Babban abin daukar hankalin shine,
zargiin da aka yi wa NNPC kin bayar da kusan dala tirilyan takwas ga babban
bankin kasa na kudin ganga dubu dari uku na mai da ake saidawa a duk rana,
wanda kudin sa ya kai kusa dala milyan dari tara a wata. Wannan zargin ya fito
ne daga babban bankin kasa. Ya kamata a yi bincike a kan lamarin, ba wai a yi
watsi da zargin ba. ina fatan za ka yi hakan domin a gano gaskiyar lamarin.
Duk masu hannu a irin wadannan
al’amuran, a kwana a tashi za a yi walkiya duk mu gan su Ina mai fatar zaka
dauki mataki ko da guda daya ne domin ka samu yin maganin al’amurancin hanci,
da suka dabaibaye gwamnatin ka.
Kawayen mu na kasashen waje sun dade
da sanin mu a yadda muke , watakila ma sun fi sanin kan mu. Akwai wani babban
abokina wanda shi mai fada wa mutum gaskiya ne, komai dacin ta, wani boye ma
gaskiya, da wata rufa rufa, akan abinda dole ne sai ya fito fili, da cewa ya yi
a tsare gaskiya , saboda babu abinda ya fi mutuncin mutum. Gaskiya da rashin
rub-da- ciki, suna daga cikin abubuwan da ke samar wa mutum mutunci.
Wannan abin ne ya sa na tuna da wani
abu lokacin da wani babban jami’i na bankin bunkasa afirka, ya sanar da ni
cewar wani aikin samar da ruwan sha a Fatakwal wanda gwamnatin tarayya ta bada
shawarar shi, amma kuma bankin ne zai dauki nauyin shi. Ba za’a yi shi ba
saboda takun sakar da ake yi tsakanin shugaban kasa Goodluck Jonathan , da
gwamna Rotimi Amechi, kuma ko yana so ko ba ya so,dole ne karshen watan Mayu na
2015 dole ne ya sauka daga mukamin gwamnan jihar, amma kuma su mazauna Fatakwal
din ya zama tilas su so a gyara masu yadda hanyoyin samar masu ruwa zai karu.
Ya dai dace shi shugaban kasa ya daina
irin wannan halayyar , ya kuma kwana da sanin irin wannan ba haka ya dace a
rika ji daga waen shugaban kasa ba. Idan ba kaine ka ke yi ba , wasu ne ‘yan
gaza gani , ai sai ka ja masu kunne, ko a samu cigaba da shi aikin samar da
ruwan.
Ya shugaba na bari ba ka wata shawarar
wadda ina ganin za ta taimaka har zuwa karshen rayuwar ka, kada ka dauki masu
yi maka kusanci a kan harkokin kasa tamkar makiyan ka, wasu daga cikin su ba ka
sani ba, har zuciyar su babu wata cutarwa, kamar yadda ni da kai muka kasance a
gwamnati. Da akwai masu sha’awar ganin cigaban Nijeriya kamar yadda mu ma muke
da ra’ayin haka. Ina da irin wadannan jama’ar tun lokacin dana bullo da tsarin
‘yan Nijeriya masu zama a kasashen waje, ya kamata ka fahimci wata gudunmawa da
ake so a ba ka ta hakikani, da kuma wacce ake son kawai zolaye ka. Don Allah ya
kai shugaba ka yi taka tsa-tsan da masu mataika maka , masu ba ka shawara, da
kuma sauran ‘yan gaza gani, wadanda su so suke yi su hada ka da mutane.
Allah ya kare shugabanni daga sharrin
masu zuga amin, saboda sun san abinda ka ke so, sun kuma san hanyar da za su
samar maka shi. Saboda su masu kare bukatunsu ne. Kamar dai yadda ni da kai
muka sani su masu bata al’amurra ne. Yanzu sun mallake ne domin su samu cimma
burinsu, amma ina son ka gane babu wani burin da ya fi Nijeriya da al’ummar ta.
Ina son ka gane cewar ka tuna ka fa riga ka yi tarihi, kada kuma ka bari ka yi
wani abin da zai bata tarihin nan. Na taimaka ma kamar yadda na taimaka wa ‘Yar
adua. Ni gare ni babu Arewa ko kudu, bare kuma rarrabuwar kai tsakanin Musulmi
da Kirista, ni abinda na sani kasa daya Nijeriya.
Da akwai kuma magana guda kada ka bari
ka iya amfani da sojoji don cimma wani buri naka, ko na siyasa ba tare da ka yi
la’akari da abin da ka iya shafar sauran jama’a ba, bayan nan kai kuma da akwai
abinda zai shafe ka zuwa gaba, saboda idan ka bata irin horon da aka sani da
soja, ka sa suka rikide wani abu, kai ma ba zai yi ma dadi ba, watarana. Ina
tuna maka amfanin sojoji da sauran dakarun tsaro shi ne kare kasa, ba ‘ayi
amfani da su hanyar da bata dace ba. Ina kara tuna maka kada ka bata tarihin
ka. Na san dai tun da kasanirin matsaloli masu wuya da Nijeriya ta shiga , a
shekarun da suka wuce, na kuma san a matsayin ka na mai tuka jirgin da ke dauke
da al’ummar Nijeriya ba za ka bari ya kife ba, domin idan ka bari har ya kai ga
yin haka , watakila kaima abin ya rutsa da kai. Mai cewa ko da wani abu ya faru
hakan ba zai sa wani abu ya same shi ba, wannan ba magana bace wadda ya kamata
ts fito daga mai hankali ba. Ni ko da yaushe ina ta’allaka kai na manufa itace
ina tare da’yan Nijeriya masu kishin kasa, wadanda kuma suke son cigaban
wuraren da suke gabatar da ayyukansu. Na kuma dauke su da kima babba saboda su
sun nuna sun san yadda rayuwa take. Fatar alheri da nake wa Nijeriya ya
ta’allaka ne da irin wadannan mutane saboda na san ba za su ba ni kunya ba.
Ta bangare abubuwan da kan bata mani
rai wasu lokutta ina samun bayanin abubuwan da ke faruwa ne, a gwamnatance
kokuma ta masu zaman kan su, abokan cigaba, da kuma abokan kawancen mu wadanda
suka hulda da Nijeriya. Saboda kuw da akwai lokacin da na kan fita zuwa
kasashen waje, idan na dawo gida kuma sai na yi bincike saboda na gano ainihin
gaskiyar lamarin. Na kan samu wasu da akwai kanshin gaskiya, amma wasu kuwa
abin ko kare ma bai ci. Da akwai kasashen da ke koyi da abubuwan da suke faruwa
a Nijeriya saboda su samu cigaba, to ashe ke nan idan har muka rika yin
abubuwan da basu dace ba, za’a kai ga lokacin da zai zo a daina ganin mutuncin
mu.
Da yake na riga na san ire iren
abubuwan da suke faruwa a in da kake yanzu, wato maganar shugabanci shi yasa
nake baka shawara wadda ta dace, kuma b azan gaj da yi haka ba , tsakani na da
Allah, da haka kuma nake ganin ni nayi abin da ya dace wato ba gwamnatin ka
shawara, da ita jam’iyyar PDP, da kuma kasar mu Nijeriya, ina rokon Allah ne da
ya kare ka , ganin irin nauyin da ke gaban ka. Na san da masu ganin ni makiyin
ka ne, ko gwamnatin ka,’yan kabilar ka , ko kuma masu baka shawara, su irin
wadannan mutanen na dauke su masu wasan yara. Idan naga wani hadari na tafe ya
same ka, zan nuna maka shi, ko kuma ina yi maganin shi kamar dai yadda na saba
yi tun can baya. Amma kuma b azan goyi bayan abinda na san a gaba ba zai zame
wa ‘yan Nijeriya alheri ba, ba tare da na yi la’akari da wanda ya sa a yi
wannan abin ko ya ke dauke da shi.
Ya shugaban kasa yanzu ni bani tsoron
in ki yarda da wani abu , ko in yarda da shi, amma abin zai kasance ne ko wane
lokaci akan muhimmancin al’amarin ko kuma akasin haka. Ko kuma idan al’amarin
siyasa ne abinda na san zai amfani kasa. Lokacin da na zauna gidan kurkuku a
Yola na koyi darussa da dama a rayuwa ta, ba wani abin bakin cikin da ban gani
ba, wani ma gara a ce mutuwa ta dauki mutum, wannan kuma saboda wani mai mulkin
kama karya na soja da yake son ya cigaba da mulkin shi. Mutuwa ita ce karshen
ko wane dan Adam , tana zuwa ne idan lokaci ya yi, wani cin mutunci da aka rika
yi wa ‘yan uwana, abokaina, sai kuma wasu jami’an tsaro da suka gallaza ma
wasu, ba don komai ba sai don saboda suna goyon bayan sabuwar PDP, ko masu
goyon bayan gwamnonin da suka bar jam’iyyar PDP,ko kuma anaiko su ne su cima
mutane mutunci a madadin ka, wannan duk nasan watarana sai labarai kamar yadda
wasu yanzu dai sai dai ayi labarin. Wannan yin amfani ne da jami’an tsaro ta
hanyar da bata dace ba, iri haka kuma an taba yin shi lokacin mulkin marigayi
Abacha , an dai ta fadin karya da karairayi dangane da ni abubuwan da suka fito
daga fadar shugaban kasa.
Maganganun da ake na cewa na taimaka
maka wajen baka shawara ka amince da mai aikata laifin da ake jiran kama shi a
London ko Amurka, domin su taiamaka ma shuganannin PDP da aka zabe su ta hanyar
da ta dace, a sashem Kudu maso Yamma, wannan ba abinda ya dace bane kuma da
akwai hadari tattare da furta haka din. Ba wanda acikin hankalin shi zai yadda
da wannan labara, hakanan kuma ko a jihar Ogun ko kuma sashen kudu maso yammam,
da zai yarda da wannan sakarcin ,wannan wata manuniya ce da ke nuna mutane na
iya amfani da hanyoyi da dama dominsu samu cimma burin sun a siyasa kokuma
akasin haka.
Abin tausayi! A shekaruna babu abin da
zai iya kange ni daga duk wani a batu da nake ganin shi ne mafi alheri ga
Nijeriya, Afrika da ma duniya baki daya. Na yi imanin cewa samar da hadin kai
da tasiri a PDP ta kowace fuska shi ne mafi alheri ga Nijeriya. A kan haka,
idan har ra’ayoyinmu sun yi tarayya, za mu kai ga tudun na-tsira tare.
Matakin da ku ka bi kai da
mukarrabanka wajen nada mugun mutu wanda ake nema ruwa a jallo a kasar waje don
fuskantar shari’a wanda kuma ya taimaka wajen yayata cin hanci a bangaren
shari’a a matsayin shugaban PDP na shiyyar Kudu maso Yamma, ya kai matuka wajen
ha’intar kasar nan a siyasance kuma tamkar cin fuska ce ga ‘ya’yan jam’iyyar
PDP da kuma al’ummar yankin.
Ina ganin siyasata ta jibinci akida
kuma ba zan lamunci wata hulda da mugum mutum a siyasance ba, ballatana a ce
shi ne shugaban shiyyar da na fito. Wannan mataki ya ruguza abin da PDP ta yi
imani da shi tun lokacin da aka kafata. Kin bin matakin da ya dace a kan
Kashamu, mutumin da ake nema a Amurka bisa laifukan safarar miyagun kwayoyi da
almundahanar kudade, ya kara tabbatar da rahotannin da ake yayata wa na hannun
manyan ‘yan siyasa game da safarar miyagun kwayoyi.
Ta kawace fuska, hakan ba zai yi wa
Nijeriya alfanu ba. Nan ba da jimawa, dillalan kwayoyin za su kwace ragamar
harkokin tattalin arzikin kasa, a game da zabe kuma, za su iya sayen ‘yan
takara, jam’iyya kuma daga karshe za su iya sayen madafun mulki ko kuma su dora
kansu kan mulki.
Ubangiji bai taba goyon bayan miyagu
ba kuma lallai zai ceto PDP da al’ummar Nijeriya daga hannun wadanda ke neman
wargazata. Idan hakan bai samu ba sannan kuma aka kasa kwato jam’iyyar daga
hannun wadannan miyagun, dole mutane masu mutunci su janye jikinsu daga
jam’iyyar.
Zan yi amfani da wannan dama wajen yin
kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da suka hada da gwamnoni, ‘yan majalisa da sauransu
wadanda ke ganin an kuntata masu da su ba da goyon bayan idan har Shugaba
Jonathan ya bi matakan da suka dace na warware matsalolin da ke damun jam’iyyar
domin kuwa shi ne wuka da dama kan batun. Na ji ana yayata wa cewa, gwamnonin
da suka canja sheka duk ‘ya’yana ne.
Na fara mamaki, kama daga kasa zuwa
sama, duk wani mai rike da wani mukami, zai kasance ko kai tsaye ko a fakaice
ya fada wannan rukuni na ‘ya’yana. Duk wanda ke da tunanin akasin haka zai
kasance kamar kogi ce wadda ta manta da asalinta. Amma a matsayina na uba
nagari, abin da nake bukata shi ne, neman hanyar sulhu na sake hade kan iyalina
don samun ci gaba ga kasa. A tsarin dimokradiyya, ana zabin shugabanni ne don
su rage nauyin da ke kan jama’a, samar masu ‘yanci, zabin rayuwa, adalci da
tabbatar masu da gwamnati tagari a maimakon a yaudara, danniya da kuma raunana
su.
Duk abin da mutum ya shuka shi zai
girba, ba na fatan ka kai ‘yan Nijeriya makura, hart a kais u ga yin addu’uar
Allah ya sa daga Goodluck Jonathan ba za su sake zaben dan kabilar Ijaw ba har
abada. Idan kunne ya ji dai to jiki ya tsira. Ba fatan hakan nake yi ba, amma
dai biri ya yi kama da mutum.
Shawarata ta karshe, ya kamata ka koyi
darasi a tarihin baya, kuma ka da ka yi tunanin ‘yan Nijeriya shashashai ne, ka
daina karyata abin da ka san ka yi, ka daina rufa-rufa. Ka tsare gaskiya da
dattako domin ka dawo wa kanka da martabarka daga zukatan ‘yan Nijeriya. Saboda
sun fa zura maka ido suna kallon duk wani abin da ake dangantawa da kai, a
yanzu babu sauran mai gaskata zantukanka. Na san kana da ikon da za ka iya ceto
PDP. Ka yi amfani da damarka da mulkinka domin inganta kasa da jama’arta. Don
Allah ka fara nuna wasu halaye na mai kishin kasa gaba dayanta. Zan yi kira da
a rika girmama ofishin shugaban kasa, domin, mulkin na nan, sai dai mai ,mulkin
ya tafi ya bar gadon mulkin.
Haka kuma, kana dai sane da yadda masu
zuba jari ke ta barin Nijeriya.
Daga karshe kuma, shirin da ka bullo
ds shi taron daddale kasa, yanzu ya zama abin firgici ga ‘yan Nijeriya, yana assasa
rashin hadin kai, rudani, wanda idan ana so ya yi tasiri, tilas sai an sa ido
domin cin moriyarsa sosai kada a bari ya haifar da rudani. Idan aka bi da shi
ta hanyar da ta dace, zai zama alfanu kuma zai ti tasiri ba tare da cusa wata
boyayyar manufa ba.
Shugaban kasa, ina yi maka fatan
alheri.
Jaridar RARIYA ce ta fassara wasikar daga harshen Turanci zuwa Hausa.
No comments:
Post a Comment