Shugaban Hukumar INEC |
Bayan kammala zaɓen
gwamnan jihar Anambra tana shirin barin baya da ƙura tsakanin hukumar INEC da
'yan adawa waɗanda su ka ce ba su yarda da tsarin zaɓen ba.
An dai share
tsawon watanni kusan shida ana shiri ana kuma jibge jami'an tsaron da babu
irinsu, to sai dai kuma an ƙare a cikin ruɗani a jihar Anambra inda yanzu haka
zaɓen gwamnan jihar ke shirin barin baya da ƙura tun bai nisa ba.
Duk da cewar dai
jam'iyyar APGA da ke mulki a jihar dai ce ke kan gaba da ƙuri'u sama da
174,000, sakamakon zaɓen dai ya gaza kammala a ɓangren hukumar zaɓen da ta ce
har yanzu da sauran gyara kuma ke shirin saka wata ranar kammala sassan da ta
ke ganin da sauran aiki a cikinsu.
Ra'ayi dai ya
bambanta tsakanin hukumar da ta ce tana shirin sake zaɓen ne a rumfunan da ke
fuskantar rikici, da kuma manyan jam'iyyu uku masu adawa da ke cewar sake ɗaukacin
zaɓen na zaman mafita na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci a cikinsa.
Zaɓen na Anambra
da ake yiwa kallon zakaran gwajin dafi ga ƙoƙarin hukumar zaɓen na shirya zaɓuka
masu karɓuwa a shekara ta 2015 dai tuni ya fara jawo ɗar-ɗar a tsakanin 'yan
siyasa dama masu kallon baƙin hadari na siyasar rikici a gaba. Ga Tarrayar
Najeriyar da ta fuskanci mummunan rikicin da yai barazanar ganin bayanta a
shekara ta 2011, sannan kuma ake yiwa kallon dan ba na tashe tashen hankulan da
suka mamaye ɗaukacin ƙasar ya zuwa yanzu.
Tuni dai aka fara
kiran karatu na gazawa ga jami'an hukumar zaɓen da suka kai ga kisa na maƙudai
na kuɗi ba tare da kai wa ga kwantar da hankula cikin jiha ɗaya tilo ba, abun
kuma da a faɗar dr Umar Ardo da ke nazari bisa harkoki na siyasa ke tabbatar da
irin halayya ta mutanen da ke jagorantar ayyukan hukumar yanzu haka.
Adalaci a cikin
alƙalanci ko kuma son zuciya da cika ɓuri na siyasa dai daga dukkan alamu
Tarrayar Najeriya na tsakanin tabbatar da zaɓe mai adalci ko kuma fuskantar ruɗanin
da ke iya mummunar illa ga ɗaukacin fagen siaysar ƙasar. Abun kuma da ya kai ga
mahukuntan ƙasar a matakai daban-daban jerin alkawuran darma sa'a da nufin bai
wa maras'da kunya yayin zaɓukan da tuni suka kama hanyar raba kan yan ƙasar
tsakanin addini da ƙabila. To sai dai kuma a faɗar Buba Galadima da ke zaman
jigon jam'iyyar APC matsalar ta Anambra na zaman buɗe ido a garesu na sabon
shiri da nufin tunkarar sabon ƙalubalen da ƙasar ta Najeriya ke shirin fuskanta
a siyasance.
To sai dai kuma
idan ta yi ɗaci ta kuma lalace ga masu adawa a Anambra ga 'yar uwarsu ta APGA
da ta kama hanyar sake ɗare mulki a jihar wai duk wani ƙorafi na 'yan adawa bai
wuci bakin masu shirin rasa damar mulki ba a faɗar Sani Abdullahi Shinkafi da
ke zaman sakataren jam'iyyar na ƙasa .Abun jira a gani dai na zaman mafitar
rikicin da ma matakai na gaba a ɓangaren hukumar zaɓen da ke ƙara fuskantar
fushi da ba daɗi na 'yan ƙasar a kullu yaumin.
No comments:
Post a Comment