Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Tuesday, September 4, 2012
Mallam Nasiru el-Rufai: Dangajere Kusar Yaki!
Kamar yadda tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya taba fada a wata hira da ya yi da Jaridar This Day, cewar tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya buka ce shi da ya zabo masa mutum mai jini a jika kuma wanda ba shi da tsoro, wanda idan ma ta kama zai iya yin akuya ga mahaifiyar obasanjon don ya bashi mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja saboda ya dai-daitawa mutane sahu daga karkacewar da ya yi. Atiku ya shaidawa Obsanjo cewar Nasan wasu mutane guda biyu abokai da Allah bai sanya sun taba hada hanya da tsoron wani mahaluki ba a fadin tarayyar kasar nan, daya daga cikinsu kuwa shi ne Nasiru el-Rufai, wanda a lokacin shine shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnati ta kasa (Director General Bureau of Public Enterprises (BPE) and the Secretary of the National Council of Privatisation).
Tabbas Mallam Nasiru el-Rufai ya nuna cewar shi ba matsoraci bane, lokacin da majalisa ta zo tantance shi a matsayin mutumin da za’a nada minister. Domin idan zamu iya tunawa anyi dauki babu dadi da el-Rufai kafin a nada shi minister, inda aka nemi ya bayar da cin-hanci shi kuma ya yi kememe ya ki bayarwa, wanda wannan ta sanya wasu da yawa daga cikin shugabannin majalisa a wancan lokacin jin kunya ciki kuwa harda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Nasir Ibrahim Mantu, inda el-Rufai ya bayyana a majalisa dauke da al-qur’ani a hannunsa ya yi rantsuwa cewar an nemi hanci daga wajensa, kuma shi Mantu ya karyata, inda el-Rufai ya bukaci Mantu shima da ya rantse da Al-qur’ani amma hakan ta gagara inda ya ce shifa bashi da tsarki duk kuwa da cewar akwai makewayi a majalisar, kusan zamu iya cewa tun a wannan lokacin el-Rufai ya nuna jarumtaka da tabbatarwa da duniya cewar shifa ba mutumin banza bane. Wannan namijin kokari da bajinta da el-Rufai ya nuna, shi ya sa jihar Georgia da ke kasar Amerika ta bashi izinin zama dan wannan jihar, wanda yanzu haka el-Rufai yana daga cikin ‘yan Najeriya da suke zuwa kasar Amerika ba tare da anyi musu binciken kwakwaf ba.
Lokacin da Mallam Nasiru el-Rufai ya zama babban ministan babban birnin tarayya ya nuna babu sani babu sabo. Domin ya kau-da duk wasu gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba, ciki kuwa harda gidan matar shugaban kasa marigayiya Stella Obasanjo da gidan shugaban PDP na wannan lokacin Sanata Amadu Ali da wasu manya manyan kusoshin gwamnati a wancan lokacin. Haka dai el-Rufai ya ringa sanya gireda yana ma-ke duk wani gini da aka gina shi ba bisa kai’da ba a Habuja. Mallam Nasiru el-Rufai kusan shine ministan Abuja mafi dadewa a tarihin wannan birni tun daga 1999 har zuwa 2007, kuma ya yi aiki dai-dai nasa.
Tun da Marigayi Mallam Umaru Yar’Adua ya zama shugaban kasa el-Rufai ya tsallake yabar kasar nan inda ya tafi kasar Amerika ya koma makaranta, ya halarci kwasa kwasai da dama a fannoni daban daban, ciki kuwa harda katafariyar Jami’arnan ta Harvard, kadan daga Makarantun da el-Rufai ya halarta sun hada da Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria, Najeryia, Jami’ar London ko University of London a Burtaniya da Harvard Business School, Arthur D. Little School of Management a birnin Massachusetts da Georgetown University da School of Foreign Services a birnin Washington dukkaninisu a kasar Amerika da kuma D.C. da John F. Kennedy School of Government da Harvard University duk dai a can Amerika. Sannan el-Rufai yana da babbar Lambar yabo ta kasa wadda ake kira OFR (Officer of the Order of the Federal Republic of Nigeria) wadda aka bashi tun yana BFE, haka kuma a shekarar 2005 jami’ar Abuja ko University of Abuja ta bashi Babban digirin girmamawa da ake kira Doctorate Degree D.Sc (honoris causa).
Bayan da el-Rufai ya dawo gida Najeriya, ya fada Jam’iyyar adawa ta CPC inda ya mara baya ga takarar tsohon shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari duk kuwa da ana kallon zai goya baya ne ga takarar babban abokinsa wato Mallam Nuhu Ribadu. A halin yanzu dai Mallam Nasiru el-Rufai shi ne babban bakaniken jam’iyyar ta CPC wadda Buharin ya dora masa wannan nauyi na dai-daita sahun jam’iyyar kamar yadda a yiwa birnin tarayya Abuja, saboda fama da matsaloli da jam’iyyar ta ke yi a kusan daukacin jihohin kasarnan.
Bayan haka kuma, el-Rufai shi ne kusan mutum daya tilo wanda tauraruwarsa ke haskawa wajen adawa da gwamnati mai ci ta Goodluck Jonathan da kuma Jam’iyyar PDP. Mallam Nasir el-Rufai ya dauki lokaci yana sharhi akan kasafin kudi na wannan shekarar ta 2012 inda ya yi kaca-kaca da wannan gwamnatin ya nuna ma basu san me suke yi ba. Hakan ta sanya el-Rufai ya dinga daukan hankalin jama’a a ciki da wajen kasarnan wajen yadda yake fashin baki a harkar tafiyar da wannan gwamnatin musamman a harkar da ta shafi tattalin arziki, wannan ta sanya jami’an SSS suka ringa sanya masa tarko suna kamashi a kusan duk lokacin da zai yi wata tafiya zuwa kasashen waje, haka nan yake tsallake irin wannan turaku da ake sanya masa.
Bahaushe ya ce al-kalami ya fi Takobi, lallai wannan magana haka ta ke, domin shakka babu wannan gwamnati mai ci babu wani alkalami da ta ke jin tsoro a kullum kamar na el-Rufai, domin sun san cewar mai ilimin gaske ne kuma masani ta fannoni da daman gaske. Mallam Nasiru el-Rufai dai idan ka ganshi irin mutanan nan ne da zaka gansu ‘yan tsirit wato ba shi da wani cika ido, wannan ce ma ta sanya abokansa suke masa lakabi da sunan GIANT wato wani babban mutum kamar dai yadda Bahaushe yake ce wa gajere malam dogo. Lallai kam ya zuwa yanzu babu wani daga cikin ‘yan Adawa wanda tauraruwarsa take haskawa kamar el-Rufai ba, kuma duk wannan ya faru ne ta sanadiyar al-kalaminsa da yake caccakar wannan gwamnati da shi. Tabbas maganar Bahaushe gaskiya ce da ya ce Alkamai ya fi takobi, domin idan da fada za’a iya da takobi watakila da farat daya za’a gama da el-Rufai amma da yake fadan na alkalami ne, babu yadda aka iya da shi sai dai a kayar da shi da hujja idan ana da ita.
Lallai Najeriya tana bukatar mutane masu gaskiya wadan da zasu iya yakar cin-hanci da rashawa da gaskiya kuma hazikai irinsu Mallam Nasiru el-Rufai.
Daga marubuci Mallam Yasir Ramadan Gwale.
Mallam Yasir, sannu da kokari Allah ya kara basira da ilimi. Tabbas ka fada da yawa akan Zakin PDP el-Rufai. Allah ya kara tawada a alkalaminka.
ReplyDelete