Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Monday, March 12, 2012
Shin Wai Za'a Rufe Shafin Sada Zumunta na Facebook?
Shin yaushe za'a rufe shafin Facebook? Shin wai za'a rufe shafin Facebook? Ranar 15 March, 2012 shafin Facebook zai daina aiki. Zan koma 2go ko Twitter idan aka rufe Facebook. Abokaina na yafe muka, zan koma 2go tunda za'a rufe shafin Facebook. Wannan kadan kenan daga cikin irin rubututtukan da na rinka cin karo da su a shafin sada zumunta na Facebook, wasu kuma kai tsaye suka kira ni a waya suna tambayata gaskiyar lamari akan maganar rufe shafin na Facebook.
Wannan dalili yasa na shiga binciken gano gaskiyar al'amarin. Abinda ya bani mamaki shi ne wannan jita - jita an yada ta ne tun shekarar da ta wuce a watan January 2011, sai ga shi an dawo da ita a wannan shekara ta 2012.
FARKON AL'AMARI - A ranar 9 January, 2011 wata jarida mai suna Weekly World News dake kasar America, ta buga wata mukala a shafinta na Yanar Gizo (Internet) dauke da cewa "Za a Rufe Shafin Sada Zumunta Na Facebook ranar 15 March, 2011" a cikin mukalar an bayyana dalilan da zasu sa a rufe shafin kamar haka: Mark Zurkerberg shugaban kamfani kuma wanda ya kirkiro shafin ya bayyana cewa shafin ya fi karfin hankalinsa, ya kuma ruguza masa rayuwarsa, saboda haka yana so rayuwarsa ta dawo kamar yadda take a da kafin bude shafin na Facebook. Sannan Mark Zuckerberg ya kara da cewa shafin Facebook ya shagaltar da mutane inda ba sa iya yin abokanai ko kawaye a zahiri sai dai a shafukan Yanar Gizo, saboda haka duk wanda ya ajiye hotunansa a ma'ajiyar hotuna (Album) a shafin na Facebook yayi kokarin canja musu ma'ajiya kafin ranar 15 March, 2012 daga ranar mutum ba zai sake ganinsu ba.
Wannan kadan kenan daga cikin dalilan da jaridar ta Weekly World News ta bayyana zai sa a rufe shafin na Facebook, a wannan lokacin wannan mukala ta tada hankulan jama'a musamman wadanda suka sadaukar da lokutansu ga shafin na Facebook (Facebook addicted).
Ana cikin wannan hali ne sai gidan television na CNN ya yi rahoto na musamman akan jita - jitar, wanda suka bayyana cewa sun samu cikakken bayani daga hukumar gudanarwar kamfani na Facebook dake tabbatar da labarin da jaridar Weekly World News ta buga karya ce tsagwaranta.
A tsakiyar wannan sati ranar 13 January, 2011 shafin Facebook ya fito da sanarwa ta musamman akan cewa ba gaskiya ba ne, maganar cewa za a rufe shafin, kuma suka tabbatar da cewa babu wani dalili da zai sa a rufe shafin har abada.
Wannan suna kadan daga abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata, sai kuma wannan shekarar ma aka sake dawo da jita - jitar, wadda wasu ke kwafo abubuwa da suka faru a shekarar da ta gabata suna yadawa.
A karshe gaskiyar al'amari akan wannan magana ta rufe shafin na Facebook ba gaskiya ba ce. Idan bamu manta ba a watannin baya da suka gabata kadan shafin na Facebook ya saka lallar hajojin kamfanin a kasuwa. Sannan a watan December na 2011 aka bayyana shafin Facebook a matsayin na biyu a duniya wurin samun maziyarta a kullum bayan shafin bincike na Google.
Ziyarci Dandalin Bashir Ahmad a shafin Facebook (http://facebook.com/dandalinbashirahmad)
Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020
No comments:
Post a Comment