Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Tuesday, March 20, 2012
Mun Rufe Kofar Tattaunawa Da Gwamnati - Boko Haram
Kungiyar jama'atu Ahlussunah
lidda'awati wal jihad da aka fi sani
da suna, Boko Haram a Najeriya, ta
ce a yanzu ta rufe kofar duk wata
tattaunawa da gwamnatin kasar
domin a ganinsu ba da gaske
gwamnatin take ba.
Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa,
da yawunta majalisar kula da
al'amuran shari'a a Najeriya ta fara
tattaunawa da gwamnatin Najeriya,
tattaunawar da ta rushe a karshen
makon da ya gabata.
Wani dake ikirarin magana da
yawun kungiyar da ake wa lakabi
da Abu Qaqa ne ya bayyana haka a
hira da manema labarai a birnin
Maiduguri.
Mai magana da yawun kungiyar ta
Boko Haram ya ce sun ga ya wajaba
ne su yi wannan karin bayani, ganin
cewa batun tattauanawar su da
gwamnatin tarayya ya mamaye
kafofin yada labarai a 'yan
kwanakin nan.
Abu Qaqa ya ce, sun amsa kiran da
Dr Datti Ahmad, shugaban majalisar
kula da al'amuran shari'ar Musulunci
a Najeriya ya yi musu na a tattauna
ne, saboda suna ganin kimar sa,
amma tun asali suna da shakku
akan ko da gaske gwamnati take
kan batun tattaunawar.
Mai magana da yawun kungiyar
Boko Haram din ya ce, ba da jimawa
bane shugaban Najeriya Goodluck
Jonathan ya yi kira ga kungiyarsu
da ta fito a tattauna da su, su kuma
bayyana bukatunsu, bukatun da ya
ce sun bayyana wadanda suka
kunshi sako musu dukkan 'yan
kungiyar su da aka kama ba tare da
gindaya wani sharadi ba.
''ABIN KAICO NE''
Ya ce an fara ganawa tsakaninsu da
gwamnati, amma gwamnati ta sa
aka kama daya daga cikin 'ya'yan
kungiyar Abu Darda wanda suka
tura ya wakilce su.
Kuma tun daga lokacin suka ga
cewa ba za su iya sake amincewa
da gwmanatin Najeriya ba.
Sai dai sakamakon rokonsu da wasu
muhimman 'yan Najeriya da suke
matukar girmamawa suka yi, sun
amince su tattauna, amma abin
kaico ne ganin an bata shirin tun bai
je ko ina ba.
A don haka Abu Qaqa ya ce ba za su
kara saurarar duk wasu da suka ce
su zo su sasanta su da gwamnati ba,
don haka jami'an tsaron gwamnati
su yi duk abinda suka ga za su iya,
su ma za su maida martani da tasu
iyawar.
Dangane da wani dan jarida da ya
yi ikirarin ana barazana ga rayuwar
sa kuwa, mai magana da yawun
kungiyar ta Boko haram ya ce, dan
jaridar shi ne silar hada su da
kwamitin Dr Datti Ahmed, a don
haka suna shawartarsa da sauran
'yan jaridu da kada su razana da
duk wata barzana.
A karshen makon da ya gabata ne
shugaban Majalisar kula da
al'amuran shari'ar musulunci a
Najeriya Dr Datti Ahmad ya fitar da
wata sanarwar da a cikinta ya ce ya
janye daga tattaunawar da suke
kokarin kullawa tsakanin gwamnati
da kungiyar Boko Haram, saboda in
ji shi, suna zargin bangaren
gwamnati da tseguntawa 'yan
jaridu batutuwan da ake tattaunawa
cikin sirri.
Daga shafin BBC Hausa
No comments:
Post a Comment