Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Tuesday, March 27, 2012
Mulkin Soja Ya Fi Na Farar Hula Cancanta Da Amfani Ga Nijeriya
MULKIN SOJA - Mulki ne da wasu daga cikin rundunar sojoji ke kwatar sa da karfin bindiga, sannan suna shimfida mulkin nasu ta yadda suka ga dama ba tare da bada damar fadin albarkacin baki ga wadanda suke mulka. Soja na gudanar da mulkin sa ba tare da kundin tsarin mulki ba, babu wakilci jama'a a cikin gwamnatinsa.
MULKI FARAR HULA - Mulki ne da jama'a ke zaben mutumin da zai jagorance su, sannan akwai damar fadin albarkacin baki, mulkin farar hula na tafiya tare da ra'ayin wadanda ake mulka. Akwai kundin tsarin mulki a mulkin, sannan da wakilan jama'a ake gudanar da mulkin.
Kasar Nijeriya wadda ta samu 'yancin kai daga turawan Burtaniya a shekarar 1960, tayi amfani da duk irin wannan tsarin mulki guda biyu, wato mulkin na soja dana farar hula.
Na dade ina yiwa kai na tambayar tun da Nijeriya tayi amfani da duk wadannan tsarukan mulki to "Shin tsakanin Mulkin Sojan dana Farar Hula wanne ya fi cancanta ga Nijeriya, kuma wanne ya fi amfanarmu a matsayinmu na 'yan kasar" amsar dana ke baiwa kai a duk lokacin dana yiwa kai na irin wannan tambayar itace "Mulkin Soja" to amma ba na gamsuwa da wannan amsa ba don komai ba sai don ban san mulkin soja sosai kamar yadda na san mulkin farar hula ba.
Wannan dalili ya sa na fara hada 'yar majalisar tattaunawa tsakanin 'yan ajinmu lokaci lokaci a makaranta, amma abin mamaki a duk karshen kowace tattaunawa sakamako na nuna Mulkin Soja ya fi cancanta, amma dai duk da haka zuciyar tawa ta taki yarda da hakan, saboda mafi yawan wadanda muke tattaunawar dasu, su ma ba su yiwa mulkin sojan kyakkyawan sani ba.
Daga karshe na yanke shawarar rubuta wannan tambaya a shafin sada zumunta na Facebook, saboda sanin wannan ce hanya kadai da zan samu gamsasshiyar amsar tambayata, domin kuwa shafin na Facebook ba irin mutanen da bai tattara ba. A yammacin ranar 27/03/2012 na rubuta wannan tambaya a shafin wannan Dandali da ke shafin na Facebook da kuma wasu majalisu na tattaunawa (Groups ) duk a shafin na Facebook, cikin abinda bai fi sa'a (awa/hour) daya ba mutane sama da 100 suka mai da martani akan wannan tambaya tawa.
A sakamakon dana tattara bayan wani dan lokaci ya nuna fiye da kaso tamanin da biyar cikin dari (85%) duk amsar da suka bada daidai ce da wadda na dade ina bawa kai na da kuma wadda 'yan ajinmu suka dade suna fada min. Wato Mulkin Soja ya fi Mulkin Farar Hula.
Dalilan da mafiya yawa daga cikin wadanda suka bayyana cewa mulkin soja ya fi na farar hula shi ne sun ce a mulkin soja an fi samun ingantaccen tsaro, ba a samun yawaitar fashi da makami, ba tashe - tashen hankula, ba tashin bama - bamai, sannan an fi samun wutar lantarki, kayan masarufi sun fi araha, rayuwa ta fi sauki ga talakawa, akwai wadataccen man fetur a gidajen mayuka akan kudi mai rahusa.
A daya bangaren kuma kasa da kaso sha da biyar (15%) din da suka bayyana cewa mulkin farar hula ya fi na soja, sun bayyana hakan ne saboda dalilin akwai damar fadin albarkacin baki a mulkin farar hula, wanda kuwa a mulkin soja babu wannan dama kwata - kwata. Har ma wani bawan Allah yake cewa ai a wannan tattaunawar da muke yi ma na daya daga cikin amfanin mulkin farar hula, wanda da mulkin soja ne bamu isa muyi hakan ba.
To a karshe koma dai taya ya ne, akwai gagarumin kalubale ga shugabannin farar hula dake jan ragamar mulkin kasar nan a halin yanzu, saboda da shugabannin farar hular suna gudanar da mulkin su kamar yadda yake a tsarin kundin mulkin kasar nan to da na san ko kusa ko alama mutane ba zasu ke bayyana cewa mulkin soja ya fi na farar hula cancanta da amfanarsu ba.
Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020
No comments:
Post a Comment