Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Tuesday, January 31, 2012
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Matasan Arewa
Aminci a gare ku ya ku matasan yankin Arewa!
A matsayina na daya daga cikinku zanyi amfani da wannan dama na tunatar damu wasu muhimman abubuwa da suke hakki ne a gare mu amma muke yin sakaki da su. Sanin kowa ne cewa matasa sune kashin bayan kowace al'umma, domin kuwa sune iyaye kuma shugabannin gobe. Haka ne ma yasa masana masu hangen nesa suka ce duk al'ummar da matasanta suka hada kansu suka zama tsintsiya mai madauri guda, to wannan al'umma nan gaba za ta zama ja gaba a kowane irin fanni na rayuwa, ta kuma yi wa sauran al'ummomin zamanin fin-cin-kau.
Ya ku matasa Arewa! Wai shin ina muka dosa ne? Shin bama ganin yadda wannan yanki namu ke cikin wani hali na rashin kulawa ne? Shin wane irin mataki muka dauka ko muke shirin dauka akan wannan hali?
Matasan Arewa bai kamata mu koma gefe muna ganin laifin shugabanni, sarakuna, malamai da manyan Arewa kadai ba, duk wani abu na rashin dadi daya faru sai mu dora musu laifi muna fadin ba sa kishin Arewa. Zahirin gaskiya wannan ba daidai bane, kuma ban yarda wadannan jagororin Arewa sune ke da laifi kadai ba, idan har suna da laifi to muma muna da namu laifin. Saboda kuwa idan manya sun kasa mai zai sa mu kuma muyi shiru mu kasa cewa komai?
Misali a matsayinmu na shugabannin gobe wane irin shiri mukayi don daukar wannan nauyi? Shin mun san tun lokacin da Sardauna, Tafawa Balewa da Aminu Kano suka fara gwagwarmaya? Idan muka koma tarihi zamu ga sun fara gwagwarmaya akan Arewa tun suna da karancin shekarun da basu fi 20 zuwa 30 ba. To mu fa yaushe zamu fara? A matsayinmu na masu ikirarin kishin na Arewa.
Zan dan yi wasu tambayoyi ga 'yan uwana matasan Arewa, wadandan tambayoyi sun dade suna zirga zirga da kai kawo a cikin zuciyata, amma kuma har yanzu na kasa samun koda amsar tambaya daya daga cikin tambayoyin. Fatan daga yau zan samu dukkan amsoshin wannan tambayoyi.
TAMBAYOYIN SUNE
Shin a matsayinmu na matasa masu so da kishin Arewa wace irin gudunmawa muka bada wurin ganin burin marigayi tsohon shugaban Kano Umar Musa Yar'adua ya cika na zuwan teku Arewa?
Shin a lokacin babban zaben daya gabata wace irin rawa muka taka wurin fitar da dan takara guda daya kwakkwara daga yankin Arewa?
Shin wane irin kokari muke yi ganin dawo da zaman lafiya a Arewa kamar yadda muke a shekarun baya?
Shin an ya kuwa akwai wani shiri da muke yi na ganin samun hadin kai da soyayyar juna a tsakanin kabilu da addinan wannan yanki na Arewa a matsayinmu na jagororin kishin Arewa?
Akwai tambayoyi makamantan wannan masu dumbun yawa dake kunshe a zuciyata wadda na tabbar ku ma ba za'a rasa irinsu a zuciyoyinku ba. Fatanmu mu hada hannu mu samarwa kanmu amsoshin wadannan tambayoyi.
Sai tambayata ta karshe, shin tawa ne hali zamu kawowa kanmu mafita? Amma saboda saukin wannan tambaya zanyi kirinkin bada amsarta. Amsar tambayar itace mu matasa mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinmu daya, bayan haka kuma mu zama masu kishi da soyayyar yankinmu. Sannan mu zama masu magana da harshe guda, wato idan matashin jihar Adamawa yace eh, to idan aka samu na jihar Kwara ma yace eh. Hakan kuwa zaiyi wahala har sai munyi wata kungiya da zata tattaro dukkan matasan Arewa ta dunkule mu wuri guda. Yin hakan ne kadai muryarmu zata ke isa inda muke so da bukatar taje, sannan hakan ne zai sa asan muhimmancimu, ta haka ne kadai zamu samu damar kare 'yancinmu da mutuncimu.
A karshe nayi amfani da wannan dama ne don na isar da wannan sako ga duk wani matashi wannan wasika, saboda sanin wannan ce hanya kadai da zan aika sakon nawa kuma ya isa zuwa wurin wadanda na aika dominsu. Fatan duk wanda ya karanta wannan wasika zai aikawa sauran abokansa ta haka ne zata samu isa zuwa ga duk wani matashi mai kishin Arewa.
Sannan zanyi kokarin ganin an buga wannan wasika a jaridu da mujallu musamman masu amfani da harshenmu na Hausa.
Allah ya daukaka Arewa, Allah ya daukaka kasarmu Nigeria!
Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160
Gaskiya Bashir kayi kokari kuma ka tabowa inda yakewa mafiya yawan yan Arewa kankayi. Fatan tunda ka fadi mafita za muyi amfani da ita wato mu bude wata babbar kungiya da zata ke magana da yawun matasan Arewa. Allah ya taimake mu!
ReplyDeleteGaskiya idan son Arewan da muke gaskiya ne ya kamata a wannan lokacin muyi wani abu. Lokaci yayi da zamu tashi domin yancinmu.
ReplyDeleteKalubalen dake gaban Matasa kenan. Malam Bashir Allah ya saka da mafificin Alkhairi.
ReplyDeleteWell done bashir
ReplyDeleteDazaka yi attaching na differences( sun an jaridar da page no. Ko audio) to natabbatar zaka ja hankalin duk mai hankali
I meant refference not difference
Delete