Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Tuesday, April 6, 2010
ALHAJI (DR) MUHAMMAD ABUBAKAR RIMI
Inna lillahi wa inna illahi raji'un.
A dare ranar Lahadi 4 April 2010 ne, Allah (S.W.A.) yayi wa Alhaji (Dr.) Muhammad Abubakar Rimi tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano (Kano da Jigawa) rasuwa.
Akan hanyar sa daga jihar Bauchi zuwa Jihar Kano, bayan ya dawo daga bikin nadin sarautar gargajiya ya hadu da yan fashi a tsakanin garin Garko da Wudil. Duk da yan fashin basu taba shi ba amma za'a iya cewa sune sanadiyar mutuwar sa.
Bayan yan fashin sun karbe musu kudin su da wayoyin su, sannan suka taho kafin suzo Wudil Muhammad Abubakar Rimi ya gamu da bugun zuciya, nan take aka kai shi asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Wajen karfe 11:40 na dare Allah ya karbi ransa.
Washe garin ranar da ya rasu akayi jana'izar sa, a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
Jana'izar Muhammad Abubakar Rimi ta samu halartar mutane sama da mutum miliyan daya daga sassa daban-daban na kasar Nigeria baki daya.
TAKAITACCEN TARIHIN ALHAJI MUHAMMAD ABUBAKAR RIMI
An haifi Muhammad Abubakar Rimi a kauyen Rimi na karamar hukumar Sumaila, jihar Kano, Nigeria. A shekarar 1940.
Alhaji Abubakar Rimi na daya daga cikin manya-manyan fiatattun kuma jiga-jigan yan siyasar nahiyar Afrika. Yayi karatun sa na Kos a Zaria, kuma ya samu takardar shedar zuwa jami'ar London, kasar England a 1972. Ya hada diflomar sa a kasar kuma ya samu shedar babban digri.
Rimi yana daga cikin mutanen da suka kirkiri jam'iyyar PRP a shekarar 1978 kuma an zabe shi a matsayin mataimakin jam'iyyar na kasa a taron ta na farko a jihar Lagos.
Abubakar Rimi an zabe shi a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Kano a October 1979 har zuwa May 1983 kuma shine gwamnan farar hula na farko a jihar. A farko 1983 Rimi ya fita daga jam'iyyar PRP ya koma Nigerian People's Party (NPP).
A lokacin mulki Rimi yayi wa jama'ar jihar Kano da Jigawa aikin da wani gwamna bai taba yi ba.
Muhammad Abubakar Rimi shi ya gina gidan jaridar jihar Kano Triumph, ya gina gidan television na CTV Kano, ya gina Kasco da kuma Knarda.
Rimi a lokacin mulkin sa ne ya kirkiro sabbin masarautu na sarakunan yanka. Kamarsu: Kano, Gaya, Rano, Karaye, Auyo da Ringim.
A 1993 Rimi ya zama ministan yada labarai sannan ya zama shugaban NACB da NSPMC. yana cikin mutanen da suka samar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Rimi ya fita daga Jam'iyyar PDP a 2006 ya koma jam'iyyar Action Congress (AC) amma a 2007 Rimi ya sake komawa PDP.
A january 2006 wasu yan ta'adda suka shiga gidansa suka kashe masa matar sa Sa'adat Abubakar Rimi.
Ranar 4 April 2010 ya rasu a asibitin Mallam Aminu Kano. An bunne shi ranar 5 April 2010 kamar yadda Addinin Musulunci ya ta nada.
A karshe Allah ya jikansa, Allah ya kai rahma kabarin sa, Ya saka masa da gidan Aljanna firdausi. Ya baiwa iyalansa hakurin jurewa.
Allah yajikansa da rahama amin.
ReplyDeleteAllah ya gafarta masa. Kuma wani abu da na lura da shi shine ba kasafai akan sami lakcocinsa na sauti da na bidiyo a intanet ba. Da fatan za a sami wadanda za su dau naiyin yin hakan
ReplyDelete