Thursday, November 24, 2011

HALIN BABBAN YARO (ABBA MUHAMMAD SAVIOLA)

Abba Muhammad Saviola, abokina ne kuma aminina ne. Allah ya hore masa iya sarrafa zance gami da mai dashi yayi dadi, wannan tasa yake jan hankalin 'yan mata da zarar ya samu damar magana dasu, wannan dalili yasa yake yiwa kansa kirari/lakabi da cewa ABBAN MAI RABO, wato duk macen da ta same shi a matsayin mijinta to itace mai rabon.

Abba babban yaro ne, wadda kalmar babban yaro a yaren samari da 'yan mata na nufin wani dan saurari kyakkyawa da yake da fafa da ji da kansa, ta bangaren iya mu'amala da ta shafi zamantakewa a tsakanin samari da 'yan mata.

Wata rana Saviola ya tashi da sanyin safiya aljihunsa babu ko kobo gashi a matsayinsa na babban yaro shi kansa ya tabbatarwa kansa ba girmansa bane ya fito yana fadin bashi da kudi. Babban tunaninsa a lokacin yadda zai samu kudin da zaiyi transpot daga hostel zuwa school, domin kuwa wannan yafi damuwa dashi ba ciki ba.

Can yana cikin wannan hali sai yaji karar shigowar sakon text a wayarsa dake cikin aljihu, yana duba sakon sai yaga sako ne daga banki ana sanar dashi an aiko masa da kudi a account dinshi. Nan take yayi wani bushasshen murmushi tare da tashi tsaye, anan ya fara tunanin yadda za'ayi aje bankin don dauko kudin, domin kuwa babu kudin da za'aje bankin dasu. A karshe ya yanke shawarar tafiya a kafa.

Isar sa bankin ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa son kowa kin Bashir Ahmad, tunda kuwa ya rasa, ta fito daga bankin. Abba komai girman budurwa bata bashi tsoron yi mata magana, kuma da zarar ta bashi dama to kuwa ya gama da ita. Kamar yadda na fada a baya. Hakan tasa bai nuna tsoro ko shakka ba, ya tunkari wannan budurwa tare da yi mata tambaya "Gimbiya don Allah nan ne Zenith Bank?" tayi murmushi ta amsa masa "eh nan ne" saboda kuwa tasan ba wannan magana ce a zuciyarshi ba, kawai dai yayi tambayan nan don ya samu daman magana da ita.

Da bashi amsa bata tsaya karin bayani ba sai tayi gaba, shi kuwa Abba maimakon ya shiga bankin tunda ya samu amsar tambayarsa, sai shi ma kawai yabi bayanta, da ta fuskanci ya biyo bayanta sai ta tsaya tace "Malam ko akwai wata tambayan ne"

Na takaice muku bayani dai, tuni Abba ya sanar da ita abin dake zuciyarshi, har ma yana kokarin karban phone number ta, sai anan ya tuna saboda farin cikin turo masa kudi da akayi a lokacin da yake bukatansu, ya bar phone din nashi a hostel. Aka kuma nemi takardar da za'a rubuta number ba'a samu ba, kawai sai yarinyar ta bude jakarta (Hand Bag) ta dauko sabuwar N1000, ta rubuta masa number a gefe.

Karka manta da cewa Abba babban yaro ne, mai son nuna isa da fafa. Sannan kuma ka tuna tashin da yayi a ranan ba tare da ko sisi ba. Da karbar wannan sabuwar one thousand maimakon ya jefa ta a aljihu sai kawai ya yage gefen da aka rubuta number, sauran kuma ya rinka yayyagawa yana wasa da su lokacin da suke tafiya da yarinyar zai rakata wurin da tayi packing din motarta.

Lalle Abba ya cika babban yaro, wannan abu da Abban yayi ba karamin kara burge tsaleliyar budurwar yayi ba, gami da kara sace sauran zuciyarta gaba daya. Bayan ta shiga mota sukayi sallama da alkawarin zai kirata da zarar ya koma hostel.

To fa, a karshe da Saviola ya shiga banki don amsar kudin da aka turo masa sai jami'an bankin suka tabbatar masa da cewa ai an samu matsala ne ba account dinsa akayi niyyar turo kudin ba, saboda haka ma tuni wanda ya turo kudin ya debe abinsa. Da farko har Abba ya bata rai, sai kuma ya tuno irin barazanar da yayi wa kyakkyawar budurwan nan kawai sai yaji farin ciki ya mamaye shi, har ma ya samu damar komawa hostel cikin kwarin gwiwa.

Kaji kadan daga cikin halayen manyan yaro.

A karshe ina jinjina ga babban yaro, Abban mai rabo kuma madugu uban tafiyar shafin DAUSAYIN MASOYA a shafin sada zumunta na Facebook.

NB: It is not true life story, it is just for joke.


Bashir Ahmad
bashirahmad29@yahoo,com
08032493020, 08050600160

Wednesday, October 26, 2011

JAMILAH TANGAZA: Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram

JAMILAH TANGAZA: Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram: Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akai. Dalili kuwa shine suna ganin muddin suka yi magana watakila ‘yan Bo...

Sunday, October 23, 2011

Ka Zama Mai Yunwar Ilimi, Ka Zama Mai Budaddiyar Zuciya - Steve Job

"Babu mai son ya mutu. Hatta wadanda ke ganin sun yi aikin kwarai ba su cika son su mutu ba, sai dole. Amma kuma babu
makawa, mutuwa ce masaukin da za ta tattaro mu duka. Babu wanda ya taba guje wa mutuwa
a baya. (Kuma babu wanda zai guje mata a gaba) haka lamarin ya kamata ya zama. Domin mutuwa ce abin da har zuwa yau duniya ba ta taba samar da irinta ba. Ita ce abin da ke kawo canji a rayuwa. Ita ce ke share tsohuwar al’umma don kawo sabuwa. A halin yanzu da nake muku wannan jawabi, ku ne sabuwar al’umma, amma nan ba da dadewa ba, watarana za ku zama tsohuwar al’umma, an share ku don kawo wata sabuwar ta maye gurbinku. Ku yi mini afuwa idan wannan
zance nawa ya firgita ku, amma wannan ita ce hakikanin gaskiya.

Rayuwarku ‘yan kwanaki ne takaitattu, don haka kada ku shagala wajen kwaikwayon rayuwar wani. Kada ku zama
‘yan abi yarima a sha kida. Kada ku yarda surutan wasu su hana ku bin shawarar da za ta fisshe ku a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne, ku zama masu juriya wajen bin abin da zai zama maslaha a rayuwarku da fahimtarku. Domin su ne kadai suka fi kowa sanin abin da kuke son ku zama. Duk wani abin da ba wannan ba, to, ya zo a bayanshi".

Wannan wani gutsuren jawabi ne, daga cikin wani dogon jawabi da marigayi Steve Job, shugaban Kamfarin kera kayayyakin sadarwa na Apple Inc., ya gabatar a ranar bikin yaye dalibai na Jami'ar Stanford "STANFORD COMMENCEMENT ADDRESS" a watan June na shekarar 2005.

Inda a karshen jawabin nasa ya kara da cewa "Ka zama mai yunwar ilimi. Ka zama mai budaddiyar zuciya. Kuma a kullum nakan yi wa kaina wannan fata. Don haka na ga dacewar yi muku wannan fata ku ma, a daidai wannan lokaci da kuke kokarin fara wata sabuwar rayuwa bayan barin Jami'a, cewa: "Ku zama masu yunwar ilmi a kullum. Ku zama masu budaddiya zuciya wajen karbar fahimta" Nagode matuka!!!

Saturday, October 22, 2011

Tafiya Mabudin Ilimi (Bashir Ahmad a Sokoto Birnin Shehu)

Gaskiyar Hausawa da suka ce "Tafiya Mabudin Ilimi" duk da na yarda da hakan, amma ban gama tabbatarwa ba, ko nace ban taba jarrabawa ba, sai lokacin da nayi tafiya daga Kano zuwa Sokoto. Taron kungiyar Dandalin Siyasa e-Forum, karo na 3, Tafiyar da ban tabayin mai nisanta ba, a tarihin rayuwata, sai dai kuma nan gaba idan Mai duka ya barmu da rai da kuma lafiya.

Wannan tafiya tawa, mai kunshe da kalubale, alfahari, ilimi gami da abubuwan al'ajabi, nayi tane ranar 14 October zuwa 16 October 2011. Tabbas wannan tafiya ko shakka babu, ta shiga cikin tafiyoyin da bazan taba mantawa dasu ba (Unforgetable Journey).

Da farko a ranar tafiyar na tashi daga bacci tun da sanyi safiya na fara shirye shirye, kamar mai barin kasar kwata kwata. Na fito daga gida misalin 7:56am ba tare dana kammala 'yan shirye shirye na ba, saboda ina tsoron kar mota ta tashi ta barni, kamar yadda aka tabbatar min za'a hadu 7:30am a tashi zuwa birnin Shehu 8:00am.

Na isa kofar shiga tsohuwar Jami'ar Bayero, inda za'a hadu, amma saboda Nigerian Time da wani bawan Allah yayi bamu tafi ba sai 9:00am. Abinka da sabon shiga, fara tafiyar ke da wuya na dakko mujallar MURYAR AREWA na fara karantawa don kar ko gyangyadi ya dauki ni a shige wani wuri ba tare dana kashe kwarkwatar idona ba. Bayan na gaji da karatun jaridar sai na dauki wayata, na shiga shafin sada zumunta na Facebook na rinka sanarwa da yan uwa da abokanan arziki halin da tafiyar tamu ke ciki. Su kuma suna taya mu adduar fatan alheri gami da sauka lafiya.

Can da tafiya tayi tafiya sai wayar ma na hullata a aljihu, nayi zuru na zubawa sarautar Allah ido, wato dai na gaji kenan amma saboda tsegumi irin nawa, ko kadan ban nuna gajiyar ba, balle na kishin gida har bacci ya samu damar kwashe ni.

Nasan masu karatu ku kanku kunsan a wannan tafiya idanuwa na sun sha kallon abubuwan da ba sai na tsaya ina bata bakina wurin lissafa muku su ba, kai zahirin gaskiya ma dai idan nace zan lissafo zan iya yi muku ragi, don haka zan fadi wasu abubuwa guda biyu zuwa uku da suka fi daukar hankalina. Na farko naga shimfida shimfidan tituna amma ba motocin yawatawa akansu a jihar Katsina. Na biyu naga wani rusheshen dutse a jihar Zamfara, wanda idan mutum ya nemi kallo tsayinsa to tabbas hular zata fadi kasa ba tare da ya sani ba. Abu na uku shine karamcin da Sakkwawa sukayi mana, wanda bazan taba mantawa ba.

A takaice dai bamu isa cikin birnin Shehun ba, sai misalin 3:36pm, kai tsaye aka wuce damu, Sokoto Guest Inn, wanda shine masaukinmu. Kai mutane Sokoto akwai iya karbar baki sai kace wadanda suka zo Kano suka dauki darasi, domin kuwa da isarmu ba abinda suka tarye mu dashi sai wani daddadan kilishi hade da sassanyan lemo. Kasan Bakano bai da filako nan take muka tashi da wannan hidima.

Misalin 9:30pm na wannan rana, aka debe mu cikin zungureriyar mota, zuwa wurin wani shakatawa mai suna Daddy's Smart dake cikin birnin na Shehu, domin gabatar da Cultural Night wanda kungiyar ta Dandalin Siyasa ta shiryawa 'yayanta domin debe kewa. A wannan wurin na sha dariyar da tayi kusan sa cikina ciwo, domin kuwa tsohon dan wasan Hausan nan na barkwanci Golobo (Boloko) shine ya cashe tare da jama'arsa.

Washe gari ranar 15 October, ranar da aka ware don yin taron, mun tashi mun shirya, sannan muka nufi wurin da za'a gabatar da taron a dakin taro na makarantar koyon karatun Al Kur'ani da Kimiyya na Muhammad Maccido, amma kafin a fara gabatar da laccocin da za'a gabatar sai da aka kai ziyarar girmama fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III. Bayan an dawo daga fada sai aka koma wurin taron.

An gabatar da laccoci a wurin taro wadanda suka shafi halin da kasarmu Nigeria ke ciki a halin yanzu, kamar irinsu TABARBAREWAR TSARO, ILIMIN BOKO, sai kuma DEMOCRADIYA wanda Prof. S. A. Yakasai na jami'ar Shehu Usman Danfodio da kuma Dr. Usman Muhammad na jami'ar Birnin Tarayya Abuja suka gabatar.

An kammala taro misalin 3:30pm, daga nan bayan an gabatar da sallar La'asar sai kuma aka tafi kai wata ziyarar girmamar gidan Alhaji Abubakar Alhaji (Alhaji Alhaji) Sardaunan Sokoto na yanzu, dattijon arziki, namiji uban masu kudi da 'yan boko. An gabatar masa da kungiya, ya kuma yi farin ciki gami da karfafa gwiwa.

Sai kuma wajen 9:30pm aka tafi wurin dinner a Mr Bigs wanda aka kai har zuwa 11:30pm daga nan kowa ya tafi masaukinsa. Kuma wannan shine abu na karshe da aka shirya gabatarwa a taron.

Washe gari ranar 16 October rana ce da duk wanda yaje birnin na Shehu zai waiwayi inda ya fito, a ranar ne muma da misalin 9:30am muka kama hanyarmu ta dawo gida Kanon Dado mai mata mai mota mai Dala da Goron Dutse.

A karshe ina kara mika godiyata ga dukkan SAKKWATAWA wadanda suka dauki dawainiyarmu tunda muka je har muka dawo gida. Allah yasa da alheri, Allah ya kara hada fuskokinmu da alheri, ameen!

Wednesday, October 12, 2011

Ibada ko Siyasa? Sunan Kwankwasiyya a Gidan Alhazan jihar Kano a birnin Makkah

Hausawa suka ce wai "Sabon salo kidan ganga da lauje" kullum siyasar kasar nan sai zama take yi gara jiya da yau, misali idan yau wannan mai mulki wa'adinsa ya kare wani kuma ya karba, sai kaga talakawa na murnar an samu canji, amma da zarar wanda ya hau an fara ganin rikon ludayinsa sai kaji talakawan sun dawo suna fadin ai gara na jiya dana yau. Ko me ke kawo haka oho. Ko kuma mu duk haka muke Nigeria ba'a zuciyarmu take ba, bama son canji da ci gabanta, mun fiso mu zauna kurar baya kodayaushe, Allahu a'alamu.

Ba komai ne ya sanin fadin hakan ba, sai ganin yadda masu mulki ke wuju - wuju da shafawa talakawa jan baki, ba tare da suna sara suna duban bakin ga tarinsu ba. Anan zanyi misali da siyasarmu ta jihar Kano, wadda masu iya magana ke yiwa lakabi da "Siyasar Kano Sai dan Kano" A lokacin da tsohon gwamna, wadda ya mayarwa da sabon gwamna dake kan karagar mulkin jihar yanzu, bana mantawa duk lokacin daya gudanar da wani sabon abu musamman a bangaren addini, sai kaji ana kiran wai ai fakewa yake da addini yana wawashe kudaden talakawa.

To sai gashi yanzu bayan shudewar tsohuwar gwamnatin, masu shafa jan baki da jar hula suka cigaba da jan ragamar gwamnatin, sai suma suka shigo da sabon salo kala - kala. Wanda duk abin dake faruwa ba wanda ya bani mamaki kamar wannan. Abin mamaki shine kuwa yadda itama sabuwar gwamnatin ke neman aron mayafin tsohuwar gwamnatin ta yafa, wato itama ta fake da addinini ta wawashe kudaden talakawa. Domin kuwa hatta a bangaren aikin Hajjin bana ma sai da gwamnatin tasa siyasa a ciki. Saboda a gidan da alhazan jihar Kano ke yada zango a birnin Makkah sai da aka rubuta KWANKWASIYYA HOUSE da baro - baron rubutu yadda ko makaho ya shafa zai ji alama. Ba a iya nan sabuwar gwamnatin ta cuso harkokin siyasa ba, bangaren aikin Hisbah da kwamitin Shari'a ma duk haka abin yake.

A karshe ba ina kare wani bangare bane, ko goyan baya tsakani wadannan gwamnatotin biyu, kawai ina son na aika wani sakona ne zuwa ga wadanda abin ya shafa don susan tuni mun gane duk wani shiri da suke yi don wawashe dukiyar talakawa.
Fatanmu Allah ya bawa wannan sabuwar gwamnati ta masu jar hula karin gwiwar yi mana aiki da kawowa jiharmu ci gaba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020