Thursday, March 5, 2015

RAHOTO: Hasashen Yadda Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Zai Kasance

Daga Ahmad Abubakar, Abuja

Cikin wannan rahoton da editan #HAUSA24 na harkokin siyasa ya hada mana, ya yi duba kan yadda ake tsammanin sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Maris zai kasance, idan an gudanar da zaben ba tare da aringizon kuri'u ko magudi ba.

Adadin Masu Rijistar Zabe Ta Dindindin A Yankunan Kasar Nan

Kudu Maso Yamma - 13,731,090

Kudu Maso Gabas - 7,665,859

Kudu Maso Kudu - 10,059,347

Arewa Maso Yamma - 17,620,436

Arewa Maso Gabas - 9,107,861

Arewa Ta Tsakiya - 9,767,411

FCT Abuja - 903,613

Hasashen Yadda Sakamakon Zai Kasance

Kudu Maso Yamma - GMB 65%, GEJ 35%

Kudu Maso Gabas - GMB 20%, GEJ 80%

Kudu Maso Kudu - GMB 20%, GEJ 80%

Arewa Maso Yamma - GMB 90%, GEJ 10%

Arewa Ta Tsakiya - GMB 60%, GEJ 40%

Arewa Maso Gabas - GMB 70%, GEJ 30%

FCT - GMB 40%, GEJ 60%

A karshe lissafin zai nuna Buhari zai samu kaso 365%, yayin da Jonathan zai samu kaso 335%.

A LURA: lissafin ba yana nufin na adadin yawan kuri'un da Buhari ko Jonathan za su samu ba ne, lissafin na nufin kason da ake hasashen kowanne su zai samu a yankunan kasar nan guda shida da birnin tarayya Abuja.

Sunday, February 22, 2015

GARABASA DAGA mACADEMY

Ilimintar da kanka, bunkasa takardun kwarewarka (CV) sannan ka samu damar cin kyauta.

mAcademy, wata hanyar koyo ce ta hanyar amfani da wayoyin hannu, mAcademy na bada damar koyar samu da darussa 150 kuma mafi yawancin su duk a kyauta. Burin wannan makaranta ne su ilimintar da al'umma musamman marasa galihu, tana da hadin guiwa da kamfanin sadarwa na MTN da kafar yada labarai ta Sahara Reporters, sannan nan gaba kadan da yardar Allah, za ta kulla dangantaka da wannan kafar yada labarai #HAUSA24.

mAcademy, tana bada damar koyo cikin yarukan Turanci, Larabci da kuma Hausa, tana ayyukan ta a sama da kasashe biyar a nahiyar Afrika.

Aika ACADEMY zuwa 131 ko duba wannan hoton don ganin yadda za ku shiga gasar, da yadda za a fitar da wadanda suka yi nasara, ba wannan ce gasa ta farko da mAcademy din ta saka ba, a baya ta sa irin wannan gasa kuma mutane da dama sun samu nasara.

Cancantar shiga gasar:

- Idan kana daya daga cikin wadanda suka taba lashe kyauta daga mAcademy watanni shida baya, ba zaka iya shiga gasar a wannan lokaci ba, jira wani lokacin nan gaba.

- Idan ka shiga gasar, ya zama dole ka aika/raba rubutun shiga gasar zuwa ga sauran abokanka daga shafin Facebook na mAcademy (www.facebook.com/bilyak).

- Gasar za ta kare ranar 13, ga watan Maris, 2015.

...Ka shirya? Shiga gasar yanzu don gwada sa'arka.

HAUSA24 za ta yi alfahari idan aka samu daya daga cikin makarantan ta ya lashe gasar, muna yi muku fatan alheri.

A LURA CEWA: Kamfanin Bilyak Consulting Limited ne ya dauki nauyin gasar ba MTN ba.

Tuesday, February 10, 2015

HOTO: Sarkin Kano, Sanusi Da Iyalansa



Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, tare da matansa uku da 'yaya 12. Wannan shi ne hoto na farko da Sarkin ya dauka da iyalansa baki daya, tun baya bikin bashi sandar girma da ya gudana a ranar Asabar 7 ga Fabrairu, 2015.

Allah ya taya Mai Martaba riko!

Thursday, February 5, 2015

AREWA MUN FARKA DAGA BACCI: Jonathan Ya Sa Mun Fara Hada Kan Mu

Masha Allah, yanzu kam zan iya cewa watakila Arewa mun farka daga dogon baccin da muka dade muna yi.

Sakamakon zaman majalisar zartarwa na kasa da aka kammala dazu ya kara min karfin guiwa kan lalle Arewa wannan karon da gaske muke yi.

Kamar yadda wani da yake da masaniyar yadda zaman majalisar ya gudana yake shaida min a waya yanzu, ya ce bayan Jega ya tashi yayi jawabinsa a gaban majalisar, inda ya bayyana cewa INEC ta shirya gudanar da zabe a ranakun 14 da 28 na watan nan, gwamnatin tarayya da 'yan kanzaginta sun nemi kin amincewa da hakan, sai dai gwamnonin APC su 14 da suka halarci taron, da Janar Buhari da kuma Hon. Aminu Tambuwal duk sun goyi bayan maganar ta Jega.

Haka kuma wasu daga cikin gwamnonin PDP daga yankin Arewa su ma sun nuna goyon bayan su ga Jegan, abinda ba a yi tsammanin hakan daga wurin su ba.

Da na nemi ya fada min wadanne gwamnoni ne daga Arewa sai yace na bari na karanta a jarida idan labarin ya fita, amma akwai gwamnan jihar J... da kuma B... haka kawai ya fada min bai karasa min sunan ba.

Yanzu dai zabe zai gudana a ranar 14 da 28, zabi ya rage gare mu, ya zama dole mu fita mu karbi katin zaben mu na dindindin don zaben shugabannin da muke gani za su yi mana abinda za mu zabe su don su.

...Ni dai na yake shawara tuntuni, a zaben shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari, na jam'iyyar APC zan zaba kamar yadda na saba, zabensa tun daga 2003.

Tuesday, January 6, 2015

Kungiyar Tsagerun Neja-Delta Sun Bayyana Goyon Bayan Su Ga Buhari

...Jonathan Ya Sake Shiga Tsaka Mai Wuya

Yayin da zaben 2015 ke kara kusantowa, shugaba Goodluck Johnathan dake neman tazarce a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP na kara shiga tsaka mai wuya, yayin da a kullum yunkurin na sa ke kara samun koma baya.

Babban kungiyar 'yan tawayen Neja-Delta, wato MEND a yau ta bayyana cikakken goyon bayanta ga takarar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, wanda ba a taba ganin makamancin irin haka a siyasar kasar nan ba. Haka kuma kungiyar ta MEND ta jaddada cewa ko kadan bai cancanci Jonathan din ya ci gaba da mulkin kasar nan ba, duba da irin yadda Nijeriya take ta samun koma-baya a karkashin jagorancinsa wanda suka kira hakan da abin kunya ne ga yankin na su, inda Jonathan ya fito.

MEND cikin wani dogon jawabi da ta aike kafafen yada labaran kasar nan, mai dauke da sa hannun sakataren ta, ta ce ta yanke shawarar goyon bayan Buhari ne don taimakawa wajen kubutar da kasar nan daga halin da ta samu kanta ciki.

Kafin wannan sanarwa ana tsammanin kungiyar ta MEND za su shiga taya Jonathan fafutuka don ganin mulki ya ci gaba da kasancewa a yankin su.

Kungiyar MEND ita ce ta sanya bom a Abuja, a ranar cikar Nijeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai, sai dai a lokacin saboda soyayya, Shugaba Jonathan ya fito ya ce ba su bane duk da sun dauki alhakin kai harin.

Zuwa yanzu dai za a iya cewa Shugaba Jonathan baida wata kwakkwarar makama da zai kama don taimaka masa ya ci gaba da zama a kan karagar mulkin a 2015.