Thursday, March 15, 2012

Na Duke Tsohon Ciniki - Da Arzikin Noman Mutanen Arewa Aka Samar Da Man Fetur A Nigeria


Idan muka dubi can baya lokacin da kasar nan bata da man fetur (fuel) ko nace kafin a tono man fetur, an dauki yankin AREWA da matukar muhimmanci, musamman a wurin shugabannin kasar nan na wancan lokacin. Ba don komai ba sai don da arzikin noman dake yankin ke samarwa kasar NIGERIA ta ke gudanar da komai, da wannan noma ake samun duk wani kudin shi, kai a lokacin Nigeria ta dogara baki daya, da wannan arziki na noma. A wannan lokaci ba rigingimu a Arewa ba BOKO H.... Kan duk wani dan Arewa a hade yake, ba a lakari da addini ko kabila, kowa ya dauki kowa a matsayin dan uwa.

Da wannan arzikin na noma aka yi duk wani wahalhalu na hako man fetur din da muke amfana a yanzu, da shi aka biya ma'aikatan da sukayi wannan gagarumin aiki.
Da shi aka gina matatan man fetur din da muke da su.

Amma wani abin mamaki sai ga shi a wannan lokaci yankin AREWA ne yafi kowanne yanki kaskanci da koma baya a kasar nan, har ma a wani kiyasi da akayi kwanan nan wai yankin ne yafi kowanne TALAUCI da FATARA, saboda yanzu an samu man fetur an yarda noma, an dauki MANOMA wawaye wadanda basu san mai suke yi ba, an dauke su a matsayin jahilai da basu waye ba. Gwamnatin a wancan lokaci tana tattalin Manoma tana samar musu da ingantattu kayan noma kamar su: motocin noma, iri, maganin kwari, takin za
mani da sauransu.

A karshe fatan za muyi karatun ta nutsu don samarwa rayuwarmu da ta 'yayanmu da zamu haifa nan gaba mafita.

Ya Allah ya taimaki AREWA da jama'ar AREWA, Ya Allah ya taimaki NIGERIA.

Bashir Ahmad
Bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Wednesday, March 14, 2012

Wasu Saurari da Budurwa Masoyan Juna Sun Mutu a Lokaci Daya a Cikin Mota


ABIN AL'AJABI - Da sanyin safiyar ranar 14 March, 2012 ne wani abin al'ajabi ya faru a yankin unguwar Kundila dake cikin kwaryar birnin Kano. An samu gawar wasu bayin Allah su biyu, Abubakar Abba da Ummulkhair Muhammad, saurari da budurwa a cikin karamar mota kiran Peugeot 406, mallakin saurayin Abubakar Abba.

Matasan guda biyu, wadanda aka bayyana cewa dukkansu dalibai ne, dake karatu a makarantar Kwalejin Sa'adatu Abubakar Rimi, sannan dukkansu suna kan ganiyar samartakarsu da basu wuce shekaru 25 ba. Kuma sun dade suna son juna, wanda har iyayensu sun shiga maganar soyayyar tasu.

ASP Magaji Majiya, jami'in hulda da Jama'a na hukumar 'yan sandan jihar Kano, ya tabbatar da faruwar wannan al'amari, kuma yace har yanzu ba'a san menene musabbabin rasuwar matasan ba. Sannan ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar 'yan sanda tana kan bincike.

Ya Allah ya jikan wadannan MATASA masoyan juna, ya kai rahma kabarinsu.

Jama'a Ga Jaridar RARIYA Matatar Gaskiya, Domin Samar Da Labaran Gaskiya


Aminci a gare ku! Ya ku al'ummar kasar Nijeriya, musamman Hausawa da kuma masu amfani da harshen. Cike da farin ciki da annashuwa nake gabatar muku da sabuwar jarida mai suna RARIYA wadda ake yi wa lakabi da MATATAR GASKIYA.

Wannan jarida sabuwar fitowa ce da aka samar domin al'umma, kuma zahiri jaridar ta zo a daidai lokacin da al'umma ke bukatarta, ba don komai ba sai don yadda al'amura a kullum suke kara cabewa gami da dagulewa musamman a harkokin yada labarai, sanin kowa ne mafi yawa daga cikin jaridun wannan zamani ba kawo sahihin labarai ne ya dame su ba, abin da suka fi mai da hankali shi ne wane labarai zasu kawowa makaranta ya samu karbuwa su samu riba mai yawa, ko da kuwa ba su da tabbacin sahihancin gaskiyar labarin.

RARIYA ta zo da salo ne na daban da ya sabawa irin na wadannan jaridu na zamani, wannan dalili ya sa ta samu lakabin MATATAR GASKIYA, kafin ta kawowa masu karatu labari sai ta bi diddiginsa sannan ta tato gaskiyarsa ta bayyanawa al'umma. Samuwar RARIYA zai zame wa masu karatu wata wukar gindi, sannan RARIYA ta yi alwashin kawo labaran da zasu inganta rayuwar al'umma, cikin hanya mafi dacewa da yanayin rayuwar zamani. Tabbas RARIYA ta samu ne bisa kishin kasarmu da al'ummarmu a matsayin wata jagora da zata nuna mana mafi ingancin rayuwa tagari abar alfahari.

Jaridar RARIYA na kunshe da bangari daban - daban masu Ilimintarwa, Fadakarwa, Wa'azantarwa, har ma da nishadantarwa. Kadan daga cikin wadannan bangarori sun hada da:

NIJERIYARMU A YAU - wannan bangare ne da yake dauke da muhimman labarai da suka shafi kasar nan baki daya.

MU KEWAYA JIHOHI - daga jin sunan bangaren ba bukatar dogon bayani, bangaren na lekawa jihohin kasar nan 36 da birnin tarayya Abuja, domin zakulowa masu karatu sahihan labarai masu inganci.

DUNIYA LABARI - A wannan bangaren kuma labarai ne kala - kala daga sassan duniya daban - daban, domin sanin wainar da ake toyawa.

BABBAN BAKO - A wannan bangare RARIYA na kurdawa cikin kasar nan ta lalubo wani babban bako masani, domin yin fashin baki akan wasu al'amura da zasu amfani masu karatu da sauran al'ummar kasa baki daya.

KULIYA MANTA SABO - Nan kuma bangare ne daya shafi harkokin shari'ah, domin kawowa masu karatu ingantattun labarai daga bangaren na Shari'ah.

SHAFA LABARI SHUNI - Shafin na kawo labarai na nishadantarwa da fadakarwa, wanda masu karatu ke aikowa da kansu, domin daukar wani darasi.

TASKAR FIM - Bangare ne a cikin jaridar dake kawowa makaranta irin wainar da ake toyawa a masana'antar fina-finan Hausa har ma da takwarorinsu na kudanci kasar nan (Nollywood) dama na sauran kasashen duniya irin su Amurka da India.

YABON GWANI - Bangaren na kawowa masu karatu tarihin wani kwazo, haziki kuma gwani a wani bangare na rayuwa, da irin gudunmawar da ya bawa al'umma.

SIYASA ROMON BAKA - Wannan bangaren kuma dandali ne na 'yan siyasa da magoya bayansu, shafin ya kunshi duk wani batutuwa da suka danganci siyasa.

LIKITA BOKAN TURAI - Nan kuma bangare ne da aka ware domin kiwon lafiya, da bada shawarwari ga makaranta ta yadda zasu kare kawunansu daga cututtuka.

TABA KA LASHE - Bangare ne da Amina Galadanci ke tsakurowa masu karatu dadaden labari daga litattafan Hausa kala - kala na da dana zamani.

WASANNI - Bangare ne domin matasan zamani, bangaren na kawo labarai ne game da wasanni kala - kala musamman a fannin kwallon kafa a ciki da wajen kasar nan.

To wannan kadan kenan daga cikin bangarorin da wannan jarida ta RARIYA ta kunsa, amma fa kamar yadda na fada ba duk bangarorin na bayyana ba, kadan daga ciki na bayyana, akwai bangarori da dama da ban bayyana ba irin su: Ra'ayin Rariya, Kowa Ya Debo Da Zafi, Allah Daya Gari Bambam, Jiya Ba Yau Ba, Tafarki Madaidaici, Tallata Hajarka, Adon Gari, 'Yar Kwalisa, Ma'aunin Hankali, Ciki Da Gaskiya, Daga Majalisar Tarayya, Hangen Nesa, Cinikayya, Asan Mutum, Girkinki Sirrinki, Sakonnin Masu Karatu da kuma GYARAN GANGAR AZBINAWA wanda babban edita da kansa wato Ashafa M. Barkiya yake gabatar da bangaren, inda yake yin tsokaci game da al'amuran da suka shafi siyasar kasar nan dama duniya baki daya.

Kai amma da yawan mantuwa nake, tunda na fara wannan rubutu nake son yin bayani akan wani bangare saya fi kowane daukar hankali na kuma na san ku ma shafin zai dauki hankalinku kuma ya burge ku, amma ban tuna ba sai da ruwan alkalamin da nake wannan rubutu yazo daf da karewa, hakan tasa idan na fara bayanin bangaren ba zan kai karshe ba ragowar ruwan rubutun zai karasa, kuma nasan ba za ku ji dadin hakan ba, saboda haka bari na bada satar amsar shafin, shafin yana kusa da shafin tsakiya, kuma shafin yana daya daga cikin shafukan da aka fi kawatawa, kai bari dai na dakata anan, domin ganewa idonka abin da shafin ke kunshe da shi yi saurin mallakar taka kwafin jaridar RARIYA, hakan zai baka damar fahimtar sauran abubuwa sama yadda zan yi muku bayani, har ma ku ma ku samu damar bawa wasu labari.

A karshe kamfanin RARIYA MEDIA SERVICES LTD. Shi ne yake daukar nauyin tsarawa da buga wannan jarida a kowane sati biyu a karkashin jagorancin Alhaji Dr. Aliyu Modibbo Ph.D, domin karin bayani za'a iya tuntubar hukumar gudanarwar kamfanin dake lamba 7, titin Thaba - Tseka, kusa da British Village, Wuse II, Abuja ko lambobin waya: 09-8701707, 09-8701708, 08034269830 email: rariyajarida@yahoo.com

Monday, March 12, 2012

Shin Wai Za'a Rufe Shafin Sada Zumunta na Facebook?


Shin yaushe za'a rufe shafin Facebook? Shin wai za'a rufe shafin Facebook? Ranar 15 March, 2012 shafin Facebook zai daina aiki. Zan koma 2go ko Twitter idan aka rufe Facebook. Abokaina na yafe muka, zan koma 2go tunda za'a rufe shafin Facebook. Wannan kadan kenan daga cikin irin rubututtukan da na rinka cin karo da su a shafin sada zumunta na Facebook, wasu kuma kai tsaye suka kira ni a waya suna tambayata gaskiyar lamari akan maganar rufe shafin na Facebook.

Wannan dalili yasa na shiga binciken gano gaskiyar al'amarin. Abinda ya bani mamaki shi ne wannan jita - jita an yada ta ne tun shekarar da ta wuce a watan January 2011, sai ga shi an dawo da ita a wannan shekara ta 2012.

FARKON AL'AMARI - A ranar 9 January, 2011 wata jarida mai suna Weekly World News dake kasar America, ta buga wata mukala a shafinta na Yanar Gizo (Internet) dauke da cewa "Za a Rufe Shafin Sada Zumunta Na Facebook ranar 15 March, 2011" a cikin mukalar an bayyana dalilan da zasu sa a rufe shafin kamar haka: Mark Zurkerberg shugaban kamfani kuma wanda ya kirkiro shafin ya bayyana cewa shafin ya fi karfin hankalinsa, ya kuma ruguza masa rayuwarsa, saboda haka yana so rayuwarsa ta dawo kamar yadda take a da kafin bude shafin na Facebook. Sannan Mark Zuckerberg ya kara da cewa shafin Facebook ya shagaltar da mutane inda ba sa iya yin abokanai ko kawaye a zahiri sai dai a shafukan Yanar Gizo, saboda haka duk wanda ya ajiye hotunansa a ma'ajiyar hotuna (Album) a shafin na Facebook yayi kokarin canja musu ma'ajiya kafin ranar 15 March, 2012 daga ranar mutum ba zai sake ganinsu ba.

Wannan kadan kenan daga cikin dalilan da jaridar ta Weekly World News ta bayyana zai sa a rufe shafin na Facebook, a wannan lokacin wannan mukala ta tada hankulan jama'a musamman wadanda suka sadaukar da lokutansu ga shafin na Facebook (Facebook addicted).

Ana cikin wannan hali ne sai gidan television na CNN ya yi rahoto na musamman akan jita - jitar, wanda suka bayyana cewa sun samu cikakken bayani daga hukumar gudanarwar kamfani na Facebook dake tabbatar da labarin da jaridar Weekly World News ta buga karya ce tsagwaranta.

A tsakiyar wannan sati ranar 13 January, 2011 shafin Facebook ya fito da sanarwa ta musamman akan cewa ba gaskiya ba ne, maganar cewa za a rufe shafin, kuma suka tabbatar da cewa babu wani dalili da zai sa a rufe shafin har abada.

Wannan suna kadan daga abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata, sai kuma wannan shekarar ma aka sake dawo da jita - jitar, wadda wasu ke kwafo abubuwa da suka faru a shekarar da ta gabata suna yadawa.

A karshe gaskiyar al'amari akan wannan magana ta rufe shafin na Facebook ba gaskiya ba ce. Idan bamu manta ba a watannin baya da suka gabata kadan shafin na Facebook ya saka lallar hajojin kamfanin a kasuwa. Sannan a watan December na 2011 aka bayyana shafin Facebook a matsayin na biyu a duniya wurin samun maziyarta a kullum bayan shafin bincike na Google.

Ziyarci Dandalin Bashir Ahmad a shafin Facebook (http://facebook.com/dandalinbashirahmad)

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020

Friday, March 2, 2012

Shafin Dandalin Bashir Ahmad ya Samu Wuri a Duniyar Facebook


Aminci a gare ku! Tare da albishir a gare ku masoya da makaranta wannan Dandali, Ina mai farin cikin gabatar muku da shafin wannan dandali a shafin sada zumunta na Facebook, mai suna DANDALIN BASHIR AHMAD wanda za'a iya samu kai tsaye akan http://facebook.com/dandalinbashirahmad duk da har yanzu ban kammala tsara shafin ba, na sanar da kune domin abin naku ne, don ku aka kirkire shi, fatan zaku so shi kamar yadda kuka so wannan Dandali.

Dalilina na budewa wannan dandali a Facebook shi ne domin samun wani wuri da makaranta dandalin za suke baje kolinsu, kuma nayi hakan ne saboda amfani da shawarar da wasu daga cikin ku makaranta suka ba ni.

Sannan shafin zai kasance wurin bani shawara ta kai tsaye kamar yadda kullum nake maraba ta kowace irin shawara daga wurinku.

A karshe ina godiya da kulawarku a gare ni a koda yaushe, musamman wadanda suke kira na a waya ko aiko min da sakonni. Allah ya bar zumunci.