Tuesday, June 2, 2015

Yadda Na Fahimci Sabon Shugaban Kasa Janar Buhari

Daga Bashir Ahmad, Abuja

Janar Muhammadu Buhari wanda a ranar Juma'a (29/5/2015) aka rantsar da shi a matsayin sabon zababben shugaban kasar nan, Nijeriya, mutum ne kamar kowa, amma za a tara daruruwa ba a samu mai halaye irin na sa ba. Na fahimci hakan ne saboda damar da Allah ya bani na kasancewa a kusa da shi sosai yadda har na iya fahimtar shi wane ne. Na fahimce shi daidai kwarkwadon da zan iya rubuta babban littafi akan sa.

Farkon haduwa ta da Buhari, na fara magana da shi ne tun kafin na fara ganinsa ido da ido, har yanzu ina tunawa nayi wani rubutu ne akan sa mai take "Dalilina Na Son Janar Buhari" a wajajen 2009, cikin rubutun na bayyana cewa ni ban taba ganin Buhari ba, lokacin da yayi gwamna a tsohuwar jihar Arewa maso Gabas, yayi ministan albarkatun man fetur da shugaban hukumar NNPC, sannan ya zama shugaban kasa a mulkin soja ba a haife ni ba, haka kuma lokacin da ya jagoranci hukumar PTF bani da cikakken wayo da hankalin da zai sa na san halin da kasa take ciki, amma duk da haka na ji na taso da son sa cikin zuciyata, da kuma imanin idan ba shi Nijeriya ta samu ba, zamu iya kasancewa a lalace ba tare da mun koma mikakkiyar hanyar da a baya muke kai ba. Wannan shi ne ginshikin rubutun nawa, sannan na sa a shafina na yanar gizo (www.dandalinbashir.blogspot.com) wanda a lokacin na tabbatar dubban mutane za su ga rubutun kuma za su karanta, amma ko a mafarki ban taba tunanin wani na kusa da Buhari zai karanta rubutun har ya sanarwa Buharin ba. Amma sai Allah ya kaddari hakan, wani wanda har yanzu ban san ko wane ne ba, ya karanta rubutun nawa kuma ya kaiwa Buharin ya gani, watakila a lokacin Buhari ya kalli kananan shekaruna ne, shi ya sa abin ya burge shi, don haka sai ya umarci wanda ya kawo masa rubutun ya gani ya kira ni a waya mu gaisa da shi. Haka kuwa aka yi ina zaune na ga waya ta shigo, dama tun a baya a tsarina bana tantance kiran da zan amsa, nan take wannan kiran ma na amsa, bayan mun gaisa da wanda ya kira din, sai ya ce fatan yana magana da Bashir Ahmad ne, na ce kwarai shi ne, sai ya ce ya fahimci ina son Buhari, ko zan fada masa dalilin hakan, sai na bashi amsa da cewa ba zan iya cewa ga dalili ba, amma ina tunanin saboda na ga yadda ya rike manya mukamai a baya ne amma ba a taba samun sa da hannu cikin kowace irin almundahana ba, watakila haka ne ya sa zuciya ta aminta da shi nake sonsa, daga nan sai kuma ya sake tambaya ta ko na taba haduwa da Buharin mun yi magana, sai na ce ai ko ganinsa ma ban taba yi ba, sai ya ce to idan aka ce yau ga Buharin za kuyi magana ya zaka ji, sai na fada masa cewa zan yi farin ciki matuka, daga nan bai kara cewa komai ba sai ya ce ga Buharin za ku gaisa, hmmmm! Maganar gaskiya har yanzu na kasa kwatanta abin da na ji a zuciyata, kawai dai na ji an cewa Assalamu Alaikum, Malam Bashir, wato Buhari ne kenan ya karbi waya, har muka gama wayar ta kusan mintuna 3, na kasa cewa komai sai dai bada amsa da eh, na'am ko a'a.

Haduwar mu ido da ido, wannan kuma ya faru ne lokacin da ya zo Kano yakin neman zabensa a 2011, na gan shi a cikin mota zai je gidan Sarkin Kano, yana dagawa magoya bayansa hannu, amma mun fara magana ne bai fi shekaru biyu ba, a lokacin ina aiki da Jaridar Rariya, bayan kafa APC, an gudanar da wani taro a otel din Transcorp Hilton, a birnin tarayya Abuja, sai gani ga Buhari, ban ji tsoro ba, kuma na taki sa'a jami'an tsaronsa basu dakatar da ni ba, watakila don sun ganni da shedar cewa ni dan jarida ne, sai kawai na je inda yake a zaune na tsuguna na gaida shi ya amsa, sannan na ce Baba ni ne Bashir Ahmad na Kano, abin mamaki ina tuna masa kaina sai ya gane, mun danyi magana ta 'yan mintuna ya tambaye ni karatu da inda nake aiki duk na fada masa. Ba dadewa kuma sai na zama daya daga cikin ma'aikatan Sam Nda-Isaiah, a lokacin da yake neman takarar shugabancin kasa a APC, da yake koda yaushe ina tare da maigidana Nda-Isaiah sai ya zama muna yawan haduwa da Buhari akai-akai, na kan yawaita zuwa gaida shi har ya gane cewa ina tare da Sam ne wato muna takara tare da shi, amma ko kadan ban ga wani sauyi a fuskarsa ba.

Akwai ranar da APC ta gudanar da wani babban taro a Abuja, kowa a jam'iyyar ya halarci taron, ga shi kuma satin Sam zai kaddamar da takararsa a Minna, ni na je da katin gayyata na gwamnoni da duk manyan jam'iyyar don raba musu a wurin taron, ciki har da na Buhari, dana je kai masa na sa, bayan mun kaisa sai nace Baba ga kati muna gayyatarka taron kaddamar da takararmu, sai yayi dariya ya ce "Bashir ai ni da na kaddamar da tawa takarar ban ga kun zo ba, ni kuma sai ku gayyace ni na ku?" Sai na ce Baba ai lokacin dukkan mu mun zo, Oga (Sam) ne dai kawai bai zo ba, kuma shi ma lokacin yayi tafiya baya kasa ne da shi ma zai zo, sai ya ce shi kenan tun da haka ne na kara masa katin gayyatar uku ya zama biyar, da biyu na bashi, sannan ya ce idan suna gari za su zo. Haka kuwa aka yi a lokacin da aka gudanar da taron Buhari na Port Harcourt amma sai da ya tura wakilansa wurin.

Buhari baya ganin mutum a matsayin karami idan har yana da babban tunani, a ranar da aka gudanar da babban taron jam'iyyar APC a Lagos inda jam'iyyar ta gudanar da zaben fidda dan takara, wanda ya samu nasarar lashe zaben, tun ana cikin gudanar da zaben saboda ganin yadda zaben ke tafiya, sai na hau sama wajen da manyan baki suke zaune, naje wurinsa bayan na gaida shi sai na ce Baba na zo taya ka murna ne, sai ya ce ya gode sosai, ni kaina a wurin nayi mamaki sosai, wurin duk gwamnoni ne da shugabannin jam'iyyar amma mun kusa mintuna 10 ina tsugune Buharin ya sun kuyo kansa muna zance wanda ko wadanda suke kusa da shi ba wanda yake jin abin da muke fada, bayan na taso na sha kallo ta ko ina, kai akwai wani babban ma sai da ya taso ya biyo ni yake tambaya ta wai ni wane ne, sai kawai na ce ni SA ne na Sam Nda-Isaiah, sai ya ce "oh na gane".

Ban taba haduwa da wani babba da yake da rikon addini kamar Buhari ba, na je yakin neman zabe da Buhari a jihohi da dama ciki har da Borno, amma duk jihar da aka je idan lokacin Sallah ya yi kafin a fita filin taro sai ya yi Sallah kafin a fita, idan kuma ana filin taron lokacin yayi, to ana dawowa masauki ba abinda yake fara yi sai Sallah, akwai wata rana da aka dawo daga Lagos, ana sauka a filin jirgin Abuja, Buhari bai wa kowa magana ba, sai kawai ya wuce bandaki ya dauro auwala, anan dole sai da kowa ya tsaya ya idar da Sallah, sannan aka tafi. Kuma yana yawaita yin azumin Litinin da Alhamis.

Na san duk wanda ya san Buhari ya san cewa shi mai gaskiya ne da kuma rikon amana, to kullum abin Buhari yake jaddawa duk wadanda suke tare da shi kenan kan su rike gaskiya da amana za su ga amfanin haka tun a duniya.

Buhari yana da wasa da dariya, idan ana zaune da shi a wajen ba a yin shiru ba tare da ana murmusawa ba. Wannan shi ne Buharin da na sani, kuma yanzu shi ne shugaban kasar Nijeriya.

- Ni (Bashir) ina daya ne daga cikin membobin kwamitin yada labarai na shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma mataimaki na musamman ga Sam Nda-Isaiah, sannan ina aiki da Jaridar Leadership.

An fara buga wannan rubutun a jaridar Leadership ta ranar 29 ga watan Mayu, 2015, ranar da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.

Saturday, May 30, 2015

MARTANI - ‘LEADERSHIP HAUSA: Tarihin Da Ba Ku Sani Ba’ Shawara Ga Ashafa Murnai Barkiya

Daga Al-Amin Ciroma

Idan za a iya tunawa, a ranar 15 ga Mayu, 2015 mun yi fitowar musamman don yin bikin Bugu na 450 wanda ya ja hankalin hankalin jama’a da dimbin masu karatu a ciki da wajen kasar nan. A lokacin ne muka nemi editocin baya, su dan tofa albarkacin bakinsu game da jaridar da yadda suke kallonta a yau.

Da kaina na aika musu da sako bai daya kamar haka: ‘Salam edita a fitowarmu ta wannan makon, za mu yi wani Special edition ne. Don haka, a matsayinka na daya daga editocinmu, ko za ka dan tofa albarkcin bakinka kan tambayoyi biyu kacal: (1) Me za ka ce game da Leadership Hausa? (2) Yaya kake ganinta a yau? (Pls also confirm to me the date u were employed and when u left.) Na gode, na ka, Ciroma.’

Ba tare da bata lokaci ba editan jaridar na farko, Malam Ibrahim Biu ya aiko da amsa, kamar yadda ya fito a bugun na musamman (15 ga Mayu), ya ce: “Tsakani da Allah jarida ta yi armashi ina alfahari da ita domin ta kawo karfin da ba Nijeriya kadai ba, duk inda mutum yake matukar zai kalle ta, hakika ya san a na yi wa Hausawa hidima. A Nijeriya kuwa LEADERSHIP HAUSA ta zama matashiya da manuniya saboda irin labaranta. 

“An wayi gari a yau akwai wasu mutanen da hankalinsu ba zai kwanta ba sai sun nemi jaridar a duk ranekun Jumma’a sun karanta, ba don komai ba sai kasancewar tana bayyana abubuwa da yawa da masu karatu suke son karantawa.

“Zan yi amfani da wannan damar na kara karfafa wa ma’aikata shashen na Hausa kwarin gwiwa kan su dage da hakuri don cimma babbar nasara nan gaba, musamman editanta a yanzu, ina mai ba shi shawara da ya ci gaba da hakuri da jajircewa har Allah Ya kara ninnika nasarori.”

“Na fara aiki a ranar 22 ga Satumbar 2006, na kuma yi murabus a ranar 9 ga Oktoba, 2006, inda a ka nada sabon edita.” In ji Malam Biu.

Shi ma edita na uku, Alhaji Salisu Alhassan Bichi a jerin editocin jaridar, ya kama aiki a ranar 24 ga Oktoba, 2011, ya kuma ajiye aiki ranar 30 ga Disambar 2011, ya ce: “Leadership Hausa ta kasance abu mafi inganci da ya taba faruwa ga makaranta harshen Hausa a wannan karni. Kasancewar masu sha’awar labarai da sharhi sun ta’allaka ne kacokan a sauraren rediyoyin kasashen ketare tun tsawon lokuta, sai ga shi a yau jaridar nan ta bayar da damar karanta duk iron labarai da sharhi akan kowane al’amari a dukkan fadin duniya.

“Har yanzu ba ta da na biyu kuma kullum kara daukaka take da shahara a tsakanin manyan mutane da talakawa. Da dama a kan aje kudi ne kafin ta iso don wanda suka saba da ita har da wasu fitattun gwamnoni da mutanen jami’a ba su yarda su rasa ta a kowace Jumma’a. Allah ya kara daukaka da basira.”

Amma ta bangaren edita na biyu Malam Ashafa Murnai Barkiya, al’amarin ba haka ya kasance ba. Farko sai da ya dauki lokaci mai tsawo bai aiko da tasa amsar ba. Daga bisani ya turo min cikakkiyar makala mai dauke da kimamin kalmomi 2689 (dubu biyu da dari shida da tamanin da tara). Ban samu lokacin karanta duka rubutun ba domin muna gaggawar kammala  aiki ne a lokacin da ya turo amsar, amma na dan tsakuro kadan din da zan iya amfani da shi, bisa alkawarin zan buga masa sauran nan gaba. 

Fitowar jaridar ‘Rariya,’ ta ranar 15 ga Mayu, 2015, ya dauki hankalina har na karanta rubutun baki daya, wanda na fahimci akwai matsalolin da zan iya jan hankalin Malam Murnai a kai, musamman don fahimtar juna.

A zatona tuni kan mage ya waye babu sauran hauma-hauma ba duhun kai, amma makalar tasa, wadda ya yi wa taken: ‘LEADERSHIP HAUSA: Tarihin Da Ba Ku Sani Ba,’ da ta fito a bangon jaridar ta ‘Rariya ’ ya tabbatar min har yanzu da sauran rina a kaba. A ganina ya kamata mutum ya yi amfani da kaifin alkalaminsa don wanzar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban al’umma maimakon haddasa rikici, gaba ko bayar da labaran kanzon kurege.

Shawarar farko da zan ba wa Malam Murnai wato editan ‘Rariya’ ita ce, ya rika amfani da hikima, ilmi gami da shimfidaddiyar zuciya a duk lokacin da kuduri aniyar aika sako ko mayar da martani. Ya kamata mutum ya mallaki kansa, ya rike akalar zuciyarsa kada ta yi tutsu da shi, domin bin son zuciya asara ce babba.

Misali, daga cikin abubuwan da suka ba ni mamaki shi ne inda ya ce: “Lokacin da Al-amin ya fara neman ma’aikata, ni ya zo har Kano ya samu, inda ya kira ni a waya na ce masa ina wurin walimar bikin Sulaiman Uba Gaya, mawallafin Jamhuriya a Murtala Mohammed Library. Ya je can ya same ni, ya ce min ya zo ne musamman domin ya ga Maje El-Hajeej Hotoro, kuma ya neme shi bai samu ba, an ce masa idan ya ga Ashafa to ya ga Maje. Na shaida wa Al-amin cewa to Maje kan kashe waya ya ma ya manta da ita ya shiga wani sagarabtu can daban. Don haka tunda kwana zai yi a Kano, ya kwantar da hankalinsa, da safe karfe goma zuwa sha daya na rana ya je LISS COMPUTERS kusa da Dangi Pharmacy inda muke aikin Jamhuriya, idan bai samu Maje a wurin ba, to Maje zai same shi a wurin.” 

Wannan maganar  ce ta fara jan hankalina har na fahimci akwai matsaloli a cikin rubutun na Ashafa, domin a tashin farko akwai coge a zancen. Abin da na san ya faru shi ne: Lokacin da Shugaban Kamfanin LEADERSHIP Mista Sam Nda-Isaiah ya bugo min waya, tambaya daya ya yi mani, ko na iya rubutu da Hausa? Na ce da shi ina dan kokartawa, ya ce ‘That’s good!’ Wannan ita ce ranar farko da na san yana da niyyar fara jaridar Hausa. Duk da na san Daily Trust na shirin fito da ta Hausa wato Aminiya. 

Kai tsaye Mista Sam ya umarce ni da in je in samu Akanta, ya ba ni kudi in tafi Kano, in nemi matashin da na san yana rubutun Hausa mu fara tunanin yadda za a kirkiro jaridar kafin ya dawo daga kasashen waje. 

Bisa wannan umarnin ne na kama hanyar Kano, amma kafin in tafi, mun dan tattauna maganar da mai dakina, kan wanda ya dace in nemo a Kanon. Da farko na kawo mutane hudu, Ado Ahmad Gidandabino, Sanusi Daneji, Bala Anas Babinlata, har da shi Ashafan. Amma a nata ra’ayin, ta ce idan har aikin jarida za mu yi, kada mu tsallake Maje el-Hajeej Hotoro. Ta dan fadi wasu abubuwan da ta sani game da shi, tun da ta zauna a Kano, kuma ta san wasu abubuwa game da adabi a lokacin. Babban abu ma ta nuna bisa yadda take kallon kowanne daga ciki, shakka babu Hotoro zai iya finsu hakuri da juriyar aiki. Wannan shi ne musabbabin neman lambar Maje daga wajen Ashafa, tun da ba mu taba haduwa ba.

Ko da na je Kano muka hadu da Murnai, na nemi ya ba ni lambar Maje, kafin ya bayar, ya rika yawo da hankalina, a dole sai ya san dalilin neman Maje a kaikai ce. Ko da na fahimci wayonsa na dage kan ya ba ni lambar kawai. A nan, duk wanda ya san Ashafa, zai iya bayar da shaida irin yanayinsa. Idan ka je neman abu a wajensa, kafin ya ba ka,  zai yi ta yawo da hankalinka tare da bin diddigin gano abin da kake nema tukunna. Na san da haka sosai, shi ya sa ban furta masa komai ba. Da ya ga dai na dage kawai ya zaro wayarsa daga aljihu ya ba ni lambar Maje, muka yi sallama, na kama gabana. 

Don haka, babu zancen mun yi zan kwana a Kano ko kuma Maje na kashe waya da sauransu.

Sannan a cikin rubutun har ila yau, daidai inda Murnai yake bayyana yada ya shigo kamfanin LEADERSHIP, nan ma ba haka aka yi ba, kuma a zatona edita zai yi adalci ya fadi hakikanin yadda ya samu aikin da ya kara haska shi a duniya. Amma watakila malamin yana bisa ingarmar dokin zuciyarsa ne, har ya kasa rikonsa da kyau, ya yi sake haniniya da yunkurin dokin suka ruda masa kwakwalwar da ya kasa damkewa yadda ya kamata. Ya bige da fadin: 

“Wshegari Al-amin ya kira ni muka yi maganar cewa don Allah na zo na yi aiki da Leadership Hausa. Na bayyana masa uziri na, na ce ina son aiki da ku wuri daya amma Sulaiman mai Jamhuriya fa? Al-amin ya ce na yi masa magana, na ce gaskiya ba zan iya ce masa wani abu ba, domin haushi zai ji. Muka shirya cewa shi Al-amin din ya kira Sulaiman, kuma haka aka yi, ya kira shi suka yi magana. 

Daga baya Sulaiman ya ce min shi wallahi babu komai, tunda ma jaridar tasa ta tsaya, kuma ana tare ai ba wani abu ba ne. Ya kira Al-amin ya ce masa ya amince. Sai ya ce shi tunda ya san Sam da dadewa, ya kira shi a waya ya ce masa ya ga jaridar da ya kafa ta Hausa, amma ya fahimci akwai matsaloli, wadanda shi idan ya na bukata, to yana da editan da zai rike masa jaridar sosai.”

Masu karatu, wannan ita ce maganar da ta fi sosa min rai, don kuwa ina ganin bai kamata Murnai ya yi saurin manta da irin halascin da ni kaina na yi masa ba. A tunanina lokaci bai yi ba da har Ashafa zai yi saurin manta wannan ba. Amma kuma ban yi mamaki ba domin na fada a farkon bayanina, muddin ka kasa mallakar kanka a yayin da kake kokarin isar da wani muhimmin sako, shakka babu, shaidan zai yi wasan kura da zuciyarka, daga bisani ka rasa alkibla. Bisa wannan dalilin ne muke ganin yadda manyan mutane, wadanda suka san kansu suke iya wasa da alkalumansu wajen yada alheri ba sharri ba, kuma su yi amfani da kaifin hankali, ilmi da basira wajen rubutu.

Kafin na nemi Ashafa, tabbas mun yi maganar nemo wani daga Kano da Maje el-Hajeej, har  ya kawo min zancensa. Na ce bai  kamata mu shiga hakkin Malam Ibrahim Sheme ba, saboda a lokacin ana buga jaridar Public Agenda a Kaduna sannan Murnai na daya daga cikin wakilan Sheme a Kano. Don haka a tunanina dauke Ashafa zai iya haifar da tasgaro ga jaridar tasu. Maje dai ya dage cewa babu wata matsala, don yana da tabbacin shi ma Ashafa zai so aikin.

Ba tare da bata lokaci ba na daga waya na kira shi. Bayan mun gaisa na tambaye shi ko zai iya aiki da mu a Abuja? Amsa mai sigar tambaya da ta fito daga bakin Murnai ita ce: ‘Wane mukami za a ba ni?’ Na yi dariya, na ce da shi, ‘Ashafa kenan! Kada ka manta na sanka da dadewa mutum ne mai son tsayuwa da kafafunsa, kana da kokari matuka kan aiki, don haka wannan wata dama ce da za ka iya amfani da ita domin cimma burinka a rayuwa. Ka zo Abuja mu hada kai mu yi aiki tare, mu taimaki juna don ci gabanmu baki daya.’ 

Ya ji dadin hakan sosai. Muka fara tunanin yadda za a dauke shi. A take wata dabara ta fado min. Dabarar kuwa ita ce mu nemi hanyar gabatar da shi a wajen Mista Sam, ta yadda ba zai fahimci ni ne da kaina na kawo shi ba.

Muka yi ta shawarar wanda zai yi mana wannan, a take a lokacin tunanin Malam Badamasi Burji ya fado min, amma Murnai ya ce a manta da zancen Badamasi. Ya kara da cewa akwai wani aminin Chairman dinmu, Alhaji Suleman Uba Gaya, shi ya fi dacewa ya yi hakan. Ya turo min lambarsa na kira shi. Bayan na kira Malam Suleiman muka yi magana, ya fahimci komai. Ya ce ba matsala zai nemi Sam.

Mun yi haka da ‘yan mintuna kwatsam, sai Mista Sam ya bugo min: “Ka san wani Ashafa daga Kano?” Wannan ita ce tambayarsa. Na shaida masa hakika Murnai haziki ne a fagen rubutun Hausa. Ban manta kalmar ma da na yi amfani da ita ba cewar: ‘Ranka ya dade Ashafa IS A GENIUS!’ abin da na fada wa Sam ke nan. Jin haka ya ce bari ya gayyato shi gobe-goben nan. 

Yana shigowa Abuja kuwa da kaina na dauko shi a daidai kasuwar Garki zuwa ofishinmu. Har na yi masa barkwanci na ce, ‘Malam Welcome to Abuja!’ aka dai yi dariya. Wannan shi ne hakikanin abin da na sani game da samun aikinsa a LEADERSHIP. Malam Suleman Uba Gaya yana nan a raye, Maje el-Hajeej shi ma haka bai kamata Murnai ya dakile wannan ba, ko da rai ya baci.

Haka kuma a rubutun nasa har wa yau, Murnai ya nuna wa duniya a ofis yake kwana. Kwarai an yi hakan, amma na dauka zai fadawa mutane nawa aka ba shi ya kama gida, hakan zai ba jama’a damar kimanta darajarsu a shekarar 2007. 

Koma dai me? Ina ba wa Murnai shawara nan gaba ya guji irin wadannan maganganun, idan ma zai yi, yana da kyau ya sa hikima, ilmi da basira a ciki. 

Na tabbatar malamina Barkiya ya san dalilin da har ya sa aka dakatar da biyan kudin gidansa. Idan ya manta ba abin mamaki ba ne domin shi mutum mai saurin mantuwa! 

Amma ba ya rasa nasaba da yadda ya ki amfani da kudin don kama gida, maimakon hakan, ya rika kwana a ofis, a zatonsa ba a gane ba. Duk da an gane din, sai da aka kara ba shi kudin gida a karo na biyu, amma gafarta malam bai daina kwana a ofis ba. Idan kai ne, za ka ci gaba da biyan kudin? Da fatan editana ya tuna da wannan, kuma zai kiyaye nan gaba.

A cikin rubutun Murnai ya kara cewa: “Babun irin wahalar da ban ci ba a wajen fito da LEADERSHIP HAUSA kowace Juma’a. An sha gama aiki za a tafi buga jaridar kudin colour separation ya kakare, sai dai na dauka a aljihu na na bayar a je a yi, don kada safiya ta yi ba a buga jaridar ba.”

Ya salam! Da na karanta wannan sadarar sai da na kusa faduwa saboda dariya. Da me wannan zancen ya yi kama? Ashe Malam Murnai yana da hannun-jari a kamfanin LEADERSHIP ba mu sani ba? Duk da yanzu nake koyon aikin jarida, amma na kan ji ana fadin ayyukan edita. An ce babban aikin da ya rataya kan edita shi ne duba jarida, tabbatar da kammalar shafuka, bayar da umarnin bin diddigin tsaftace labarai da rahotanni, da dukkan shafukan jarida. Uwa uba, tantance manufar jarida don gudun haddasa husuma ko tashin hankali a cikin al’umma gami da wayar da kan jama’a bisa abubuwan da ke faruwa.

Idan har ban yi kuskure ba, ashe kenan babu abin da ya hada edita da harkar dab’i wato buga jarida. Ke nan a yayin da edita ya yi wannan, ya gama aikinsa. Daga nan jami’in dab’i yake dorawa. Zai tabbatar da fitar jarida a tsarin da ake sayarwa a kasuwa.

Idan har haka ne, mene ne matsayin Murnai a LEADERSHIP HAUSA? Jami’in dab’i, mawallafi ko edita? Na dauka Murnai zai fito ya fadi dalilin biyan kudi daga aljihunsa da ya ce yana yi, don a gaggauta fito da jaridar. A ganina, ba wanda zai ba wa edita laifi idan aka kasa buga ta. Wannan ke nan.

Yana da muhimmanci mu tunawa Murnai cewa kowane kamfani yana da tsarin fitar kudi daga wajen akanta. Me ya sa ba zai hakura har sai lokacin da kudin suka fito daga can ba? Ko su kansu masu kamfanin ba su san da aikin jaridar ba? Sannan tun daga aka fara LEADERSHIP, akwai ranar da aka ce saboda babu kudi, jarida ta makale ta kasa fitowa? Ko ya taba jin LEADERSHIP HAUSA ta tafi hutu, ko ta yi nukusanin fitowa?

Ba mu sani ba ko dai malam yana da wata ‘yar yarjejeniya da ya kulla da wasu...? Ko kuma sun ba wa yaransa na goro, wanda idan jaridar ba ta fito a daidai lokacin da ya kamata, za su iya tilasta wa malam ko yaran malam su amayar da dan hasafin da suka yi wa hadiyar Kafino? Allah-gafarta malam ya girmi wannan, kuma bai dace ya rika yayata hakan ga duniya ba.

Tun da aka ba ni wannan kujerar, da zarar na kammala aikin jarida na rattaba hannu kan shafuka, wallahi ba na waige. Zan kama hanya sai gida. Idan ta jarida ba ta fito ba, babu wanda zai tambaye ni dalili don ba aikina ba ne.

A gaba, Murnai ya kara cewa: “Aka rika kawo motoci birjik ana bai wa editoci da sauran manyan ma’aikata, sai da aka shafe sama da shekaru biyu ana raba motoci, amma ni sai dai kallo, sai alkawarin idan an kara kawowa za a ba ni. Farkon lokacin da aka fara kawowa, da aka bai wa editoci sabbin motoci garau daga kamfani, ni sai aka hada ni da wata akwalar Honda Cibic. Kullum ta lalace a hanya, ko ta ki tashi ko ta cakire. Kafin na fara hawanta ma sai da na sai mata sabbin tayoyi. 

“Bayan na yi hadari da ita ne, aka ba ni hakuri, aka ce za a ba ni sabuwa, amma hakan ba ta yiwuba, har sai da haushi ya sa na rubuta takardar barin aiki, inda a cikin dalilai na har da rashin dauka ta da daraja, ga rashin ba ni kudin kama haya, ga kuma rashin ba ni mota, wai sai ake ce min na hakura sati mai zuwa za a ba ni sabuwa rangadau.”

Allah sarki! Ban so a ce Murnai ya fadi wannan ba, domin malam ne ya jaza wa kansa matsalar ba kamfani ba. Tabbas an yi rabon motoci, amma kamar yadda na fada a baya, kowane kamfani yana da tsarin gudanar da ayyukansa. Ina son edita ya kara tuna cewa ko a cikin editocin ma akwai wadanda suka riga shi fara aiki, amma kafin a zo kansa, akwai wata tsohuwar motar da aka nuna masa. Aka tambaye shi ko yana bukatar mallakarta, ko kuma zai jira a kawo wasu sabbi? 

Da ya shawarci mutane, na tabbata wani zai ce kada ya karbi tsohuwar, za a iya ba shi shawarar ya bari har sai an kawo wasu sabbi ya karba. Amma na fahimci a lokacin kowa so yake a ce yana da mota. Watakila dalilin da ya sa Malam ya karbi tsohuwar akwalar kenan.

Har bayan da ya yi gaggawar karbar motar, Murnai ya ji dadinta kwarai domin ko ba komai a kanta ya koyi tuki. Sai dai, kamar yadda na fadi a baya, bai kamata edita yana irin wannan zancen a kafa kamar wannan ba. Ko da zai yi, da sai ya yi magana cikin falsafa da ilmi. Amma aikin gama ya gama, malam ya tallata kansa a duniya, kuma bai fadawa mutane dalilin rashin ba shi sabuwar mota ba. Watakiala masu kamfani sun lura bai riga ya kware a tuki ba, kullum fadawa yake cikin hatsari daban-daban, me zai sa su dauki dankareriyar mota su bayar?

Mu ma ture duk ma wannan a gefe, don ba a ba ka mota ba har sai ka tayar hankali? Bai dace Gafarta Malam yana irin wadannan maganganun ba. Yaya yake son mu na baya mu yi?

Zan takaita a nan domin ba na son tsawaitawa, amma ina ba Malam Ashafa shawara da ya rika tauna zance kafin ya fade ta, hakan shi ne jarunta ba kawai abin da ya zo zuci ba.

Ban damu da yadda har ya kammala rubutunsa bai fadi wani abu daya da ya gani na ci gaba a LEADERSHIP HAUSA a yau ba. Duk kuwa da sanin cewa a yanzu duk kamfanin nan, babu jaridar da ta fi ta mu ta Hausa kasuwa. Sabanin a zamaninsa da bai fi a sayar kwafe dubu biyu zuwa uku ba. Ya kamata malam ya zo ya tambaya a yau kwafe nawa ake bugawa? Kuma nawa ake sayarwa? Sauran editocin da suka gabata (wato Malam Ibrahim Biu da Salisu Alhassan Bichi), sun yaba mana sun kuma ba mu shawarwari masu amfani.

Don haka ya dace editan Ashafa ya daina ci ga zuci, ya rika dora alkaminsa bisa ilmi da basira domin idan baki ya san na fade, bai san na mayarwa ba. Ban ji dadin yadda ya nuna hassadarsa karara ba, don kuwa har ya kammala ‘...Tarihin da ba ku sani ba,’ babu inda ya yaba da irin yadda jaridar take a yau, amma hakan ba ta hana shi bata lokacinsa wajen kwaikwayon LEADERSHIP HAUSA ba. Duk wanda ya kalli ‘Rariya’ da idanun basira, zai ga hakan. Na dauka Murnai zai yi wa jaridar tasa sabon zubi ne ta bambanta da sauran jaridu, kamar yadda kowa ke yi ba wai ya rika kwaikwayon wasu ba. Amma dai ko makaho ya shafa ya san ‘Ta Mu Ba Irin Ta Su Ba Ce!’ 

Shawara ta karshe da zan bayar a nan ita ce ya daina bata wa kansa lokaci wajen neman yardar mutane don a yaba masa, a wajen Allah ake neman yarda. Kalas! 

Saturday, May 23, 2015

Za A Tsaurara Tsaro Wajen Bikin Rantsar Da Buhari, Ana Tsammani Shugabannin Kasashe 50 Za Su Halarta

...Ana tsammanin shugabannin kasashe sama da 50 za su halarta


Yayin da ya rage mako guda a gudanar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, #HAUSA24 ta kutsa ta tattaro yadda aka shirya bikin zai kasance.

Bikin wanda ake tsammanin shugabannin kasashen sama da 50 za su halarta za a gudanar da shi ne filin taro na Eagles Square a babban birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda HAUSA24 ta samu labari daga majiya mai tushe duk wanda zai shiga filin taron sai ya kasance yana tare da takardar gayyata, kuma sai an tantance shi kwana daya kafin bikin, sannan ranar rantsuwar a sake maimaita irin tantancewar.

Majiyar ta mu ta bayyana cewa saboda tabbatar da ingantaccen tsaro a wajen bikin jami'an tsaro ba za su bar duk wanda bashi da takardar gayyata ya kusance filin taron ba, haka za a dakatar da zirga - zirgar ababen hawa daga yankin wajen kwana biyu kafin taron.

Bakin da suka shigo Abuja kuma ba tare da takardar gayyata ba, akwai shirin da aka yi na samar da manyan allunan kallo don haska abinda ke faruwa a sannan daban - daban a Abujan nesa da filin Eagles Square kamar yadda majiyar ta tabbatar mana.

Tuni dai tun yau Juma'a aka fara gudanar da bukukuwan ranar rantsuwar inda aka fara da addu'o'i a babban masallaci na kasa.

Saturday, May 16, 2015

Shawarwari 52 Zuwa Ga Matan Aure, Zawarawa Da 'Yan Mata - Sheikh Jaafar Mahmud Adam

Daga Sheikh Jaafar Mahmud Adam

Da sunan ALLAH mai gamammiyar rahama mai jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahama, Annabi Muhammadu (SAW) da alayansa, da sahabbansa, da duk wadanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar tashin al-kiyama. Bayan haka, shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani, kafin a yi auren.

Ga wasu shawarwari 52 wadanda idan matan suka yi la'akari da amfani da su da yardar ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure.

1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.

2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.

3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.

4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.

6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.

9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.

10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.

11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.

12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.

13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.

14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan uwansa da abokansa.

15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.

16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.

17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.

18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.

19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.

20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.

21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.

22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.

23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.

24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.

25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.

26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.

27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.

28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.

29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.

30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.

31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.

32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.

33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.

34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.

35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.

36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.

38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha'awa ko soyayya.

39- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.

40- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.

41- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin mijinki abinda ya umarceki da a basu.

42- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.

43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.

44- kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.

45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.

46- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.

47- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.

48- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan uwansa.

49- Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.

50- Kada ki ringa baiwa 'yan uwan mijinki labarin laifukansa.

51- kada ki ci wani abu da mijinki baya son warinsa misali tafarnuwa.

52- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da 'yan uwansa.

Wadannan su ne shawarwari 52 daga bakin Marigayi Sheikh Jaafar Mahmud Adam zuwa ga mata. Allah ya bada iko wajen kamanta da aiki da shawarwarin.

Thursday, May 14, 2015

Ya Zama Dole Buhari Ya Cika Duk Alkawuran Da Ya Dauka Lokacin Yakin Neman Zabe - Sule Lamido

Gwamna Sule Lamido na jihar Jigawa, ya kalubalenci zababben shugaban kasa, Janar Muhammdu Buhari da jam'iyyarsa ta APC.

Lamido yayin da yake jawabi a yau a jihar Neja, yayin bude wasu ayyuka ya ce Buhari da APC ya zama dole su cika dukkan wasu alkawura da suka daukarwa 'yan Nijeriya lokutan yakin neman zabe, ba tare da neman kowane irin uzuri ba.

"Sun yi kokari ruguza Nijeriya da kawo tashin hankali tsakanin kabilu da mabiya addinai, sun yi alkawuran karya. Ya zama dole su cika wannan alkawura ba tare da neman ayi musu kowane irin uzuri ba" in ji Lamidon.

Ya kara da cewa a lokacin yakin neman zaben APC ta maida hankali ne wajen aibata PDP ta hanyar amfani da rashin tsaro, Boko Haram, rashin aikin yi, don haka ya zama dole su cika dukkan alkawuran.