Saturday, December 13, 2014

Yakin Neman Zaben Sam Nda-Isaiah: An Fara Da Murmushi An Kammala Da Murmushi

MASHA ALLAH! MASHA ALLAH!! Godiya ta tabbata ga Allah (SWA), an fara da murmushi an kammala da murmushi.

Yau 11/12/2014 APC ta kammala babban taronta na kasa, inda wakilan jam'iyyar suka zabi dan takarar shugabancin kasa a zaben 2015 na jam'iyyar, kuma Allah ya bawa Janar Muhammadu Buhari nasara da gagarumin rinjaye.

Maigidana Sam Nda-Isaiah na daya daga cikin masu neman takarar su biyar, sai dai Allah bai bashi nasara ba, a zahiri, amma a badini yayi nasara (duk wanda ya san tsakanin su da Buhari zai fahimci hakan).

Kusan watanni 10 ana wannan aiki, tun da aka fara Allah cikin ikonsa ya sa an shiga cikin lafiya, kuma yau ga shi an kammala cikin lafiya.

Bayan na mika dukkan godiya ta ga Allah, ina kuma godewa iyaye na da dukkan 'yan uwana da suka bani cikakken goyon baya, sai kuma edita na Al-Amin Ciroma (Leadership Hausa), da dukkan abokaina masu daraja, kwarai na samu muhimmiyar gudunmawa daga gare ku, kuma ina godiyar sosai da sosai Allah ya sanya alheri. Kullum ina kara godewa Allah da ya ba ni abokai irin ku.

Ina rokon ku addu'ar Allah ya sanya wa abinda zan sa anan gaba ya kasance mai alheri na gare ni da addinina.

...Ina taya Baba (Janar Muhammadu Buhari) murnar wannan gagarumar nasara, kuma in sha Allah zan bada duk wata gudunmawa da zan iya, da dukkan abinda Allah ya hore min don ganin Buhari da APC sun yi nasara a 2015!

Wednesday, December 10, 2014

TA'AZIYYA: Rasuwar Ibro Ta Sani Hawaye

Kamar mafi yawan lokuta, yau ma karar kiran wayata ne ya tashe ni daga bacci, bayan na tashi na duba wayar na ga sabuwar lamba ce, da na amsa wayar sai na ji wata baiwar Allah ce daga Sokoto, bayan mun gaisa sai tace "Don Allah wai Dan Ibro ya rasu?, an fada min cewa ya mutu, amma ban yarda ba sai na ji daga wajen 'yan jarida". Kai tsaye na bata amsa da cewa "A'a". Ba tare da tunanin ya kamata na bincika gaskiyar labarin ba, dalilina anan shi ne kusan sau biyar kenan a sani na ana yada jita-jitar Ibro ya mutu, yayi hatsarin mota, amma daga baya sai Ibro ya fito ya karyata labarin.

"Ban mutu ba, amma idan lokacin amsa kira ya zo, zan tafi" wannan amsa ce daga bakin Ibro, a wani lokaci a baya da aka yada irin wannan jita-jitar cewa ya rasu.

Bayan mun kammala waya da Malama 'yar Sokoto, ban ajiye wayar ba, sai na shiga Facebook, har ga Allah ko a zuciyata ban shiga don tabbatar da labarin mutuwar Ibro ba, saboda a zuciya ina da yakinin cewa bai mutu ba, kawai abin da aka saba ne na yada jita-jita akan sa.

Rubutun da na fara cin karo da shi ne ya sanya bugun zuciyata tsayawa cak, rubutun edita na Al-Amin Ciroma (Editan Leadership Hausa) na gani, inda yake bayyana labarin rasuwar ta Ibro, wannan rubutun kadai ya tabbatar min lalle Ibro lokaci yayi (Allah ya jikansa). Ina yin kasa sai ga rubutun Ado Ahmad Gidan Dabino, Auwal Danlarabawa da wasu da dama duk suna nuna alhinin su da addu'ar Allah ya gafartawa Ibro.

Kafin na ankara sai naji idanuwana sun cika da kwalla, sai kuma hawaye ya biyu kumatu da daga baya. Ba komai ya sa zuciyata ta kara cikin kankanin lokaci ba, sai tsoron Allah da ya kara shiga jikina. Na kara tabbatar da cewa idan lokacin mutuwar mutum bai yi ba, ko duk mutanen duniya za su so ya mutu ba zai mutu ba, amma da zarar lokacin yayi to fa 'babu tsumi kuma babu dabara' kamar yadda mawaki Aminu Ala yake fada a cikin wata wakarsa.

Allah ya jikan Rabilu Musa Ibro, Allah ya gafarta masa, Allah ya bawa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi. 

Da ba don dan Adam akwai shi da saurin mantuwa ba, da zan iya cewa har abada ba za a iya mantawa da Rabilu 'Dan Ibro' ba.

Friday, December 5, 2014

TAYA MURNA GA 'YAN KADUNA KAN NASARAR EL-RUFAI

Kafin na taya Malam Nasir el-Rufai murnar nasarar zama dan takarar gwamna, sai na fara taya mutanen Kaduna murna, saboda hanyar da suka hau ta samun shugaban da zai sake dawo da martabar Kaduna a idon duniya. 

 Maganar gaskiya ba karamin farin ciki nayi ba, da nasarar el-Rufai, Kaduna uwa ce ga Arewa, amma tuntuni martabarta ta dusashe a idon duniya. 

 Idan 'yan Kaduna suka zabi el-Rufai ba shi suka yi wa alfarma ba, kan su suka yi wa, kamar yadda Janar Muhammadu Buhari ya bayyana lokacin kaddamar da takarar ta el-Rufai. 

Ina matukar kishin el-Rufai ba dan Kano ba ne, da dan Kano ne.... Fada ma bata baki ne. 

 Allah ya bawa el-Rufai nasara a Kaduna!

Sunday, October 12, 2014

Abin Da Janar Buhari Ya Fada Min

Janar Muhammadu Buhari, bai da mantuwa, ya fada min magana kusan shekaru biyu, jiya muna haduwa, ina gaida shi, ya sake maimaita min wannan magana.

Mun hada da Janar jiya a Owerri jihar Imo, wurin daurin auren 'yar Gwamna Rochas Okorocha, a lokacin da naje gaida shi na yi tunanin ya manta sunana, ashe bai manta ba, yana kallo na ya ce Bashir, na durkusa na gaida shi, na tambaye shi kanwata Fatimatu Buhari (Karamar 'yarsa) ya ce tana lafiya.

Ga mamakina sai na ji ya ce "Bashir, Nijeriya fa ta ku ce" maganar ta ban mamaki sosai, saboda ba a lokacin ya taba fada min hakan ba, sannan ya ci gaba da cewa "dole ku so ta, ku sa ta a zuciyarku, ku kyautata mata, sannan ku yi sadaukarwa a gare ta, haka ne zai sa ita ma a nan gaba ta kyautata muku".

Duk da ba kowa ya ji maganar da yake fada min ba, sai wadanda suke kusa da shi, shugaban jam'iyyar APC, Cif John Oyegun da matarsa, su kuma ba Hausa suke ji ba, amma na ga idanun mutane, cikin har da gwamnoni suna kallon mu... Ban sani ba ko tunani suke Baba Buhari yana cewa Bashir kai zaka gaje ni... (Dariya)!

Ba iya wadannan maganganun Buharin ya fada min ba, amma sauran na dauke su a matsayin sirri, ya fada ne a kaina, ni kuma ina gani idan na fito na fadi, wasu za su ga kamar na yi alfahari...

...Allah ya karawa Janar Buhari lafiya, Ya kara masa nisan kwana mai amfani.

Monday, September 29, 2014

Taya Murna Ga Ado Ahmad Gidan Dabino MON

Lambar Girmamawa Ta MON Da Aka Karrama Gidan Dabino Da Ita

Gidan Dabino Yayin Wasu Daga Cikin Tafiye - Tafiyensa A Kasashen Turai

Alhamdulillah! Masha Allah!! A madadin dukkan wani Bahaushe mai son ci gaban harshen da burin ganin daukakarsa, ina taya shugaba na kuma malami na, Ado Ahmad Gidan Dabino MON, murnar babbar lambar girmamawa da kasar mu Nigeria ta ba shi a yau (29/09/2014) a matsayin dan ta, da ya sa ta alfahari a bangaren da ya dauka na rayuwa.

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya mannawa Gidan Dabino lambar mai suna MON.

Ga wanda bai san wane ne Gidan Dabino ba, ko kuma ya san shi yake bukatar karin bayani akansa ga kadan daga cikin tarihin rayuwarsa, wanda na tsakuro a turakar Marubutan Hausa.

An haifi Ado Ahmad Gidan Dabino a Danbagina Karamar Hukumar Dawakin Kudu a shekarar 1964, ya yi karatun allo a Zangon Barebari. Bai samu damar yin karatun boko ba sai da ya kai shekara ashirin, sannan ya fara zuwa makarantar yaki da jahilci ta masallachi, watau makarantar da aka fi sani a Kano da makarantar Baban Ladi,daga nan ya yi karatun Sakandare a GSS Warure inda ya samu SSCE a 1990. Daga nan ya yi kwas na shekara guda akan karatun makafi da koyon aikin kafinta, A shekarar 2005 kuma ya sami diploma akan aikin sadarwa daga jamiár Bayero ta Kano. 

Ado Ahmad na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani kuma littafinsa mai suna In da So da Kauna na daya daga cikin fitattun littattafan Hausa na kowane zamani. 

Ya rike mukamai da dama a Kungiyoyin marubuta, shi ne shugaban Kungiyar Marubuta ta Raina Kama, ya taba zama Mataimakin shugabna ANA reshen Kano, ya zamar mata maáji kafin ya zama shugabanta a 2006. 

Gidan Dabino ya taba zama Edita na FIM magazine kasancewar daya daga cikin wadanda suka kafata a 1999. Kuma shi ne mawallafin Mumtaz. Kazalika shugaba/daraktan gudanawarwa na Gidan Dabino International Nigeria Limited. 

Ya gabatar da makalu a manyan tarrurruka na karawa juna sani a jami'o'i daban daban a gida Nijeriya da wasu daga cikin kasashen turai. 

Za a iya kiransa mashiryin wasan Hausa, dan jarida kuma mawallafi. 

Litattatafansa da suka fito sun hada da:

In Da So da Kauna 1 da 2 (1991)

Hattara Dai Masoya 1 & 2, (1993)

Masoyan Zamani 1& 2, (1993)

Wani Hani Ga Allah 1 & 2, (1995)

Duniya Sai Sannu (1996)

Kaico (1997)

Sarkin Ban Kano (2004) tare da Sani Yusuf Ayagi

Ina kara taya Ado Ahmad Gidan Dabino murna, ina kuma kara yi masa addu'a da fatan alheri, kamar yadda ya karbi wannan kyauta daga Nijeriya, Allah ya nuna mana ranar da zai karba daga Afrika da duniya baki daya. 
Takardar Shedar Girmamawa ta MON da aka bawa Gidan Dabino