Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Monday, February 25, 2013
SOYAYYA A GIDAJEN HAUSA FULANI:
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNA ENGR. (DR) RABI'U MUSA KWANKWASO
Ya mai girma Gwamnan jihar Kano, muna roko a gare ka da ka taimaka a sassauta dokar masu hawa babur tunda an hana goyon biyu, ya kamata a sassauta dokar daga 6pm (yamma) zuwa wani lokacin don bawa kananan yan kasuwa damar yin kasuwancin su cikin nutsuwa ba tare da fargabar komai ba. Ya mai girma wallahi kananan yan kasuwa suna cikin halin kunci akan wannan doka, sakamakon wasu masu sayan kaya sai wajen sallar la'asar suke zuwa sayan kayan saboda jihohin su da nisa, sannan ga kuma yan kasuwa da suke kasuwancin dare na kusa da gidan margayin Sheikh Nasiru Kabara da kuma yan kasuwar Dubai (Jakara), da sauran kasuwanni da dama. Ya mai girma Gwamna mafiya yawan wadannan yan kasuwa suna amfani ne da babur don gudanar da zirga zirga tsakanin wajen neman abincin su da kuma makwancin su. Fatana mai girma Gwamna ya ga wannan gajeren sako nawa, ko kuma makusanta Gwamnan su gani don isar da sakon nawa, domin a dauki matakin da ya dace. Allah ya taimaki gwamnatin jihar Kano da al'ummar jihar gaba daya, Allah ya kare mana mutuncin mu, addinin mu da al'adar mu, Ya kuma ba mu lafiya da zama lafiya.
Tuesday, January 15, 2013
Dariya: Tafiya Daga Kano Zuwa Lagos
Thursday, December 20, 2012
Budadden Sako Zuwa Ga Sabon Gwamnan Jihar Kaduna
Zuwa ga Mai Girma, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, Gwamnan Jihar Kaduna.
Assalamu – Alaikum!
Da farko ina yin mana jaje na rashin Gwamnanmu da mukayi Mr. Patrick Ibrahim Yakawo, a sanadiyar hadarin jirgin sama, muna fatan Allah Yasa ya taradda da yan’uwansa acan, mu kuma Allah Ya kyautata namu bayan nasu Yasa mu cika dakyau da Imani, ba yanda za ayi domin dukkan mai rai mai mutuwa ne.
Bayan haka, inaso in yi anfani da wannan dama domin inyi maka nasiha da kuma bada shawara, kasancewar bani da wata hanya da zanzo in sameka ni dakai sai ta wannan hanyar wanda na tabbata, in baka gani ba, wadanda suke kusa dakai zasu gani kuma zasu sanar dakai.
1. Da farko ina tunatar dakai da kara sanya jin tsoron Allah a cikin al’amuranka duka na yau da kullun, domin shi ne zai zame maka jagora akan dukkan abin da ka fuskanta.
2. Ka godewa Allah a bisa wannan ni’ima da ya yi maka. Ta yaya zaka gode maSa? Shi ne ta hanyar aikata abin da duk Ya umurce ka dasu gwargwadon ikonka, ka kuma nisanci duka abubuwan da Ya hanaka, idan ka siffantu da haka, to, shi zaisa Ya yi maka kari a bisa wannan ni’iman da Yayi maka yanzu.
3. Ka zamo mai adalci a bisa wadanda Allah Ya daura maka alhakinsu a kanka. Duk mai hakki ka bashi hakkinsa gwargwadon yanda doka ta tsara.
4. Ka zamo mai gaskiya da rikon amana da kuma daukan alkawarin abubuwan da kasan bisa ikon Allah bai fi karfinka ba.
5. Ka guji yin duka wani abu da zai zamo nau’in yin zalunci ne ga wadanda kake shugabanta, domin babu shamaki tsakanin addua’an wanda aka zalunta da Mahaliccinsa, kamar yanda Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wasallam ya sanar damu haka, ya kuma ja kunnen mu akai.
6. Ni a tawa shawaran, ina ganin akwai wasu abubuwan guda biyu da suke neman sufi karfin talaka gabaki daya, wato sune harkan ilmi da abin da ya shafi harkan lafiya, ka sanya ido kai tare da bada dukkan gudummuwan da zaka iya badawa.
7. Ka sakamma kananan hukumomi mara domin suma su sami daman yin ma nasu al’ummomin ayyukan morewa. Ka kuma sanya ido akan yanda suke gudanar da harkokinsu gudun kada su wuce gona da iri.
8. Kula da harkan tsaro shima yana da matukar muhimmanci, domin sai da zaman lafiya ake samun daman gabatar da duk wasu ayyuka.
Daga karke, ina rokon Allah da Yayi maka jagora, Ya sanya maka hannu a bisa wannan nauyi da ya daura maka, Ya kasance tare dakai a duk inda kake, Ya baka ikon sauke dukkan nauyin da Ya daura maka, Ya kuma sanya maka katangar karfe tsakaninka da dukkan makiya mutun ko aljan. Muma Allah Ya biya mana dukkan bukatummu.
Wassalamu Alaykum,
ABDULKARIM MUH’D TANKO
Tuesday, November 13, 2012
Kotu Ta Yanke Wa Jarimi Sani Musa Danja Hukunci Daurin Shekara Guda A Gidan Yari
Kotun tafi da gidanka ta Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta yankewa shahararren dan wasan kwaikwayon nan na Hausa Sani Musa Danja daurin shekara guda a gidan yari.
Kotun ta daure Sani Danja ne sakamakon fitar da wani fim din sa mai suna Gudaliya ba tare da bin dokar hukumar tace finafinan ta jihar Kano ba, wanda hakan ya sabawa dokar hukumar ta sashi na 100 (2) ta shekarar 2001, sannan hukuncin da aka yanke masa na karkashin sashi na 112 na kundin tsarin mulkin hukumar.
Bayan samun sa da laifin, alkalin kotun mai shari'a Mukhtar Ahmad ya yanke wa Sani Musa Danja hukuncin zaman yari na tsawon shekara guda ko kuma biyan tarar N30,000, karkashin sashi na 157 na kundin hukunta masu laifuka, na shekara ta 2001.
Kotun ta daure Sani Danja ne sakamakon fitar da wani fim din sa mai suna Gudaliya ba tare da bin dokar hukumar tace finafinan ta jihar Kano ba, wanda hakan ya sabawa dokar hukumar ta sashi na 100 (2) ta shekarar 2001, sannan hukuncin da aka yanke masa na karkashin sashi na 112 na kundin tsarin mulkin hukumar.
Bayan samun sa da laifin, alkalin kotun mai shari'a Mukhtar Ahmad ya yanke wa Sani Musa Danja hukuncin zaman yari na tsawon shekara guda ko kuma biyan tarar N30,000, karkashin sashi na 157 na kundin hukunta masu laifuka, na shekara ta 2001.
Subscribe to:
Posts (Atom)
