Safeena Buhari diya ce ga Gen Muhammadu Buhari. Abin da yake faruwa shine akwai wata baiwar ALLAH da watakila 'yan uwa suke ganin post dinta a koda yaushe a facebook da wannan suna na Safeena Buhari, mun yi kokari domin gano shin da gaske safeenan Gen Buhari ce ko kuwa ta karya ce, Alhamdulillah wakilinmu ya je har gidan Gen Buhari a kaduna inda aka tabbatar masa da cewar wannan Safeena Buhari da muke ganin a fzbk ba ita ce ba.
Wato muna da yawa wadanda muke musayar kalamai da ita ta bayan fage wato Inbox, na taba tambayarta tsakaninta da ALLAH ita diyar General ce, ta yi min rantsuwa akan cewa ita diyarsa ce, wanda sakamakon bincikenmu ya tabbatar mana da cewa karya take.
Abinda yake faruwa shine, kusan da yawanmu da muke magana da ita ta shaidamana cewar tana aiki a QATAR amma kuma yanzu tana zaune a Germany sakamakon jinyar mijinta, wasu kuma ta shaidamusu cewar tana England, akwai daga cikinmu wadanda ta yaudara da sunan zata samar masa da Scholarship dan su yi karatu a QATAR, haka kuma tayi wa wani alkawarin tuntubar Sarkin DUBAI domin nema masa taimako, duk da take yin wadannan maganganu da alkawura, mu tuni mun gane ta, kawai shiru muka yi mata, amma kuma yanzu lokaci yayi da muke ganin ya kamata mu bankada wannan Asiri, domin ta fara yaudarar wasu da samar musu da kwangilar harkar mai a kasashen larabawa, wanda idan muka ci-gaba da yin shiru zata bata sunan Gen Buhari ne, kuma zata damfari wadanda basu santa ba, haka kuma itace dai take amfani da wani account mai suna YUSUF BUHARI wanda shima dane ga Gen Buhari amma bai da masaniyar ana amfani da sunansa anan facebook.
Dan haka jama'a a kiyaye Mu'amala da ita, domin ba Safeenar gaskiya bace, watakila wani Dan iskan kato ne yake amfani domin ya bata musu suna kuma ya nemi abin duniya. Hakika mai amfani da wannan suna na Safeena Buhari yana da masaniyar gidan Buhari sosai, dan kawai ya samu ya ci-kasuwarsa, a kwanakin baya ta sanya wani hoto na Matar Gen Buhari da matar Tunde Bakare da kuma Safeena Buhari ta ainihin, idan kuka duba Profile dinta zaku gani. Muna addu'ar duk wanda yake wannan danyan aiki ALLAH ya shirye shi, idan kuma ba mai shiryuwa bane, ALLAH ya shiga tsakanin nagari da Mugu.
Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Monday, October 22, 2012
Sunday, October 21, 2012
Gwamnonin Kasar Nan Da Suka Fi Bajinta
Sakamakon binciken da wata kungiya mai suna Eagle Eyed Youth Association of Nigeria tare da hadin gwiwar kungiyoyin sa kai fiye da 100 da kuma jin ra'ayoyin jama'a a sassan kasar nan daban - daban, ya bayyana sunayen gwamnoni a kasar guda 10 da suka fi yiwa talakawansu aiki. Gwamnonin su ne:
1) Dr. (Barr) Ibrahim Shehu Shema, na jihar Katsina.
2) Barr. Babatunde Raji Fashola na jihar Lagos.
3) Chief Rochas okorocha na jihar Imo.
4) Alh. Aliyu Wamakko na jihar Sokoto.
5) Eng. Rabi'u Musa Kwankwaso na jihar Kano.
6) Alh. Tanko Al Makura na jihar Nasarawa.
7) Dr. Rotimi Amaechi na jihar Rivers.
8) Rear Admiral Murtala H. Nyako na jihar Adamawa.
9) Alh. Sule Lamido na jihar Jigawa.
10) Comrade Adams Oshiomole na jihar Edo.
Shin a naku ra'ayin wannan sakamako yayi daidai ko da son zuciya a cikinsa? Idan akwai son zuciya a naka ra'ayin wane gwamna ya kamata ya zama a matakin farko?
Saturday, October 13, 2012
Sarkin Kano Ya Cika Shekaru 49 Akan Gadon Sarauta
Allah mai yadda ya so. A yau Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya cika shekaru 49 akan gabon sarauta (13 Oktoba 1963 - 13 Okboba 2012) Idan Allah ya kaimu shekara mai zuwa zai cika shekaru 50 daidai wato rabin karni akan gadon na sarauta.
A madadin ni kaina da sauran maziyarta wannan shafi muna taya Mai Martaba San Kano da sauran daukakin jama'ar Kano munnar wannan rana.
Allah ya karawa Sarki lafiya da imani, Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu Kano da kasarmu Nijeriya baki daya.
Bashir Ahmad
Thursday, September 27, 2012
Nigeria: Zan Cika Shekaru 52 Bayan Samun 'Yancin Kai Na
Kwanaki uku ya rage na cika shekaru 52 bayan samun 'yancin kai na daga hannun turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya. Zan yi murnar zagayowar ranar ne kawai saboda ta cancanci hakan, amma ba don ina da 'yancin kan nawa ba, domin kuwa a tarihin rayuwa ta ban taba shan wahala, da rayuwa marar 'yanci ba kamar bayan samun 'yancin kan nawa da ake ikirarin wai na samu. Hmmm ta bangare na dai ba wani 'yanci da zan iya cewa na samu, sai dai samuwar rayuwar bauta da na sake samun kai na a ciki.
To ku kuma 'yayana, mai za ku ce da wannan rana ta 1st October? Na san kalilan daga cikin ku suna murna da ranar har bukukuwa suke yi sakamakon zagayowarta.
Amma dai bari na ji amsa daga gare ku. Shin kuna farin ciki da zagayowar ranar?
Ku ziyarci Dandali Domin ba da amsoshinku.
Tuesday, September 18, 2012
Mu Kauracewa Amfani Shafin YouTube

Yan uwa ya kamata mu kauracewa amfani da shafin YouTube da rage mu'amala a shafin matambayi baya bata na Google, sakamakon kin cire video wasan kwaikwayon da aka yi isgilanci ga Fiyayyen Halitta Annabin Muhammad (SAW).
Tun bayan fitowar wannan wasan kwaikwayo a shafin na YouTube gwamnatin kasar Amurka ta umarci kamfanin Google da ya mallaki shafin na YouTube da su cire video daga shafinsu, saboda kyale shi cin zarafin mabiya addinin Musulunci ne.
Amma kamfani na Google ya kekasa kasa da cewar yin hakan ya saba dokar kare hakkin loda video na masu amfani da shafin.
Wannan dalilin ya sa wasu kasashen Musulmai suka yanke shawarar kauracewa amfani da YouTube a ranakun 20, 21 da 22 na watan Satumba da muke ciki, don nuna fushin su ga kin cire video da shafin yayi. Wanda kuma akalla Musulmai sama da miliyan 100 suna amfani da shafin a kowace rana.
To ya kamata mu ma mu shiga sahun 'yan uwanmu Musulman duniya, na kauracewa amfani da shafin a wadannan rana ku, koda kuwa akwai muhimmin aiki da za muyi a cikin sa, yin hakan ba karamin asara zai haifarwa kamfanin ba, idan kuma hakan ma suka ki yarda da bukatarmu na cire video, to sai mu dauki matakin daina amfani da shafin na dindindin, wato na har abada.
Aikawa, sauran 'yan uwa wannan sako.
Subscribe to:
Posts (Atom)
