Tuesday, June 12, 2012

Gidauniyar Rochas Okorocha Za Ta Gina Jami'ar Kyauta A Kasar Nan


Gidauniyar ci gaban ilmi da samar da shi kyauta ga masu karamin karfi ta Rochas Okorocha, ta bayyana kudirinta na gina Jami'ar farko a kasar nan da za ta ke bayar da ilmi kyauta ga masu karamin karfi.

Gidauniyar a halin yanzu na da mallakin makarantun sakandare har guda biyar a fadin kasar nan, wanda duk ake bawa masu karamin karfi ilmi a kyauta a cikin su, makarantun akwai su a bangarorin kasar nan daban daban, akwai a Ogboko jihar Imo, Owerri, Kano, Ibadan da kuma Jos.

Lalle Rochas ya jiri tuta a fadin tarayyar kasar nan, ya kuma zama abin kwatance, da za a samu masu tausayin talakawa kamar sa guda goma a cikin masu mulki da masu arzikin da ke dunkule a kasar nan da ilmi bai gagari 'yan talakawa ba.

Wannan gidauniya ta dade tana tuttula ilmi ga 'yayan da iyayen su ba za su iya daukar dawainiyar biyan kudade karatun 'yayansu ba, kuma wani abin sha'awa tun kafin ya samu mulkin jihar Imo da yake kai a halin yanzu gidauniya ta ke, kuma take yin aikin alkhairai daban daban da suka shafi fannin samar da ilmin zamani.

Sunday, June 10, 2012

Ana Zargin Faruk Lawan Da Hannun Dumu - Dumu Wurin Karbar Cin Hancin $600,000


Ana zargin shugaban kwamitin bincike kan badakalar tallafin man fetur Hon. Faruk Lawan da hannu dumu - dumu wurin karbar cin hancin zunzutun kudi dala mai dukan dala har dalar Amurka $600,000 daga wurin wani kamfanin man fetur da baida suna.

Hon. Faruk an ce da farko ya musanta zargin sai bayan da yaga takardu tsirara dauke da bayanin da ake zarginsa a kai. Tuni majalisar wakilai ta gayyace daya garzaya gabanta domin kare kansa daga wannan zargi.

Rahotonni sun nuna cewa ita ma dai hukumar nan mai yaki da yiwa arzikin kasa zagon kasa wato EEFC ta shirya tsaf domin gayyato Faruku don yi mata bayanin dalla dalla yadda akayi hakan ta faru.

Idan har wannan zargi ya tabbata gaskiya ne Faruk Lawan ya amshi wannan makudan kudade, lalle mu talakawan Nijeriya sai mu fara ja da baya, da rage tunanin cewa nan gaba kasar nan za ta zama daidai, da kuma daina murna da farin ciki duk lokacin da muka samu labarin anyi kokari kawar da wani laifi a kasar nan.

Ba komai ya sani fadin haka ba, sai tunowa da nayi lokacin da Faruk Lawan ya bayyana rahotonsa karo na farko, game da irin yadda kwamitinsa yayi aiki tukuru ba tare ba rana sai aka gano yadda wasu 'yan tsirara suka rinka wadaka da rabebeniya da dukiyar al'ummar kasar nan, da yadda Faruk ya rinka daukar alwashin ba zasu rufawa kowa suka samu da laifi asiri ba. Hakan tasa talakawa suka fara yiwa juna barka da fara tunanin lalle kakarsu ta fara yanke saka, sai kuma gashi kwatsam ana zargin mai dokar bacci da bugewa da gyangyadi. Allah ya kyauta.

Allah Ya Yi Wa Kanin Mataimakin Shugaban Kasa Rasuwa


Allahu Akbar! Allah ya yi wa Alhaji Aliyu Sambo, kanin magirma mataimakin shugaban kasa Arc. Muhammad Namadi Sambo rasu a jiya.

Alhaji Aliyu mai shekaru 40 ya rasu ne sakamakon hadarin mota daya ritsa da shi akan titin Mando yankin Kawo dake cikin garin Kaduna.

Allah ya jikansa da sauran al'ummar Musulmai baki daya.

Alhamdulillah! Yau Na Cika Shekaru 21 A Duniya


Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) Mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SWA). Ina kara godiya ga Allah daya raya ni yau tsawon shekaru ashirin har da daya a wannan duniya mai cike da fadi tashi. Allah ina godiya da ka halicce ni cikin mabiya addinin Musulunci kuma ka zaba min addinin a matsayin addinina, kuma ka dora rayuwata akan tafarkin koyarwar addinin, lalle wannan shi ne babban abin godiya. Ya Allah ina rokonka ka bani ikon karasa rayuwata ba tare da na saba da koyarwa addinin Musulunci ba.

Wannan rana ta 10th June, rana ce mai matukar muhimmanci a gare, kuma rana ce da duk wani masoyina yake taya ni farin cikin zagayowarta. Kamar yadda lissafi ya nuna yau ma Allah ya sake nufarmu da zagayowa wannan rana, saboda haka yau na cika shekaru 21 da haihuwa daidai da watanni 252 ko satuka 1095 ko kwanaki 7671 ko awanni 184104 ko mintuna 11046287 ko sakonni 662777275 hhmm lalle na girma. Ina alfari da wannan rana a matsayin ranar da Allah ya nufi wanzuwata a wannan duniya domin na bauta masa.

A kodayaushe idan wannan rana ta zagayowa abinda yafi tsaya min a raina shi ne yadda iyaye na suka dauki dawainiyata tun daga haihuwata har zuwa yanzu, sun sani makarantu daban daban domin nasan yadda zan bautawa mahaliccina kuma na iya zama da duniya da al'ummar da ke cikin ta lafiya. Zahiri babu wata kalla da zan bayana ta godiya a gare su naji na gamsu sai kawai naci gaba da yi musu addu'ar Allah ya saka musu da mafificin abinda suka yi min na alheri.

'Yan uwa da abokaina ma sun taka muhimmiyar rawa a fannin rayuwata, a koyaushe suna zuwa gare ni idan na bukaci hakan, suna taimako na da bani shawarwari na alkhairi, sukan nuna goyon bayansu a gare ni a dukkan ra'ayi, sukan nuna farin cikin su gare idan abin farin cikin ya same ni, da nuna bakin ciki idan akasin farin ciki ya faru, sukan kasance dani kodayaushe domin kada su bar ni cikin kadai ci. Nagode! Nagode!! Nagode!!!.

Ya Allah ka raya mu, ka bamu ilmi mai amfani da zamu taimaki yan uwanmu da addininmu.

Tuesday, June 5, 2012

Tsakanin Buhari Da PDP Wa Ke So Tarwatsa Nijeriya? I



Ga duk wanda ya san Janar Muhammadu Buhari zai iya fassara shi a matsayin mutum mai tsattsauran ra’ayi akan abinda ya yarda da shi. Wanda ba ya shakkar bayyana ra’ayinsa ga kowa a kowa ne lokaci, kazalika kuma a ko ina.

Tsayayyen da ya ke fafutukar kawar da mulkin danniya da kama-karya. Kaifin dayan da ba ya fargabar shelantawa duniya manufarsa ta hukunta duk wani barawon shugaban da ya kwashi dukiyar talaka. Wanda a halin yanzu miliyoyin talakawan Nijeriya su ke son sa ba domin giwa ta fadi a sha gara ba, face sai domin kyautata masa zato da su ke yi cewa, shine kwalelen da zai tsallakar da su daga kududdufin karangiyar bakar wahala da su ka tsinci kansu sakamakon rashin nagartaccen shugabanci.

Janar Buhari ya kasance mai alfahari tare da bugun kirjin cewa, ya zama shugaban kasa, ya zama ministan man fetur, ya zama gwamnan tsohuwar Maiduguri kana kuma ya rike shugaban hukumar rarar mai ta kasa, amma kuma bai taba satar ko kwabo ba. Ya kan kuma jaddada cewa, a shirye ya ke ya amsa takardar gayyata daga kowa ne domin kare kansa akan shi ba barawo ba ne. Sau da dama a Nijeriya idan aka samu mutum mai bayyana kansa a matsayin mai gaskiya, sai tafiya ta yi tafiya sai a tsince shi ya hada kai da wadanda a baya ya ke kira a matsayin azzalumai kuma barayi domin karbar nasa kason.

Amma wani abin mamaki da ya kara daukaka kimar Janar Buhari shi ne yadda har yanzu ya ki aminta ya je ya sayar da ‘yancin talakawan da su ke son sa, domin a cika masa asusunsa. Shi ne wanda masu kashi a gindi su ke fargabar ya samu dama domin sun tabbatar ba zai raga musu ba. Janar Buhari ne talakawa ke tsananta son sa ba tare da ya na da kudin da zai kyautar a gare su ba. Sabanin sauran ‘yan siyasa da sun kwashi dukiyar kasa su ke kuma rabar wa ga talaka a yayin da su ka so a sake zabensu.

Janar Muhammadu Buhari ne ake ta kulle-kulle tare da makarkashiyar ko ta wanne hali a samo laifin da za a jingina masa domin a tozarta shi. Ko a yayin da hasalallun talakawa su ka yi tinzurin yi wa PDP korar-kare a wasu jihohin Arewa, sakamakon zargin tafka magudi da aka yi, wanda hakan ya janyo yamutsin da aka yi asarar rayuka da kuma dukiyoyi. An nemi a jingina wannan tarzoma ga Janar Muhammadu Buhari.

Kalamansa na ‘kowa ya kafa ya tsare ya kuma raka kuri’arsa’ a yayin gudanar da zabe, na daya daga cikin abinda ‘yan barandan siyasa da kuma sojojin baka su ka karbo kwangila domin lika masa a matsayin makamashin da ya assasa wutar wancan rikici. Kana kuma an zarge shi da yin amfani da karin maganar ‘jiki magayi’ a matsayin sababin rashin zaman lafiya da ya zama alakakai a wasu jihohin Arewa.

Akwai karashen wannan jawabi a kashi na II a kasa.