Tuesday, January 31, 2012

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Matasan Arewa


Aminci a gare ku ya ku matasan yankin Arewa!

A matsayina na daya daga cikinku zanyi amfani da wannan dama na tunatar damu wasu muhimman abubuwa da suke hakki ne a gare mu amma muke yin sakaki da su. Sanin kowa ne cewa matasa sune kashin bayan kowace al'umma, domin kuwa sune iyaye kuma shugabannin gobe. Haka ne ma yasa masana masu hangen nesa suka ce duk al'ummar da matasanta suka hada kansu suka zama tsintsiya mai madauri guda, to wannan al'umma nan gaba za ta zama ja gaba a kowane irin fanni na rayuwa, ta kuma yi wa sauran al'ummomin zamanin fin-cin-kau.

Ya ku matasa Arewa! Wai shin ina muka dosa ne? Shin bama ganin yadda wannan yanki namu ke cikin wani hali na rashin kulawa ne? Shin wane irin mataki muka dauka ko muke shirin dauka akan wannan hali?

Matasan Arewa bai kamata mu koma gefe muna ganin laifin shugabanni, sarakuna, malamai da manyan Arewa kadai ba, duk wani abu na rashin dadi daya faru sai mu dora musu laifi muna fadin ba sa kishin Arewa. Zahirin gaskiya wannan ba daidai bane, kuma ban yarda wadannan jagororin Arewa sune ke da laifi kadai ba, idan har suna da laifi to muma muna da namu laifin. Saboda kuwa idan manya sun kasa mai zai sa mu kuma muyi shiru mu kasa cewa komai?

Misali a matsayinmu na shugabannin gobe wane irin shiri mukayi don daukar wannan nauyi? Shin mun san tun lokacin da Sardauna, Tafawa Balewa da Aminu Kano suka fara gwagwarmaya? Idan muka koma tarihi zamu ga sun fara gwagwarmaya akan Arewa tun suna da karancin shekarun da basu fi 20 zuwa 30 ba. To mu fa yaushe zamu fara? A matsayinmu na masu ikirarin kishin na Arewa.

Zan dan yi wasu tambayoyi ga 'yan uwana matasan Arewa, wadandan tambayoyi sun dade suna zirga zirga da kai kawo a cikin zuciyata, amma kuma har yanzu na kasa samun koda amsar tambaya daya daga cikin tambayoyin. Fatan daga yau zan samu dukkan amsoshin wannan tambayoyi.

TAMBAYOYIN SUNE

Shin a matsayinmu na matasa masu so da kishin Arewa wace irin gudunmawa muka bada wurin ganin burin marigayi tsohon shugaban Kano Umar Musa Yar'adua ya cika na zuwan teku Arewa?

Shin a lokacin babban zaben daya gabata wace irin rawa muka taka wurin fitar da dan takara guda daya kwakkwara daga yankin Arewa?

Shin wane irin kokari muke yi ganin dawo da zaman lafiya a Arewa kamar yadda muke a shekarun baya?

Shin an ya kuwa akwai wani shiri da muke yi na ganin samun hadin kai da soyayyar juna a tsakanin kabilu da addinan wannan yanki na Arewa a matsayinmu na jagororin kishin Arewa?

Akwai tambayoyi makamantan wannan masu dumbun yawa dake kunshe a zuciyata wadda na tabbar ku ma ba za'a rasa irinsu a zuciyoyinku ba. Fatanmu mu hada hannu mu samarwa kanmu amsoshin wadannan tambayoyi.

Sai tambayata ta karshe, shin tawa ne hali zamu kawowa kanmu mafita? Amma saboda saukin wannan tambaya zanyi kirinkin bada amsarta. Amsar tambayar itace mu matasa mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinmu daya, bayan haka kuma mu zama masu kishi da soyayyar yankinmu. Sannan mu zama masu magana da harshe guda, wato idan matashin jihar Adamawa yace eh, to idan aka samu na jihar Kwara ma yace eh. Hakan kuwa zaiyi wahala har sai munyi wata kungiya da zata tattaro dukkan matasan Arewa ta dunkule mu wuri guda. Yin hakan ne kadai muryarmu zata ke isa inda muke so da bukatar taje, sannan hakan ne zai sa asan muhimmancimu, ta haka ne kadai zamu samu damar kare 'yancinmu da mutuncimu.

A karshe nayi amfani da wannan dama ne don na isar da wannan sako ga duk wani matashi wannan wasika, saboda sanin wannan ce hanya kadai da zan aika sakon nawa kuma ya isa zuwa wurin wadanda na aika dominsu. Fatan duk wanda ya karanta wannan wasika zai aikawa sauran abokansa ta haka ne zata samu isa zuwa ga duk wani matashi mai kishin Arewa.

Sannan zanyi kokarin ganin an buga wannan wasika a jaridu da mujallu musamman masu amfani da harshenmu na Hausa.

Allah ya daukaka Arewa, Allah ya daukaka kasarmu Nigeria!

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Monday, January 30, 2012

Shin Kotu Ta Yiwa Hamza Al-Mustapha Hukuncin Adalci?


Kotu ta yankewa Major Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan shafe sama da shekaru 13 a gidan yari. Alkaliyar Kotun Mrs Dada ta bayyana cewa an yankewa Al-Mustapha hukuncin ne saboda da sa hannunsa aka kashe Hajiya Kudirat Abiola matar MKO Abiola. Al-Mustapha yaje kotun ne sanye da fararen kaya wanda bayan yake hukuncin ya fito yana murmushi gami da dagawa mutane hannu. Wannan dalili yasa wasu daga cikin magoya bayansa kuka, wasu kuma na Kabbara.

Major Al-Mustapha ya bayyanawa manema labarai cewa a matsayin na Musulmi bayyi mamakin hakan ba, kuma dukkan wani munafiki karshensa bazai yi kyau. Lauyan da yake kare Al-Mustaphan ya bayyana cewa zasu daukaka kara kuma suna sa ran samun hukuncin adalci a kotun gaba.

TAMBAYOYI: Shin wannan hukunci da kotu ta yakewa Al-Mustapha akwai adalci a ciki? Shin duk shekarun daya shafe a gidan yari basu isa hukunci ba? Shin duk mutanen da Ojukwu ya kasha mai yasa ba'a yanke masa hukuncin kisa ba? Shin ina labarin mutanen da Al-Mustaphan ya lissafo a kwanakin baya wanda da sa hannunsu aka kashe MKO Abiola? Shin wane mataki manyan Arewa suka dauka don ganin ba'a yiwa dansu hukuncin zalinci ba?

Ya ALLAH ga bawanka Hamza Al-Mustapha kar ka bari ayi masa hukunci na zalinci.

An Yankewa Al-Mustapha Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

A Najeriya wata kotun daukaka
kara a jihar Legas ta yanke wa
tsohon dogarin marigayi Janar
Sani Abacha, Hamza Al-
Mustapha hukucin kisa ta
hanyar ratayewa sakamakon
kisan uwargidan marigayi MKO
Abiola.

Mai shari'a Mojisola Dada ta ce ya
kamata a rataye Manjo Hamza Al-
Mustapha, sakamakon samunsa
da hannu a shirya kisan
uwargidan shahararren dan
kasuwa kuma dan siyasa
marigayi Moshood Abiola.

Al-Mustapha, shi ne na hannun
damar tsohon shugaban mulkin
soji Janar Sani Abacha, ya shafe
shekaru 13 yana zama a gidan
yari, tun bayan da aka zarge shi
da shirya kisan.

Wannan shari'a ta ja hankalin
jama'a sosai a kasar, musamman
ganin lokacin da aka shafe ana
gudanar da ita - da ma
abubuwan da suka rinka faruwa
a lokacin shari'ar.

Anta samun shaidu masu cin
koro da juna a lokacin shari'ar,
yayin da kungiyoyi daban-
daban suka nuna damuwa kan
yadda aka dade ana gudanar da
ita.

A shekarar 1996 ne aka kashe
Kudirat Abiola sakamakon wani
harbi da wasu mutane suka yi
mata.

Marigayi Moshood Abiola ne ake
kyautata zaton ya lashe zaben
shugabancin kasar da aka
gudanar a shekara ta 1993,
wanda daga bisani gwamnatin
mulkin soji ta Janar Ibrahim
Babangida ta soke.

Kuma babu wani abu da yake
tunawa 'yan kasar wancan zabe
kamar wannan shari'ar.
Sai dai babu tabbas ko wannan
hukunci zai kawo karshen
sa'insar da shari'ar ta haifar.

Wannan hukuncin ya zo a daidai
lokacin da Najeriya ke cikin
mawuyacin hali ta fuskar tsaro
da kuma siyasa, abinda masu
lura da al'amura ke ganin ka iya
kara cakuda al'amura a kasar.

Daga shafin BBC Hausa

Thursday, January 26, 2012

Ba Zan Sake Tsayawa Takarar Kowane Irin Mukami Ba - IBB

Tsohon Shugaban kasar Nijeriya, kuma daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, wanda ya janye daga takarar a zaben shekarar da ta gabata ta 2011, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shaida cewa ya yi bankwana da siyasa kuma ba zai kara neman wani mukamin a gwamnatance ba.

IBB ya yi wannan magana ne a wani taron shekara da kamfanin Trust Media LTD ya shirya wanda aka gabatar a Transcorp Hilton Hotel dake birnin tarayya Abuja, wanda yayi magana a matsayin shugaban taron.

Babangida ya ce "Ina da labari ga duk kafafen yada labarai na kasar nan baki daya, duk da zan ci gaba da zama mai bada shawarwari ga 'yan siyasa masu zuwa anan gaba, amma ba zan kara tsayawa takara don a zabe ni a kowane irin mukami ba anan gabata. Ya ce Babangida ba zai sake tsayawa kowane dan takara don samun nasarar wani mukami ba".

Tsohon shugaban kasar ya yi amfani da irin kalaman da tsohon shugaban kasar Amurka Richard Nixon ya yi a lokacin da shi ma yake bankwana da siyasa.

Shugaba Goodluck ya Bukaci Tattaunawa da 'Yan Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kalubalanci kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram da su fito su bayyana kansu su kuma bayyana bukatunsu a matsayin matakin farko na fara tattaunawa da su.

Shugaban ya kuma amince cewa amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen tashe-tashen hankulan ba. Sai dai Jonathan ya kara da cewa, sabanin tsagerun Naija Delta, matsalar 'yan Boko Haram ita ce ba a san shugabanninta ba balle a tattauna da su.

Sai dai shugaban Kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya ce ba za su tattauna da gwamnatin Najeriyar ba. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Jonathan ya ce babu tantama kungiyar boko Haram tana da alaka da sauran kungiyoyi masu jihadi a ketaren Najeriya.

Akalla mutane 186 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da kungiyar ta kai a Kano ranar Juma'ar da ta gabata. "Idan suka bayyana kansu, suka kuma ce ga dalilin da ya sa muke gwagwarmaya, ga dalilin da ya sa muke fito na fito da gwamnati, ga dalilin da ya sa muke lalata dukiyoyin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, to daga nan za a samu ginshiki na fara tattauna wa, in ji shugaba Jonathan.

Shugaban na Najeriya ya kuma kara da cewa, "Za mu tattauna da ku, ku sanar da mu matsalolinku, za mu warware muku su, amma idan ba su bayyana kansu ba, da wa za ka tattauna?" Sai dai shugaban na Najeriya ya bayyana cewa akwai bukatar a kawo ayyukan ci gaba a yankunan arewacin kasar inda ake da dimbin matasa marasa aikin yi, abinda yake baiwa kungiyoyi masu tada kayar baya damar samun magoya baya cikin sauki.

"Amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen hare-haren ta'addancin ba," in ji shi, "ana kuma bukatar a samar da yanayin da zai baiwa matasa damar samun ayyukan yi".

Daga shafin BBC Hausa
www.bbchausa.com